← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 168

Sashe 75

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wasu da murmushi a fuskar su suka amsa mata, yayin da wasu ba yabo ba fallasa suke kallon ta basu tanka ba, saida ta ƙarasa tsakiyar falon ta tsaya kusa da kujerar da Alhaji yake zaune, saida ta rusuna ta zauna sannan ta aje tasar ta ɗaga kai dan duban Alhajin, ido biyu suka haɗa da Jabir dake kusa da Alhaji yana riƙe da hannun shi sai murzawa yake kamar mai mishi tausa, murmushi ta sake faɗaɗawa har haƙorin makkar ta suka bayyana guda biyu tace "Sannun ku da zuwa.?"

Cikin taushin murya da kuma girmamawa ya sauke idanun shi ƙasa yace "Ina wuni Maama?"

Da fara'a ta amsa da "Lafiya ƙalau, ya hanya?"

Kafin ya bata amsa Aliyu ma dke murmushi yace "Auntynmu mun same ku lafiya?"

Kallon shi tayi shima yana gefe É—aya na Alhajin ta amsa da "Lafiya lau Yaya Aliyu, an zo lafiya?"

Masu yin Ummu ne a É—akin suka fashe da dariya har da Alhaji dake faÉ—in "Ka ji wani shirme a gurin uwar autata, É—an naki kike kira da Yaya kuma?"

Dariya Aliyu ma yayi yace "Abba ai haka take faÉ—a, dama nace sai na zo zaka mana tsakani."

Ummu da kunya ta kamata ne ta rufe fuska da hijabin ta mai hannaye, Jabir dake kallon me ke faruwa a ran shi ya ayyana _"Daga uwa ta gari ta koyi kunya."_

BuÉ—e fuskar ta tayi ta kalli Alhaji tace" Ga furar nan."

Tana faɗa kuma sai ta miƙe tana faɗin" A kawo musu abincin ne?"

Kallon ta Alhaji yayi yace "Ki tambaye su."

Kafin ta tambaye su Aliyu yace "Ai autar Abba ma ta je ta kawowa wannan acicin da ba ya juriyar yunwa, ban san ya aka yi ta jima ba?"

Da mamaki ta kalli Aliyu bayan kallon Jabir da tayi tace "Kar dai motsin ta na ji a madafa?"

Jinjina mata kai yyi yce "Ƙwarai." Yunƙurawa tayi ta miƙe tana cewa "Bari na duba ta kar ta min ba daidai ba."

Ta y tako huÉ—u zuwa biyar a falon Hajia Asiya da ke zaune tuntini tana ta hararen Ummu ta gyara zama cike da jin an mata ba daidai ba tace "Kenan da furar da abinci duk ke kika gyara?"

Tsayawa Ummu tayi ta kalle ta tace "E Hajia."

A daƙile ta amsa da "Ya yi kyau." Sai kuma ta kalli Alhaji tace "Na ɗauka aikina ne, sannan yarona ne zai zo, na sa ƴan uwan sa sun mishi girki, ya zamuyi kenan? Na ƴar gold ka zaɓa masa ya ci saboda mu ba mu iya ba?"

Dafe gaban goshi Alhaji ya yi, me ye na wannan maganar a gaban yara? Ita sam abun faɗa da tsegumi ba ya mata kaɗan? Kuma ka san à inda zaka yi maganar mana, shikenan ko ina ma sai ka saki baki? Kallon ta yayi dan kar maganar tayi tsayi yace" Shikenan, ki basu wanda kika dafa ɗin."

Sai kuma ya kalli Ummu yace" Maman Kuwailat k...." Da sauri Ummu da abin ya ƙuna mata rai sosai har idanun ta sun cika da hawaye tace" Shikenan Alhaji, a rayuwar nan dai ai ba'a rasa maciya abinci."

Tana faÉ—in haka ta juya ta bar falon, da kallo duk suka bita musamman da Hajia Asiya ta harare ta tace" Munafurcin banza, haka kullum kike nuna ke ta Allah ce ai."

