← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 168

Sashe 96

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ameen Ya Allah." Ta faÉ—a a tausashe, sannan kuma ya sake cewa "Sai kuma maganar hushin nan da kike da shi Ha.."

Da sauri Hajia ta katse shi da "Ni bana hushi da shi, kawai ina so ya gane gaskiya ne, amma abinda ya faru ya zame min izini, ba zan yarda na kwanta da ɓacin ran ɗaya daga cikin su ba, dan ban san ko zan farka ba."

Nan ma dai da farin ciki ya amsa mata sannan yace "Sannan zan ga Bilal na masa magana akan abinda ya kamata a sama wa Fahad É—in ya fara yi shima, dan bai iya nema ba ko kaÉ—an, a bashi ya kashe kawai ya sani, to yanzu tunda za'a masa aure ai ya kamata ya fara sana'a shima."

Jinjina kai tayi tace "Hakane, Allah ya ƙara shirya mana su, amma dai ina da shawara."

Cike da kulawa yace "To, ina jin ki?"

A nutse tace "Yadda Alhaji ke ma yara idan zai ɗora a kasuwa, kai tsaye ba ya saka su a harkokin shi, yana fara basu kuɗi ne su ja jarin su na kan su, a shekara ya kan buƙaci da su dawo da abinda suka samu, idan kuɗin sun ƙaru ko da kaɗan ne shine yake alamta mishi yaro na iya tattalawa, to daga nan yana iya saka yaro a kowace irin harkar sa, idan kuma ya salwartar, to yana ƙara masa ne har sau uku, to daga nan ban san matakin da yake niyyar ɗauka ba, dan gaskiya daga Bilal zuwa Mukhtar da Sabeer babu wanda aka sake ba wa jari sau biyu, na farko suka ɗora riba a kai su kawo sai su fara fita tare da shi, to shima Fahad a masa haka mu gani ko Allah zai sa a dace."

Cikin jin daɗin shawarar Alhaji Abbas yace" Wannan ai shawara ce mai kyau, hakan ya yi sosai, ina ga ma ni zan bashi jarin ya fara juyawa, tunda yanzu komai dake nan na magada ne, bai kamata a taɓa ciki ba, zan bashi ko miliyan biyu ya fara mu ga kamun ludayin shi."

A hankali ta girgiza kai tace "Sun yi yawa, ka bashi É—aya ya fara jarabawa mu gani."

Dariya yayi yace "To ai kinga bayan wata ɗaya akwai hidimar auren shi da za ta taso, dole zai buƙaci kuɗi."

A sanyaye tace "Duk da haka, ni zan É—auki nauyin auren nashi."

Murmushi yayi yace "To shikenan, Allah ya saka miki alkairi, Allah kuma ya ƙara shirya mana shi."

Amsawa tayi da "Ameen." Kafin suka ɗn taɓa wata hirar da ba ta shafi Fahad ba, ya dai jima suna tattaunawa kafin ya koma, inda Fati da suke waje ta so ta bi shi ya ce ta jira maman ta na zuwa sai su koma tare.

*Alhamdulillah.*
15/08/2023, 20:14 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*RUBUTACCIYA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

_NA_

*SAMIRA HAROUNA*

_SADAUKARWA GA_

*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_

_Bismillahir- rahamanir-rahim._

*45*

Kamar wacce ta dawo daga wata uwa duniya a ƙafar ta tsabar yadda ta shigo a kasalance, watsa ruwa kaɗai ta yi ta kwanta bayan sun yi saida safe ita da Kuwailat, Alhaji kuma tun daga farfajiya ma sukayi sai da safen, bacci ta so ya ɗauke ta mai nauyin gaske, sai dai tana kwantawa matsalar ta tayi mata sallama, haka ta shiga saƙa da warwara na abinda ke damun ta.

Gyara kwanciyar ta tayi a karo na tsohon dare, kamar kuma motsin ta ake jira sai kuwa wutar gidan gaba ɗaya ta ɗauke ɗiff! A hankali ta lumshe idanu dan ta san yanzun nan zafi zai gigita mata lissafi, shiru tayi tana sauraren da gaske marar ta ce ke motsi? Ko da yake ba sabon abu bane ai, dan haka tayi tunanin bari ta jaraba shan Lemun tsami mana a lipton yadda take jin maza na yi, shin zai yi mata ita ma? A hankali ta miƙe tare da lalubar wayar ta ta fito daga ɗakin.

Karo sukayi da Alhaji zai shiga ɗakin dake daf da madafa wanda b ɗaki bane, kawai an masa ƙofa ne sai ka ɗauka ɗaki ne, amma inda aka aje generator ne tun ma kafin ya auro Ummu yake nan, kasancewar babban generator ne dake ɗaukar gaba ɗaya unguwar, kallon ta yayi yana murmushi yace "Hajia, zafi ya tashe ki ko?"

