← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 168 OF 168

Sashe 168

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da jikin ta ita ma ta mishi alamar" Ba komai." Sai kuma ta taɓe baki ta sauke ajiyar zuciya, kama hannun nashi tayi ta ƙarasa maƙala mishi agogon, sannan ta fuskance shi sosai tana ƙara gyara masa hiramin kan shi tana faɗin" Abun mamaki baya ƙarewa duniya."

Da idanu ya tsare ta yana aika mata da tambaya, tana cikin gyara masa ta dubi idanun shi tace" To, da fari aurena da kai ne abinda ya fi bani mamaki, sai kwatsam kuma abokin ka ya aure min ƴata, hakan ya sa na rasa kallon da zan ma Kuwailat, shin zan ce mata *matar abokin mijina*? Ko kuma *ƙanwar mijina*? Na rasa."

Hannayen shi ya sa ya zagaya ta bayan ta ya riƙo ƙugun ta, hakan yasa duka hannayen shi ke kan tilin jigidar ta, cikin kafeta da idanu yace" Ke kuma da ba kya son hutar da kan ki, kin fi so kullum kina ba wa sheɗan dama yana zuwa miki da shubuha kala kala."

Murmushi tayi har haƙoran makkar ta suka fito fili tana ƙara saka yatsan ta tana kwantar masa da doguwar girar sa tana faɗin" Yau zaka fara bayar da karatu, ina so ka nutsu sosai *alarammana*, dan ka dace da faɗar ubangijinmu."

Jinjina kai yayi cike da jin daÉ—i ya amsa da" In sha Allah, nagode sosai."

Sumbatar kumatun ta yayi ita ma haka sannan ya nufi wajen SaddiÆ™ ya sumbace shi, kallon ta yayi bayan ya É—ago yace" Sai na dawo."

Har zai fita tayi saurin riƙo hannun shi ya dakata, juyowa yayi yana kallon ta, turo baki tayi cikin shagwaɓa tace" Dan Allah, dan Allah *my man* ka da ka haɗani da kowace mace a duniya, dan Allah?"

Gyara tsayuwar shi yayi yana ƙarewa idanun ta kallo da suka kawo ruwa taf, tallabo fuskar ta yayi cike da tausayawa da jin sabuwar ƙaunar ta dan ko sunan da ta kira shi da shi bata taɓa ba, tana dai cewa man, amma yau na farko da ta kira shi da *nata*, cikin nutsuwa yace " Haba mana *mai ɗakina*, ni fa dake kawai nake son ci gaba da rayuwata, har yanzu ban ji akwai wani gurbi dake buƙatar kawo wata sabuwar hallita dan cike shi ba, kin gama min komai a rayuwata Kulsum, kin zama uwar ƴaƴana biyu, Kuwailat da Assadiƙ da masi zuwa nan gaba, kin zama tasirina sannan cikar kamalata, ni kam me zai aike ni da haɗaki da wata?"

Sai kuma ya girgiza kai tare da sumbatar bakin ta yace" Kin manta da ke É—in Maamana ce? Ta ya zan iya haÉ—aki da wata kuyi tarayya? Ai ko a aljanna ke ce shugbar su, kamar yadda anan gidan duniya bayan mahaifina ke nake burin kyautatawa dan na samu shiga aljanna..."

Sai kuma ya rumgume ta tsam a jikin shi yana lumshe idanu yace" *Ina son ki Kuwailat*."

A zabure Ummu ta ɗago tana zaro idanu tace" Kuwailat kuma? Ƴar tawa?"

Waina idanu yayi sannan ya É—an harareta yace" Ke Maama wai me kika É—auke ni, wallahi zan aje hiramin nan muyi baram baram kafin na bar gidan nan, ina ce ke aka fara sakawa Kuwailat É—in ko?"

