Sashe 22
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A zafafe Mardiyya ke kallon ta tana addu'ar ko kaɗan ne Fa'iza ta mata wani gangancin da zai saka ta ɗauke fuskar ta da mari, cikin ƙufula tace mata" Me kika gani? Kin ji kin tsargu ne?"
Waina idanu Fa'iza tayi sannan tace" Ba haka bane, na dai ji kalaman da kika faɗa min kamar na wacce ta ƙullace ni."
Wata hararar ke kik jiyo Mardiyya ta zabga mata tare da faɗin" Wannan kuma matsalar ki ce, ni dai nasan komai daren daɗewa gari zai waye, kuma in sha Allah za'a yi walƙiya halin kowa ya fito."
Cikin nutsuwa da dattako Hajia Radiya tace" Mardiyya, dan Allah, ki ji da halin da Æ´ar uwar ki take ciki mana, ina ke ina rigima a wannan yanayin?"
Wani malalacin murmushi Fa'iza tayi ta kalle su dukansu tace" Saida safen ku."
Ba ta sake jiran jin ta bakin kowa ba ta fice daga ɗakin, hakan yasa Mardiyya komawa ta zauna tana bin ƙofar da harara, da sauri Abida ta zauna kusa da Mardiyya ta dafa kafaɗarta kamar wata tsarar ta tana faɗin" Kiyi haƙuri aunty Mardiyya, sam Fa'iza bata kyautawa lokuta da dama, ni kaina wallahi ina zarg..."
Da gaggawa Hajia Radiya ta tare numfashin ta da cewa" Kul Abida, ki faÉ—i alkairi ko kiyi shiru, idan har kin san baki da hujja ko tabbas akan abinda za ki faÉ—a, to kar ki bari mala'iku su rubuta a littafin ki."
Da sauri Mardiyya ta kalli Hajiar tace" Hajia, ki barta ta faɗa mana, ni kaina wallahi ba zan taɓa yarda cewa wai babu hannun Fa'iza a ɓatan yaran ƴar uwata."
"Me ce ce hujjar ki?" Cewar Hajia Radiya tana tsare ta da idanu, ba tare da shakku ko ɗar ba Mardiyya tace "A bayyane yake mana Hajia, Fa'iza shekarar ta shida da aure a gidan nan amma ko ɓatan wata bata taɓa yi ba, a shekarar ta ta bakwai aka yi auren *Mukhtar* da Nuriyya, wata goa da auren su ta haifi ƴar ta ta fari, irin kyaututtuka da farin ciki da kuma soyayyar da duka ahalin ku suka nunawa yarinyar dalili ne da ya isa yasa Fa'iza ta sace yarinyar tun bata yi sati biyu da haihuwa ba. Duk da tashin hankalin da ake ciki da rikicewar da Nuriyya ta yi, a haka ubangiji ya sake azurtasu da cikin *Eesha*, amma ita ma fa aka sake biyo baya aka ɗauke duka wata shida da haihuwar ta, Hajia me yasa ba zamu zargi Fa'iza ba, tunda har yau da take da shekara ashirin da huɗu ba ta yi ko da ɓari ba."
Ba wai dan ita kanta bata wannan tunanin ba, so da dama idan ta ga Fa'iza ta kan ji ranta ya ɓace har taji kamar ma ta shaƙi wuyan ta tace _"Ki fito min da jikokina Fa'iza."_
Amma kuma ba ta da hujja, bata san da wane dalili za ta tuhuma surukar ta ta ba wanda yin haka ta san har shi kan shi ɗan nata Bilal ba lallai ya yarda ba, amma ita kanta tana zargin Fa'iza kuma wasu lokuta ayyukanta sukan sake jefa zargi a zuciyar mai saka mata ido, dan sau *biyu* tana kamata tana waya, amma da ta ganta sai ta aje wayar ta ce za ta sake kira, hakan na sake sakata jin anya kuwa! Anya Fa'iza ba akwai abinda take aikatawa marar kyau ba? Amma yanzu dan bata so gabaɗayansu su gina zarginsu akan rashin tabbas ta kuma zama babbar da ta goyi da bayan ganin laifi marar tushe, sai kawai ta wani basar tare da ƙara gyara gilashin wayar ta da wani murmushi a fuskar ta tace "Shikenan? Saboda wannan ne zamu zargeta da wannan babban laifin?"
Rusunawa Abida tayi cikin sanyin murya da ladabi tana kallon Hajia tace "Ammi, lamarin *aunty* Fa'iza akwai abun ɗaure kai da saka mutum shakku, ko ni dake abokiyar zamanta bana gane mata, ku duba fa ku gani rana ɗaya aka yi bikin mu da su Nuriyya, amma har yau ni da ita bayan gaisuwa ba abinda ke haɗamu, kullum fuskar ta a haɗe sannan tana ɗakin ta tana faman ƙuminiya da wayar ta."