Tunda aka fara maganar nan kan Aliyu ke ƙasa haka ma Jabir, da yana daga cikin ladabin da suka koya a karatun su, Aliyu na cike da wannan takaici ya ji ta ci gaba da faɗin" In gama kashe kudi dan kawai ɗana dana jima ina jiran dawowar shi, sai a wani ce wata wai ta dafa, akan me to? Mu bamu iya bane? Ko guba za mu saka mishi? Ba dan ma an zo mana da baƙo ba, abincin ma ai sai mu bashi a baki."

Lumshe idanu Jabir yayi wanda ya ji an koma kan shi kuma, a hankali ya buÉ—a idanun shi tare da yin tsam ya tashi tsaye yana sakin hannun Alhaji, bai yarda ya saurari kowa ba ya kama hanyar fita dan basu wuri su gana matsayin su na alhali guda, saida ya fice daga falon Khamis ma ya bi bayan shi, hakan yasa ma shi da Khamis din suka nufi wajen Hajia Lubabatu dan gaishe ta.

Khamis na fita a bayan Jabir Alhaji ya kalli Hajia Asiya cike da takaici yace "Ke har abada ba ki iya tausa bakin ki ba, me ye haka dan Allah? Kamar wata ƙaramar yarinya ki tsaya kina abu irin haka, me ye wani kwana da girki a wannan shekarun namu? Suna da mahimmanci ne yanzu a rayuwar mu?"

Tsaki ya sake ja ya kawar da kan shi yna kallon yaran da ta ci albarkacin su da ya datsa mata maganar da ta fi haka sannan yace" Yadda kike jin Aliyu ya zo gidan ubaan shi, haka Jabir ma nan gidan uban shi ne, Allah ya azurtani da komai na rayuwa, daga ciki har da yara maza da mata, sai dai n ba fi saka tsammanin samun rahamar ubangiji ta dalilin taimakawa yara irin su Jabir, ban rantse miki ba, amma kuma ban ce miki zan yi kaffara ba idan har na ce na fi ganin zallar soyayyar da uba ya kamata ya samu daga gurin yaran da ya haifa a idanun Jabir, wataƙila kema kin ga haka, ko kuma kin gani kin take sani saboda ƙin gaskiya."

A hankali ya shiga kiciniyar tashi tsaye, hakan yasa Aliyu miƙewa ya taimaka mishi ya tashi yana jin shi ma rigimar maman shi tasa yake son ci gaba da zama a can, amma ya zai yi? Mahaifiya ce, dole yayi haƙuri da ita. Saida suka fara takawa Alhaji ya sake faɗin "Kar ki sake min irin haka, duk ƙiyayyar ki da Jabir ki nuna mishi ita a bayan idanun shi, amma ban da gaban idanun shi."

Ficewa sukayi tare da Aliyu da shima abun bai mishi daÉ—i ba, saida suka fice É—aya daga cikin yaran na Hajia Atika tace "Lallai ma, yanzu Abba akan wani bare yake faÉ—a miki haka? Wannan idan gaban shi ne ai sai ya raina ki."

Da rashin sanin abun yi Hajia Asiya tace "Hmmmm!"

*Suna* ƴar hirar ƙasar da suka baro da Hajia Luba Kuwailat ta shigo da kwando ɗauke da kwanukan abinci Ummu ta zubo ta ce ta kawo ma Hajia ba sai an mata girkin dare ba kawai, wannan abincin da ta kawo Khamis ya ce a zuba mishi yana jin yunwa, sai kuma ya kalli Jabir yace "Alaramma, a zuba da kai ne? Na ji Yaya na cewa ba ka juriyar yunwa."

Kallon Khamis É—in yayi d wani irin kallo yace "Kusa a buga a jarida mana, naga sai maimaitawa kuke, tabbacin ni mutum ne fa kenan."

