Sashe 150
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana shiga É—akin da irin zafi zafin nan ya tsaya gaban ta har lokacin tana zaune kan gadon, fuskar shi a haÉ—e yace "Ba ki ji na kira ki bane?"
Cike da ƙarfin hali irin na Ummu ta masa wani kallon sha ka tafin nan sannan ta ɗauke kan ta tace "Ai ban ɗauka da ni kake ba."
Jinjina kai yayi yace "Ok, dama ba ke kaÉ—ai bace a É—akin nan?"
A nutse ta miƙe tsaye tana aje wayar ta tana kuma kallon shi tace "Jabir, ai kasan ko ni dabba ce bai kamata ka min kiran da ka min ba wai zo nan, sannan ka tafiyar ka, ni na ɗau..."
Bai so haka ta fara faruwa tsakanin su ba, bai so a ce nan kusa wani abu ya fara haɗa jikkunan su ba, to amma ya ga Ummu fin ƙarfin shi take so ta yi, abinda ya hassala shi kenan da azama cike da jarumta ya zura hannun shi ya damƙo damtsen ta tare da jawo ta jikin shi.... Yadda ta faɗa jikinshi shi kuma ya saki damtsen nata sai ɗaya hannun shi da yayi gaggawar zagaya shi ta ƙugun ta ya haɗa da na shi ƙugun dan kar ta samu damar zame masa har sai ya faɗa mata abinda yake son faɗa.
*Amma* yana dora hannun shi a ƙugun nata sai saman wannan jarababbiyar *jigidar* dake rikita mutane bayin Allah... Hannun shi ne kawai ya taɓa jigidar, ya ji shatin ta tare da jin sautin ta saboda taɓawar da ya ma jigidar, wani irin tsammmm! Jikin shi yayi ya amsa har saida ya ji tsigar jikin shi ta tashi, da zafi ne ya riƙe ta dan ya kora mata nashi kashedin ta gane nashi haukan ya girmi nata fa.
Amma sharrin shedan dake saka wa ɗa tunani marar kyau akan maaman shi, sai ya shiga dan shafa ƙugun nata da duka hannayen nashi biyu yana sake jin yawan jigidar a ƙugun ta.
Idanun ta yake kallo ba wannan rusunawar da wani kakkaucewa, kamar yadda take kallon shi yana hango tsana da jin haushin shi a idanun nata da suka rikiɗa tsabar takaici da baƙin ciki kuma sun mata taff da hawaye. Cike da shaƙiyanci yake jan duk jigidar da ta dira a hannun yana tantance yadda suka saki ƙugun nata da kuma zaren da aka yi ɗaurun su da ita, mafi aksari zaren yana ja, bai fi uku zuwa huɗu ba da ya ji zaren su bai jawu ba sanda ya ja shi, matso da fuskar shi ya sake yi daf da ta ta, wanda hakan yasa Ummu saurin kawar da kan ta hawaye na silalo mata a kumatu.
Yatsu biyu ya sa ya riƙo haɓar ta tare da juyo da kallon nata ga fuskar shi, daga leɓen ta da ta cije zuwa kan hancin ta da idanun ta dake zubar ruwa yake ƙarewa kallo, sai yake ji a zuciyar shi _"Ashe haka Maama take da kyau idan aka ƙure ta? Ashe haka jikin ta ke da laushi kamar na mage? Ashe haka jikin ta ke fitar da wani ƙamshi mai daɗi?"_
A zahiri kuma wani narkakken kallo yake mata amma muryar shi a É—an kausashe yace" Wai ni kam *haihuwata* kikayi ne? Da komai komai nayi sai kin ce wa ye wa ye, to na faÉ—a miki bana son tashin hankali, idan na ce kiyi kawai kiyi ba sai na maimaita ba, yawan hayaniya ciwon kai yake saka ni, sannann...."
Yatsa biyu ya sa ya kamo leɓen nata da ta cije ya ciro shi daga cikin bakin nata ya ɗan matse leɓen nata, hakan yasa bakin ta buɗewa har ya ji iskan kanunfari ya daki hancin shi da ya saka shi ƙara matsa kan shi kusa da fuskar ta sanan ya ɗora da" Kuma bana son sunan nan *Jabir*, ina dai buƙatar canji daga bakin ki, ba girmamawa bace mace ta dinga kiran sunan mijin ta babu sakayawa, kin gane?"
Za ta iya rantsewa a lokacin babu jini a jikin ta bayan ruwan da suke fitowa a idanun ta, haƙiƙa yau baƙar rana ce a gare ta, kuma bata jin zata iya gafartawa iyayen ya da wuri akan abin da suka yi mata. Jabir kuma bai sake ta sai ma ƙara tambayar ta" Na ce kin fahimta?"
Ƙura masa idanu kawai tayi tana kallo, hakan yasa Jabir busa mata iska a idanun nata yace" Na ce kin gane? Ko sai kin ji a jikin ki?"
Kafuwa da son nuna masa shi ba komai bane ya sa ta ƙi amsawa, shi kuma dake namijin duniya ne sai ya ɗaga rigar ta tare da zura hannun ta cikin rigar ta ta, da sauri ta lumshe idanu saboda wani irin tartsatsi da taji ya dira a jikin ta saboda sanyin tafin hannun shi da ya taɓa fatar jikin ta har saida ta ja wani siririn numfashi, yanzu kam a ainahin jigidar ya ɗora hannun yna lalubawa ba tare da wani abu ya masa shamaki ba, ɗaya daga cikin jigidar ya kamo wa ce ta kasance ta zaren roba, yana kallon fuskar ta ya sake nanata "Kin gane nace? Idan baki amsa min ba da ɗaiɗaya zan cire wannan jarabar dake tayar mana da hankula."
