Sashe 153
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da haka sukayi sallama Ummu ta miƙe ta cire hijabi, ruwa ta watsa sama sama ta fito shima dan tayi bacci ne dan ta wartsake sosai, doguwar rigar leshe ta saka da ta mata kyau ta kama jikin ta sannan ta yafa mayafi, wayar ta kawai ta ɗauka sannan ta saka kuɗin da za ta bawa yaran su sha ruwa a hanya sanan ta saka takalmi flat da suka dace da kayan ta, ba kwalliya tayi ba amma ta yi kyau sosai ga ƙamshi da take bazawa ta fito amaryar ta sak.
Tana buɗo ɗakin ta ci karo da Jabir dake ɗan dube dube yana so ya ga inda kwanukan abincin da aka girka masa yake, jin motsi ya sa shima ya kalli wurin, kyan da ta masa a idanu ya sa ya ɗan kafe ta da idanu har ta rufe ƙofar da makulli ta fara takowa tsakiyar falon... *Ba ta* ce da shi komai ba, hasalima tun kallon farko ba ta sake duban wajen da yake ba, hakan ya ƙona masa rai sosai, musamman da ya ga ma kamar shirin fita ne ta yi, d gaske fita ne z ta yi? Zuwa ina? Wa ta faɗa ma? Da izinin wa? Shi ga sakarai? Soko? Shashasha da bai san me yake ba kenan?
Dama dai tunda safen nan azumin shi ya warware, dan da ya fita kafin su yi sallah shi da su Aliyu a masaukin da Fahad ya sauke Mansur saida ya yo wanka a ɓoye, bai yarda su Aliyu suka gane ba dan ya san zai sha tsiya, dan haka yanzu ma yake jin zai kuwa sake kirta wani sabon rashin mutumcin da zai kafawa Maama tarihin da ba za ta manta da shi ba.
Ganin taƙim taƙim ta kama hanya yasa shi ɗan karkata kan shi yace "Ina abincin? Zan kai wa baƙona ne."
Irin juyowan nan ce tayi kamar kana tafiya saman titi a maka oda, to wannan Æ´ar juyawar da zaka yi ai ba'a bakin komai take gare ka ba, haka Ummi tayi tare da faÉ—in "Na faÉ—a maka dama ai ba zan iya ba."
Da ƙarfi Jabir ya lumshe idanu yana ɗan tauna leɓen shi, bai buɗa idanun ba har sai da ya ji tana ƙoƙarin buɗe can ƙofar gida zata fita, da sauri ya juya sai ya hango ta daf take da fita dan har ta buɗe ƙofar, da sauri ya ɗaga ƙafar shi ya fito farfajiyar a kausashe yace " *KUSLSUM*."
Har za ta fita, amma abinda ta ji ya dakatar da ita ta juyo da matsanancin mamaki tana kallon Jabir har ƙanƙance idanu take yi irin ɗan ta nan ya kira sunan ta, ta manta da wasu yaran ma suna kiran sunan iyayen da suka haife su ne duk da tana ɗaukar hakan a matsayin rashin girmamawa, amma sai ta sauke numfashi ta girgiza kai irin _"Allah ya shirya min kai."_ Ɗin nan tare da sake jawo ƙofar za ta fita, daga inda yake yana kallon ta a hassale yace" Ina zuwa?"
Sake juyowa tayi a yangance tace" Gidan mu."
Fuska a haÉ—e yace" Koa ciki, babu inda zaki je."
Wani sakaran murmushi tayi tana girgiza kai tace" Jabi..." Bai bata damar faÉ—a masa ya fa daina yi mata irin wannan karan tsayen kawai ya É—an tako yana faÉ—in" Idan na sake maimaita miki ba zaki ji daÉ—i ba wallahi, kuma ba zaki sa ni kaffara ba."
Gyara tsayuwa tayi ta haɗe fuskar ta irin za ta yi halin nan, duk da ta ga shima fuskar shi haɗe tale sosai saboda ɓacin ran ya masa yawa, sau nawa yana cexa tayi ta na ƙin yi, dan ta nuna masa bai isa ya zaa mijin ta ba ko me? Ya umarce ya ta ƙi yi, bayan ta gaya masa da rashin kunya shine ma a gaban shi zata fita kula bai sani ba, to wallahi sai ya zane ta idan ya sake cexa ta koma ba ta koma ba yanzu, kula ba zai yi kaffara ba.
Ummu dake kallon shi cike da tsiwa tace "Na gaya maka gidan mu zan je, gashi nan fa yana kallon namu gidan, su Aisha ne zasu tafi, kaga ko ai ba zaka hana ni yi musu sallama ba."
Ƙara cije leɓen shi yayi yana shaƙiyin murmushi, daman shi ya kalla bai ga abinda ya so gani ba, sannan ya kalli hagun shi, nan ma dai bai ga abinda yake hasasowa ba, da ɗan sauri ya juya da niyyar komawa ɗaki, sai kuma ya tuna a aljihun shi akwai cazar wayar shi da ya fita da ita, sai kawai ya dakata ya saka hannu aljihu ya zago ta.