Wulwula idanu tayi ta sauke ajiyar zuciya tace" Oho! Yanzu na ji batu, to Allah baka haƙuri, kuma ai ba zan gaji da faɗa maka kana min rashin kunya ba."

Jinjina kai yayi ya juya zai fita yana faɗin" Sa'ad, Fahad, Aliyu, Mansur, ke har da wannan ma ƙaramin ɗan sheɗanin da bayan sheɗan ya saki nono ya kama (Jibril) duk sun rasa yadda zasuyi da ni, bare ke maama da awa biyu kawai ke ladabtar dake."

Dariya Ummu keyi ita dai ba ta ce komai ba saida ya kai ƙofar ɗaki tace" *Jabiru*."

Juyowa yayi da mamaki yace" E, lallai dai ta tabbata da sheÉ—anu a gidan nan, ko kuma dai na uncle Fahad ne suka dawo kan ki."

Kanne masa ido É—aya tayi tare da faÉ—in" *Ina alfahari da kai*."

Murmushin jin daÉ—i yayi tare da aiko mata da sumbata yace" Ni ma haka, ina son ki."

Da fara'a tace" *Ni ma h...*." Sai kuma ta juya da sauri ta nufi É—akin ta tana faÉ—in" Ni Allah ban yarda ba, haka kawai Jabir ka asirce ni a gidan na, gaba É—aya fa kai kake sarrafa tunanina."

Tana daf da shigewa Jabir yace" Aunty."

Dakatawa tayi ta juya tana kallon shi, shima kanne mata ido ɗaya yayi cikin raɗa yace" Ki saka wannan kayan baccin farare sannan ki kashe wuta, yau wasan ɓuya zamuyi, kuma idan ba tsoro ba karki cire jigidar nan."

ÆŠan hararen shi tayi tace" Oho! Dan ka gano ni ko?"

Murmushi ya mata alamar haka ɗin ne fa, dan haka ita ma cikin raɗa ko dan Kuwailat dake ɗakinta tace" Karka damu, yau sai dai bayan komai ya kamala ka roƙa mana gafara, amma dole zan ma gafarta rawar jigida."

Wani irin yanayi ya ma fuskar shi tare da ɗan cije gefen leɓen shi alamar" Ta saurara masa mana, fita fa zaiyi."

Ita ma da idanun ta da kuma bakin ta ta shiga yi masa alamar" To ka tafi mana." Sannan ta É—aga masa giraren ta biyu ta kanne masa idanu, sai kuma ta zura hannun ta ta baya tanayi kamar zata zare zif É—in rigar ta, hakan yasa Jabir zaro idanu yana matse baki da nuna mata" A'a fa."

Saida ta zare zif ɗin sannan ta ɗan juya bayan ta dafe ƙofar ɗakin ta da hannu ɗaya, ɗayan kuma ta dafe bango, hakan yasa ta juya masa baya gaba ɗaya ya zama yana ganin santalelen bayan ta da ko bras babu sai tarin jigidar ta da ya hanga, yana kallo ta ɗan fara yin sama da ƙasa da ƙugun ta tana kuma yin gefe da gefe da shi tare da juyowa tana kallon shi... A rikice Jabir ya yo kan ta da niyyar damƙota amma sai ta juyo gaba ɗayan ta cike da salon mugun ta ta dinga wani irin motsi jigidar na bayar da sautin dake ƙara ɗaga masa hankali, yana daf da kawowa kusan ta ya shuge ɗakin da gudu ta rufo ta sa makulli.

Jingina kanshi yayi a ƙofar a tausashe yace "Maama, dan Allah mana, ɗanki ne fa."

Ummu na ta ƙyalƙyala dariya yace "Um um! Ka je kayi karatun ka, ai zaka same ni gidan."

A tausashe sosai kamar wani mai shirin yin kuka yace "Um um maama, ban da nutsuwar karatu yanzun, zan kira Aliyu ya karɓa min, ko naje ba zan iya komai ba."