Dariya Khamis yayi yana kallon Kuwailat dake zuba abincin, inda shima Jabir ke kallon hannayen ta dake da ragowar lallen ta dake daf da zubewa, cikin wata nutsatsiyar murya Jabir dke kallon Kuwailat yace" Zuba da ni."

Kallon shi tayi ta saki murmushi tace" To Yaya, ai nasn idan ka ci abincin nan da muka girka ni dq Mamie za ka daina hushi dani."

Kallon ta Hajia Luba tayi tace" Subhanallah! Hushi kuma ? Ke da Yyan naki? Daga zuwan shi?"

Kallon ta tyi tace" E mana Mama, wai dan ban gaishe shi da wuri bane yake hushi dani."

Dariya Hajia tayi tace" Any dai, to amma dai zuba mishi abincin mu gani zai daina hushin ko kuwa."

Tana gama zuba musu ta aje gaban su tare da ɗauko cokali, tana dawowa ta samu Jabir zaune dangal dangal ƙasa ya wanke hannun shi ƙofar ɗaki har ya saka ya fara cin abincin da ya saka shi haɗiyar yawu, da mamaki ta kalle shi tace" Lahh ! Yaya, kai baka cin abinci da cokali?"

Kallon ta yayi tare da sakin wani tattausan murmushi ya nuna mata tafin hannun ta yace" Me yasa Allah ya mana wannan? Saboda abubuwa dayawa da basu misaltuwa, daga cikin ladubban cin abinci kuma akwai ci da hannu dan ya fi albarka, sannan da tanÉ—e hannun bayan gama cin abincin, dan haka kar a min dariya idan an ga ina lashe yatsuna."

Dariya duk sukayi har da Khamis da yace" Yaya mai wayo, wato ka kare kan ka daga tuhuma tun kafin ka aikata laifin."

ÆŠaga mishi gira Jabir yayi alamar" E mana." Sauka ci gaba da cin abincin su, suna tsaka da ci Aliyu ma ya shigo suka gaisa da Hajiar, lokacin kuma aka fara kiran sallah la'asar suka nufi masallaci, suna dawowa Jabir ya shirya a É—akin da aka ware musu shi da Aliyu dan kuwa Aliyu ne ya ce maa Abba a haÉ—asu É—aki É—aya dan sun saba kwana tare, yana gama shiryawa tare da Aliyu da Khamis suka kaa hanyar zuwa gidan mahaifin Jabir dan duba shi.

Tiryan-tiryan suka bi kwatancen gidan, suna isowa inda Jabir ke kyautata zato ya fita yana faÉ—in "Bari na fara dubawa na tabbatar ko nan É—in ne."

Aliyu ma fita yayi daga motar ya zagaya yana cewa "OK, shiga ka duba, zamu jira ka a nan."

Cikin nutsuwa yake takawa har ya isa daf da ƙofar, a buɗe ƙofar take sai matsakaicin soron dake shafe da siminti, tsayawa yayi da niyyar yin sallama, sai dai kafin yayi sallamar ya ji muryar mahaifin shi a zahiri wacce ya jima bai ji ta ba, ya so jin shauƙin na jin wannan muryar cike da begen haɗa idanu da mahaifin nashi, ya ɗauka zai same shi cikin farin ciki marar misaltuwa, ya ɗauka zai same shi cikin nutsuwa ne da amince, amma sai yake jin muryar shi na tashi da irin yanayin nan da ya san shi da shi, cikin ƙaraji da ɓacin rai yake faɗin _"Shikenan Bara'atu, ba kin ce haka ba? To na daina yi ma Uzeifatu faɗa dan ta dinga tayaki aikin gida, amm ki sani akwai ranar da zaki yi dana sani, dan ni nasan ba yadda za'a yi a raini mace ba tare da koya mata aiyuka irin na gida ba, ki ci gaba Bara'atu."
Chapter 75 · 0% Book details