Cissssss! Jin ƙarar cirewara jigidar ta yasa ta saurin buɗa idanu ta juya inda ta ji duwatsun na zuba, a firgice ta kalle shi da idanun ta da sukayi ja har kwallin da ta saka ya fara zubowa, ganin ta kalle shi sai ya ɗaga mata gira cike da shaƙiyanci yace "Kin fahimci abinda na faɗa? Kuma za ki gyara?"
Ɗan mutsu mutsun ƙwatar kan ta ta fara yi tana girgiza kai wasu hawaye na ziraro mata tace "Jabir ka daina, ka daina wulaƙantani haka Jabir babu kyau."
Ciss! Ta sake jin katsewar wata jigidar, da sauri ta matse bakin ta saboda kuka ke son kubce mata irin wanda za ta buÉ—e bakin nan, cike da dagiya shima ya sake jan wata jigidar ta cire yana faÉ—in" Zan ga bayan su, sannan na koma kan ki, dan dama wannan ba abun da ya kamata na same ki da su bane idan nayi niyyar *shiga gonata*."
A haukace ta kalle shi cikin tashin hankalin jin yana tunanin ita Ummu har zata iya yi masa saken da zai iya hangen gonar nan bare har ya shiga, da sauri ta ƙara ƙoƙarin ƙwacewa tana faɗin" Jab... Shikenan naji, na fahimta."
Tallabo haɓar ta yayi abinda ya sa ta kenan rintse idanu saboda kunya a ce Jabir ne haka ke taɓa jikin ta, shi kuma yana kallon bakin ta dake ta saa shi haɗe yawu yace" Oya Maama! Me ye sabon sunan nawa?"
Cikin jin zafin wannan rashin kunya da yake yi mata ta É—aga murya tace" Jabir ka sake ni mana? Ya zaka m..."
Yatsar shi manuniya ya ɗora kan laɓɓan ta ya furta" Shiiiiiii! Ni mijin ki ne, ba wawan d zaki iya ɗagawa murya haka ba, kin gane?
Saida ta ja majina sannan ta jinjina kai alamar e dan ta kula kawai Jabir dama dai bai karanto komai ba, wataƙila Aliyu rufa masa asiri yake yi, ama dole ya ƙware a fitsara dama. A hankali ya fara sakin ta har ya raba jikin shi da nata, bai tsaya ɓata lokaci ba ya juya zai fita yana faɗin "Ina jiran ki yanzu, ko na dawo na ɗauke ki."
Saida ta ga fitar shi da sauri ta faɗa kan gado tna dafe kan ta ta fashe da wani sabon kuka, tsakanin ta da Allah take kuka tana faɗin "Ya Allah, Allah kana gani, shi ɗin ƙanena ma na biyu, amma *sanadin aure* yana min rashin ladabi, Allah idan bashi da lafiya ne ka bashi, idan kuma da gangan yake min saboda raini Allah ya nesanta ni da shi, dan in haka ta ci gaba da faruwa zan iya mutuwa dan takaici."
Tana cikin tunanin nan ta ji muryar Jabir irin ka haÉ—u da kakar kan nan da kake tsokana yana faÉ—in "Maama, da gaske yunwa nake ji, kuma idan yunwa ta jigata ni rikicewa nake, dan Allah ki zo ki taimaka min."
Ƙwafa Ummu tayi ta taso a fusace ta fito daga ɗakin ta ma manta da bata so ya gan ta da wannan kayan, tana zuwa gaban shi ta tsaya irin ƙiƙam ɗin nan tana kallon shi cikin muryar da ta sha kuka tace" Me zan maka?"
Saida ya ɗaga kan shi ya kalle ta sosai, wato Maama dai har yanzu da sauran ƙuruciya, ba zaka ce ita ta haifi budurwar nan ba Kuwailat wacce yanzu yake mata kallon *ƴa* tunda maman ta yake aure, sai kuma ya kalli ledar gaban shi yace" Wannan zaki gyara min."
A fusace ta ɗauki ledar, sharrin zuciya da rabon ayi sai hannun ledar ya cire lemu orange da ayaba suka faɗo, hakan yasa shi kallon ta a ɗan fusace shima, ganin za ta duƙa ta ɗauke da sauri ya miƙe ya zagaya yana mata alama da hannu da ta bari yana faɗin "Bar shi kawai, zan iya ma."
Cak ta dakata dan ya gama ɗaure ta saboda tuni ya duƙa yana ɗauke kayan shi, cikin ledar ya mayar sannan ya aje kan teburin ya miƙe zai nufi madafa sai kuma ya kalle ta yace "Sanin kan ki ne ba abinda mace za ta yi na aikin gida da ni ba zan iya ba, nima kawai neman fitina ce ta sa na ce ki min, dan bana so muyi zaman doya da man ja."
Ficewa yayi ya bar ta tsaye, É—an kumburo baki tayi irin baka da mafitar nan kuma abun bai mata daÉ—i ba ita ma, jin motsin shi a madafa ya sa ta juya ta koma É—aki duk jikin ta ba karsashi. Jabir kuma da kan shi ya yanka lemu da kankanar har ma da tufa sannan ya sa gaba yana sha yana jin nutsuwa na saukar masa na yunwar da ya kwasa dan bai yi sahur mai kyau ba, madara kawai ya sha da ruwa ya kora da salatin Annabi.