A kasalance ta amsa mishi da "A'a, madafa zan shiga."

Da mamaki ya dube ta yace "Ba dai yunwa ta tashe ki ba?"

A hankali ta furta "Kusan haka."

Da kallo ya bita ta shiga madafar, buɗe ɗakin yayi da makulli ya haska da fitilar wayar shi ya hangi generator ɗin dake cikin wani irin babban keji, barin ɗakin yayi buɗe tare da leƙa madafar ya hangi Ummu dake tsaye tana ɗauko maysakaiciyar tukunyar da zta ɗora ruwan zafi yace "Bari in duba in ga Jabir ɗin ko ya samo man, idan babu ko na motar ki sai mu tsiyaye mu tayar da gen ɗin ko?"

Juyowa ta yi, da gaske dai shi so yake ya dinga jan ta da magana, dan kar ya ga ko tana wulaƙanta shi ne tayi murmushin yaƙe kawai tace "To shikenan, ai dai kun san mai yana tsada ko?"

Dariya yayi, ko ba komai ya ji daÉ—in yadda ta amsa mishi sannan yace "Nufin ki siya zan yi kenan? Ko dan Æ´ar ki ai kin bamu kyauta ko?"

Murmushi tayi mai sauti kawai tace "Shikenan to, na bayar."

Fita yayi ita ma ta ci gaba da abinda take yi, Alhaji kuma ƙofar gida yayi tsaye yana jiran Jabir wanda tun kafin a ɗauke wutar dama yayi tunanin sai an ƙara mai a gen ɗin, hakan yasa ya zo ɗakin su, sai ya samu Aliyu kwance Jabir ya faɗa masa magani ne ya sha na zazzaɓi ya kwanta, dan haka ya ce shi bari ya je ya samo man bakin hanya, haka ya fita Alhaji na ma Aliyu sharrin ragon maza ya zama ba zaki ba tunda canjin yanayi ya kwantar da shi, dariya Aliyu yayi yace mishi _"Jabir ma fa yayi kalar nasa zazzaɓi Abba, kawai dai dan baya so komai sai ka sani ne, kuma shi nashi zazzaɓin har da rashin mace ya jaw..."_

Da sauri Alhaji ya kwaɓe shi da _" Aliyu, bana son maganar banza."_

Ya É—an jima nan kafin Jabir ya dawo É—auke da jarkar mai a ciki, da mamaki Alhaji ya tare shi yana faÉ—in" Jabir, har man nawa ka siyo mana?"

Murmushi kawai yayi bai ce komai ba, raɓawa yayi zai wuce Alhaji yace" Kawo na shiga da shi ciki ko?"

Da sauri Jabir ya kalle shi yace" Subhanallah ! Abba ni fa?"

Murmushi Alhaji yayi na ganin yadda Jabir ke ɗauke da jarkar man ka rantse da Allah man kaɗan ne a ciki bayan kuma cike yake, ko da yake ai Jabir ya yi ga-ruwa, dan haka tun yana matashi ya saba ɗaukar wannan jarkar cike da ruwa (biyu ma yake haɗawa☹️).

Bayan Jabir ya bi yana faÉ—in "Muje to sai ka juye."

Suna kusan shiga ɓangaren Alhaji dake gaba ya dakata saboda kiran da aka masa a waya, wanda ya kira dole ne ya amsa duk da 12 na dare ne lokacin, amma dake ya wakilta ya zauna inda ake can yanzu haka ana sauke masa kayan shi, to kiran zai iya yiwuwa da matsala ko akasin haka. Dan haka ya dakata ya ma Jabir alama da ya wuce tare da faɗin "Ina zuwa, je ka kawai ɗakin buɗe yake ka juye man."

Cire takalmin shi yayi ya shiga falon da sallama a tausashe da kuma ciro wayar shi ya kunna fitila. Ummu dake tsaye ta yanka lemun tsami guda biyu, na uku ta ɗauka za ta yanka sai ta ji sautin sallamar Jabir cikin wannan ƙasaitacciyar nutsuwar, bata san dalilin da ya sa gaban ta ya yanke ya faɗi ba, cikin ta ya hautsina gaba ɗaya, hakan yasa ta juyawa da sauri da razanin me ya shigo da shi yanzu? Kar dai kuma ya shigo nan gashi ita rigar bacci ce jikin ta iya guiwan ta kuma.

Garin wannan ƙoƙari da firgici juyawar da ta yi wuƙar nan ta sauka a tsakiyar tafin hannun ta, yadda yankan ya ratsa ta ya ta rintse idanu da ƙarfi tare da sakin wuƙar ta ɗaga murya a sirance ta furta "Ahhhhhhh! Subhanallah!"
Chapter 96 · 0% Book details