Riƙon da ya ma cazar ya sa Ummu gyara tsayuwar ta tana kallon shi da son gane me yake nufi? A daƙile yana kallon ta ya nuna mata hanyar komawa da yatsa yace "Wuce nan, ba zan sake maimaita miki ba."
Irin mamakin nan neya kashe ta, hasbunallah wani'imal wakil? Wai me yake nufi? Me yake so yayi da abar hannun shi? Ko da yake an ce wai ga wuri ga waina, bari ta É—an masa tsayayya ta ga me zai faru, dan haka ta gyara tsyuwar ta tace" Jabir, ka tabbata ba ka shan komai? Kai yanzu ko Kuwailat ka hora da bulala bare ni uwarrrrrrrrr....Aaaaaaazaaaa."
Subhanallah! Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Ita Jabir ya tsala wa bulala a ƙafafu? Ihun da tayi ba ta ankara bane, sam da ta ga yana nufo ta bata ɗauka da gasken dukan ta zaiyi ba, amma sai taji saukar cazar nan a ƙafafun ta da gasken gaske da ya saka ta zabura ta juya ta sake juyawa ta shiga diddira ƙafafu tana kallon shi sai salati take yi. Duk da ya ji saukar bulalar da ihun ta a ƙahon zuciyar shi, amma sai ya share kawai dan tanƙwarata yake so yayi, sake nuna mata ƙofar yayi da ƙarfin murya yace "Wuce nace."
Kukan ke son taho mata, amma take daurexa bata so ya É—auka shi ya sakata kuka da bulalar nan, sai kawai take daurewa tana faÉ—in "Jabir, Jabir wallahi ka ji tsoron Allah, kag...."
ÆŠaga cazar ya sake yi ya kuwa tsula mata a baya tare da rintse idanun shi.. Haba wa? Ai sai Ummu ta daka tsalle tare da sakin kuÉ—in hannun ta da wayar ta ta kwamtsa ihu tana kiran "Wayyo... Wayyo, mama mama mama.. Aunty, auntyna..."
Sai kuma ta durƙushe ƙasa a rikice ta rarrafa ta cakumo rigar Jabir tana kallon fuskar shi hawaye na zubo mata a kumatu, cikin tashin hankalin da ita duk shekarun da ta ɗauka gidan Alhaji bata taɓa riskar kamar sa ba tace" Yi haƙuri, zan yi, zan dafa wallahi, zan dafa, zan dafa Jabir, daina dukana hakanan kaji? Wallahi zan maka girkin yanzu."
*Wani* irin girma ya ji kan shi ya masa da ya saka shi haÉ—e fuska tamau sannan murya a tsume yace" Wuce to."
Da gudu gudu ta miƙe ba tare da tsayawa ɗaukar wayar ta ba, hasalima ta manta da su kawai ta wuce tana kama gyalen ta dake neman faduwa, dole tayi gudun ceton rai, dole ta ƙaurace ma Jabir, tunda aljanun shi har duka suke yi, ba shakka za ta faɗa wa su Anna su sama mishi magani, idan ba haka ba ta koma gidan su da zama, dan matsalar masu irin wannan larura kai ba zaka iya ramawa ba, kula idan sun illaya banza a banza suka illata ko alƙali ba zai ƙwatar maka haƙƙin ka ba.
Shi ya ɗauki wayar da kuɗin ya kai mata falo ya aje, sannan ya zauna ya kira Fahad ya ce dan Allah shi ya taho da abincin sai su kai wa Mansur, Ummu kuma yayi niyya sai ta dafa shi, idan ya dawo anjima ya ci tunda ba azumi yake ba. A rikice ta shiga madafa ta ɗora tukunya ba tare da ta san me za ta dafa ba, saida ta ji tukunyar tayi zafi ne ta zuba ruwa kawai ta rufe ta fito, tana shigowa falon da ta gan shi zaune wallahi da gaske saida gaban ta ya faɗi, cikin sissine kai ta raɓa shi sosai kamar za ta bi bango sannan ta shige ɗakin ta, kaya ta canza kafin ta fito gadan gadan ta fara aikin, tana yi kuma tana share hawaye idan har ta tuna yau ita ce namiji ya daka, namijin ma wai Jabir, Billahillazi Alhaji Kabir lallaɓata yake yi, ita ke masa laifi kuma ya lallaɓa abar sa har ma ya mata kyauta na baki da ta turo gaba saboda hakan na birge shi, ama yanzu kawai sai a haɗata da mai iskokai, ya zo yayi ta narka a cikin gida? Yanzu da irin fitsarar nan da yake mata idan ya mata a gaban mutane fa? Shikenan darajar ta sai ta zube? Ko da yake ai ta ji an ce hantiti da jibda suna maganin iskokai ko? Wataƙila ta jaraba yi masa kafin su Anna su kawo mata ɗauki, dan wata rana kasheta zaiyiaa gidan ba wanda ya san ma aikin shi ne.
*Alhamdulillah.*
👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
*RUBUTACCIYA*

_NA_
*SAMIRA HAROUNA*
_SADAUKARWA GA_
*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_
*Tallah, tallah, tallah*
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_
Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes