Sashe 114
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka ta kwaa tana faɗawa Ubangiji damuwar ta, tana rarrashin shi da yi masa kirari kan ya kawo mata mafita, sannan ta ƙara da bata son mafitar da gaggawa, alkairi kawai take nema, sai gashi safiya na wayewa ta samu iyayen ta, wanda ta san ba zata sake yin kukan maraici ba, ba zata sake tunani akan yadda za ta ci ko tasha ba, duk da dai ma Alhaji ya mata ihsani na rabuwa, dan kuwa milyan biyar ya bata cif tare da takardar da ta gani yaa shaida mata da yana sake tabbatar mata mallaka motar ta duk da dama shi ya siya mata, Alhamdulillah, ta ji daɗin kyautar dan akwai abinda ta hango zata yi da kuɗin, ta ji ina ma maza zasuyi koyi da shi, da mace ba ta tagayyara ba dan auren ta ya mutu, da ba zata yi wani abu ba wai shi *zawarci*, da zata fi ƙarfin komai har ubangiji ya sake damƙata hannun wanda ya zaɓa mata.
Yadda tayi nisa a tunani ya sa har bata ji sanda Aisha take ci gaba da tayar da Maman ba, saida ta ji tana faɗin "Yawwa, Mamiena, tashi ga aunty Ummun ki na kawo miki, nayi yaƙi na ƙwato miki ita, kuma yanzu ta yarda ke mahaifiyar ta ce."
Kallon Aisha tayi da irin yanayin nan na _"Oh Allah !" Sannan ta kalli Mamie da ta riƙe hannun Ummu gam tana shirin tashi da wani irin maɗaukakin zumuɗi tana faɗin "Aunty Ummu, da gaske ke ce? Ke ce a gabana?"
Ɗan riƙe ta Ummu tayi tana fara'a tace "Ni ce, ni ce da kai na *Mamie*."
Rarako idanu tayi alamar mamaki ta kalli Aisha tace "Mamie? Ƙawata kin ji me ta ce? Wai Mamie? Ni ce Maman ta?"
Dukan su murmushi suke, kafin Ummu ta sake cewa "E mana, *Mamana*, ke fa mahaifiyata ce."
Ƙurawa fuskar Ummu idanu tayi, hakan yasa Ummu sadda kan ta tana jin kunyar wasu abubuwa da suka faru tsakanin ta da Maman, daga kan sunan *aunty* da take kiran ta, zuwa kan hirarrakin da suke yi wasu lokuta a grp ko a pc, Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un ! Ita ga gwana iyayya ƴar masani, komai da ruwan ta komai ta sani, ashe duk hirar nan da take yi wacce ta shafi mata da maza duk Maman ta na jin ta? Ita kam ya za ta yi?
Mama Nuriyya kuma ko ko a kai wannan tunani bai zo mata ba, to ita bata ɗauki hakan a wani abu ba, hasalima alfahari za ta yi da ƴar ta ta kasance mai sani dayawa akan abin da ya shafi mace da namiji, kuma take da sanin maganin wasu matsaloli da dama, ita kawai tunanin ta wai jaririyar da aka ɗauke mata a cikin tsumma, ita ce zaune haka gaban ta? Tayi tsayi sosai, tayi jajir da ita, tayi kyau, fatar ta a kwance alamar hankalin ta kwance a gidan mijin ta, ga haƙoran makka dake nuna ta sauke farali, ita wannan abu ina za ta saka kan ta dan farin ciki? Daga wannan kallon kuma sai ta fashe da kuka, hakan yasa suka rumgume juna suna kukan tare Aisha na rarrashin su.
*A* ƙanƙanin lokaci labarin samun jikanyar margayi Saheeb Ahlan, ga makusanta wannan ahali tuni suka ga fuskar Ummu, dan zumuɗi ya sa suka kasa haƙura, take wasu kira suke ta WhatsApp kuma hoto mai motsi dan su ga fuskar da aka ce tana kama da Hajia sak. Ita kan ta Hajia saida ta zuba ruwa tiles ta sha dan murna, ta gode Allah, tayi murna tayi juyi duk da tsufan ta, haka kuma Abbu ya kira ta ta ɗauka aka bata Ummu suka dinga kuka da murnan ganin juna, abu ɗaya ya sa farin cikin su raguwa sanda Hajia take ce ma Yaya Bilal "Kar dai ku kuskyra ku dawo min nan ba da ita ba, ku nema mata izini wajen mijin ta, ina so na gan ta."
Take Ummu da Mama da har lokacin take nan suka kalli juna, shiru É—akin ya É—auka kfin Ummu ta kalli Hajia ta wayar tace "Granny, ba zan iya zuwa yanzu ba, amma za ki ganni bayan wata uku in sha Allah."
Da mamaki Hajia ta kalle ta tace "Bayan wata uku kuma? Me yasa sai bayan wata ukun?"
Saida ta sauke ajiyar zuciya ta É—an kawar da duban ta daga fuskar Hajia sannan tace "Saboda ina *idda*."
Da Mamie da Hajia da kuma Yaya Bilal ne suka maimaita kalmar "Idda?" A tare, sai Aisha da tace "Aunty, wai kun rabu da Abban Kuwailat ne?"
Saida ta sauke ajiyar zuciya sosai kafin ta kalli Hajia tace "Zamuyi magana daga baya, labarin mai tsawo ne."
Dan ta kawar da hankulan su sai tace ma Hajia "Ba wannan ba yanzu, Granny ya haƙurin rashin jigon ahalinmu?"