Cikin fashewa da dariya tace "Alaramma ba ruwana, wallahi ba na zama silar fasa karatu ba."

Murmushi yayi yace "To naji, zan tafi, amma dan Allah ki tarbe ni da kyau."

Cikin ɗaga murya tace "A dawo lafiya, Allah bada sa'a, *ina ƙaunar ka ƙanena*."

Dariya kawai yayi ya fice daga gidan yana mai cike da kewar Maaman shi da yi mata fatan alkairi, haka kuma yana gyara yanayin shi ko dan kar su haɗe da Aliyu ya sha jarabar tsiya, duk da dai yasan jiya shima aka ɗaura nashi auren wataƙila ya shiga tasu duniyar, amma Aliyun shi da ya sani da surutu wanda zai iya cewa shine Aliyu na farko da ya sani haka, sai ya masa tsiya inda ya gano shi.

*MA SHA ALLAH, ALLAH NA GODE MAKA DA KA NUNA MIN ƘARSHEN WANNAN LITTAFI NA RUBUTACCIYA, KOMAI YAYI FARKO DAMA YAKA DA ƘARSHE, ALLAH NAGODE MAKA DA KA ARA MIN RAI DA LAFIYA HAR MUKA KAMMALA SHI, INA NEMAN AFUWAR KA AKAN KURAKUREN DA NAYI DA KUMA SUƁUL DA BAKA KAN WASU ABUBUWA, ALLAH KA GAFARTA MANA BAKI ƊAYANMU, ALLAH YAA SA A MIZANINMU.*

_MASOYANA NA NESA DA NA KUSA, WANDA SUKA BANI HAƊIN KAI HAR MUKA KAMMALA WANNNAN RUBUTU, INA GODIYA A GARE KU, ALLAH YA BAR ƘAUNA DA ZAMAN TARE, HAƘIƘA KUN SAKA NI FARIN CIKI DA ZAFAFEN COMMENT ƊIN KU, NAGODE MUKU SOSAI DA ƘAUNAR DA KUKA NUNA MIN, WANDA MA SUKE GRP ƊIN AMMA BASU SAN TSIYAR DA MUKAYI BA, KU SANI INA GANIN KU KUMA KUN KYAUTA, SANNAN NAGODE DA CIKA MIN GIDA DA KUKAYI, MASOYANA NA ASALI KUMA INA SAKE GODE MUKU, INA ƘAUNARKU FISABILILLAH._ 😍

*HMMMMMM! WATAƘILA KU JI NI A KUSA KO A NESA, BA DAI ZANCE KOMAI BA GASKIYA, AMMA KU SANI IDAN KUKA NA TASO ZAKU JI NI DA WANI GIGITACCEN SALON DA ZAI HAUKATA TUNANIN KU, SAI DAI GASKIYA BA'A FREE BA🚶‍♀️😕, YASIN FREE NOVEL YAFI DAƊI SABODA WASU ABUBUWA, AMMA KUMA PAID MUTUM ZAI SHA MADARA YA CI KAZIII.*😎

_CYAMATU, YAGANA MUSSA, LUBABATUSHEHU,HAJIA ZUWAIRIYYA, UMMU HUSNA, HALIMA AHMAD, JAMILA YUSHA'U, MAMAN ABULKHAIR, ALEESA, MURJANATU UMAR, HALIMA SHEHU, MAMAN ABNA, MA NIÈCE UMMU (MOM ABBA BAZOUM), NUR, AISHATU ISMA'IL, AMINATU ABBA. Dama sauran da baa zan iya lissafaku ba duk ina gode muku abisa ƙwarin guiwarda sharhinku yake bani, da fatan idan na taso a sabuwar tafiya zaku yi haƙurin bibiyata sannu sannu._

*KWATE, KI TSARO MANA LABARI MU DIRAR MASA MU BIYU.*😉

*Alhamdulillah.*
Chapter 168 · 0% Book details