Ai ko dubarar tayi aiki dan take aka koma jimamin abinda ya faru na rashin Alhaji da aka yi. Ganin jikin Mama kam yayi sauƙi da gaske har ma an sallame su saboda bata son zaman lokacin da zasu tafi Abbu ya kalli Mama yace" Hajia, dan Allah muna neman wata alfarma?"
Da kulawa Mama tace "Ba damuwa, ku faÉ—i duk abinda kuke so."
A nutse yana kallon Ummu yace "Muna so ne dama idan Kuwailat ta kamalla iddar ta taje mana ziyara?"
Shiru Mama tay tana nazarin wannan kawaici da aka mata, kafin ta kalle shi tana murmushi tace "Alhaji, na kawo muku Ummu ne yau ba dan na koma da ita ba, daga jiya zuwa yau na fahimci raÉ—aÉ—in da kuke ciki na rashin Ummu, na san ba zamuyi nesa da juna ba, dan haka na kawota ne dan ta zauna da ku matsayin ku na iyayen ta."
Da sauri Abbu ya girgiza kai dan shi sai ya ga kamar irin tayi zuciya ne ya kawo musu ƴar su kenan, dan haka yace "A'a Hajia, ba zamu taɓa raba ki da Kuwailat ba, ƴar ki ce, a ƙalla mu dai yanzu mun samu nutsuwar zuci tunda mun san mu muka haife ta, amma Kuwailat, ta ki ce ai."
Ummu ma dake sauraren su kallon Mama tayi tace "E Mama, ba zamu rabu da juna ba, ke Mamata ce, ina so na zauna tare da su, amma ba haka kwatsam ba, idan na gma idda zan je na kwana tare da su."
Cike da gamsuwa Yaya Bilal yace "Hakane, hkan yayi, Allah nuna mana ranar."
Sai kuma ya kalli Kuwailat ƙarama yace "To amma, za dai a barmu mu tafi da Kuwailat ƙarama ko?"
Kallon Kuwailat É—in tayi kafin tace "Abbana, ba zan iya cewa E ko a'a ba, saboda tana hannun mahaifin ta ne, kuma yanzu na hutun makaranta, idan zata iya neman izinin shi zan fi kowa farin cikin aje wa da Hajia da ita."
Aunty Fa'iza dake manne da Kuwailat É—in ce tace "Ga Eesha ai tasan gidan, sai muje tare da ita mu nemi izinin nashi, dan gaskiya ina so mu tafi da ita."
Abbu dake zaune bakin gado Mama Nuriyya na riƙe da hannun shi ne yace "Bai san mu ba, bamu san shi ba, kamata yayi muje dukanmu sai mu nemi izinin nashi."
Cike da gamsuwa Mama ta jinjina kai tace "Hakan ya yi, sai dai Dan Allah ina mai ƙara baku haƙuri akan auren Ummu ɗin, har ma da sakin nata, dan ji nake kamar ni ce silar komai."
Lokacin da Abbu ke kallon Maman yana nuna mata ba fa komai, ko gaban su take ai haka zai iya faruwa, a lokacin Kuwailat ta matsa kusan Maman nata ta faÉ—a jikin ta kamar za ta yi kuka cikin raÉ—a tace" Mamie, me yasa Abba ya sake ki? Yanzu shikenan ba zaki sake zuwa gidan mu ba? Ni kaÉ—ai zan yi ta zama can?"
Tausayin yarinyar ya sa Ummu rumgume ta tana rintse idanu ita ma cikin raÉ—a tace" Karki damu Kuwailat, komai da kika ga ya faru haka Allah ya tsara mana tun kafin wanzuwar mu, kar ki saka damuwar rashina a gidan mahaifin ki, ya riga da ya yanke hukunci cikin hushi ba yadda na iya, amma ko yanzu ya ce na koma É—akina zan koma ba tare da jayayya, dan ba zaniya rayuwar farin ciki ba tare da ke da shi ba, amma dai ki sa a ran ki Maman ki tana tare da ke, Allah ba zai barki kiyi maraicin rashina ba."
Ƙara ƙamƙame ta Kuwailat tayi tana kuka cike da tausayi, Mama Nuriyya na kallon su ita ma kamar ta musu hawayen, dan ita tsarin nan na brin Ummu a nan bai mata ba gaskiya, tana so ƴar ta ta kasance tare da ita, su shaƙu da juna kamar yadda sukayi da Eesha, duk da ta san zaman ba mai jimawa bane, dan tana samun miji ita ma aure zata yi, amma dai ko yaya ai zasu zauna, sai dai ba zata faɗawa kowa abinda ke ran ta ba dan kar a kalle ta marar godiyar Allah, a tafi a haka ma dai.
*********************
Hankalin Aliyu bai gama tashi ba da yarda ko mahaifin shi tsufa ya fara gigita shi saida ya zo shiga falon Hajia babba ya ji abinda ke faru, ya tara iyayen su duka wai har da Hajia babba yana tambayar a cikin su idan har akwai wacce ta san tana da sauran buƙatuwa ga namiji har yanzu? To ta faɗa mishi shi kuma ya sawaƙe mata, dan baya son shiga haƙƙin kowace a cikin su, ba kuma ya so wata matar ta kai shi wuta, dan haka ya tsare su da wannan tambaya, inda su kuma suka shiga zare idanu suna mamakin shi, to su wace buƙata ce da su saboda Allah akan wannan lamari? Har gwara ma Hajia Atika da ta ji da shekaru goma zuwa takwas da suka wuce ne baya yayi wannan tambayar, to shakka babu da ta amsa mishi sai dai ya ga butulcin ta, amma zuwa yanzu ta haƙura kam ba ta jin wani abu mai kama da hana bawa bacci ita dai, dan haka tana nan har sai tayi takabar sa daga nan a bata nata kason bayan ta karɓi na yaran ta ma.