Cike da son kwantar da tarzomar ta sake cewa" Na ji, yanzu dai bana so na sake jin wannan maganar, Mardiyya..." Ta faÉ—a tana kallon Mardiyyar tare da É—orawa da" Ki zauna da ita na wani lokaci, zan je na duba Kabil na ga ya yake? Na tabbata za ta farka anjima kaÉ—an, idan ya so sai ki tafi ko?"
Jinjina kai tayi tace" To shikenan Hajia, bari na kira Alhaji na faÉ—a masa ya bar ni nan."
Sanda Hajia Radiya ta miƙe ne ta kalle ta tace" Wai dama tare kuke da shi? Kuma kika barshi a waje?"
Murmushi tayi tare da sadda kanta tace" Tare muke Hajia yana nan falo, cewa yayi dare ya fara yi ba zai bar ni nayi tuƙi ba, amma zan faɗa masa sai ya koma kawai, ni idan na ida sai na tafi."
Murmushi Hajia tayi tace" To shikenan, tunda yana falo ma ai mun gaisa."
Inda Hajia ta tashi Abida ta zauna tana kallon Nuriyya dake kwance ba ta san me suke ba tace "Allah ya baki lafiya Æ´ar uwa, kina ganin jarabawa, in sha Allah komai zai tafi daidai."
Jinjina kai Mardiyya tayi tace "In sha Allah, mai son ganin bayan ta ma Allah ba zai bar shi ya gani ba, tunda har bayan an rabata da *Æ´an matan ta* sai Allah ya bata *namiji* (Kabil)."
Kallon Mardiyya Abida tayi jiki a sanyaye tace "Gaskiya ne, ban ma faɗa miki ba..." Ta faɗa cike da zumuɗi da fara'ar ta sannan ta ɗora da "Ina nan ina shiryawa Kabil murnar ƙarin shekara, amma fa sirri ne ka da kowa ya ji, dan ko ita ƴar uwa ban faɗa ma ba haka ma su Ammi."
Da mamaki mai ɗauke da murna Mardiyya tace "Dan Allah? Amma fa Abida za ki yi kashin kuɗi, duba da yadda ahalin Ahlan kuke shirya taro komai ƙanƙantar sa ba kwa masa da sauƙi."
Dariya suka fara sakawa, sai kuma Abida ta ɗaga kafaɗu alamar ko a jikin ta tare da cewa "To me ye a ciki aunty Mardiyya? Kuɗin ba komai bane idan aka haɗa da ƙaunar da nake wa Kabil, dan haka ni dai dan Allah ka da ki bari kowa ya ji sai ranar kawai."
Jinjina kai Mardiyya tayi tace "To shikenan, amma nima zan bayar da gudummuwata."
Da fara'a ta ɗaga kai alamar gamsuwa tace "Shikenan." Haka suka ci gaba da taɓa hira da jiran farkawar Nuriyya su ga yanayin jikin nata.
*Bayan* ta gaisa da Kakan na Jabir *Alka* ta wuce zuwa na ta ɓangaren, a tsakiyar tabkeken falon nata ta samu Alhaji Saheeb ɗin da Kabil suna buga tamola cikin farin ciki da ƙyaƙyata dariya, dakatawar su ya samo asali ne daga shigowar ta da sallama da kuma fara'a tana tunkarar su, farar rigar sa daya riƙe da hannu saboda tsayin ta zai hana shi gudanar da wasan tamolan da jikan nashi ya saki tare da sassauke numfarfashi yana kuma yi mata murmushi.
Ƙarasowa tayi ta rumguma Kabil ɗin a jikinta tana shafa kan shi da faɗin "Wato ana ta guje-guje ko? Har sai ka gajiyar min da bangona?"
Murmushi Kabil É—in yayi, duka yanzu ne zai yi shekaru huÉ—u, dan haka bai ce mata komai ba sai ci gaba da buga Ball É—in sa, maida dubanta tayi ga dattijon tace "Shine ka biye masa kuke buga min tamola a tsakiyar falo?"
Dariya dattijon yayi yace "Shigowa ta kenan daga masallaci na same shi yana bugawa, shine na ke taya shi."
Jinjina kai tayi a hankali tace "Da kyau to, sannun ku da ƙoƙari."
"Ameen." Ya faɗa, na wasu daƙiƙu kuma sai ya zura hannun shi ya riƙo nata hannun, hakan yasa suka kalli juna a tausashe yace "Ya jikin maman shi?"
Saida ta kalli Kabil dake bal ɗin shi cikin taushin murya tace "Jikinta da sauƙi, sai dai har yanzu bata farka ba, amma na bar su Mardiyya wajen ta su kula da ita."
A tsanake yace "Allah ya bata lafiya." A sanyaye ta amsa da "Ameen."
Shiru sukayi na wasu shuɗaɗɗun mintuna suna kallon Kabil na wasar shi shi kaɗai cike da bege da sa ran ina ma yana da wasu ƴan uwan da za su riƙa taya shi wasa? Wayar Alhajin ce ta shiga siriyar kururwar da take nuna tana buƙatar agajin shi, cikin dattako ya lalubo wayar daga aljihu, duk da bai san lambar ba, amma kasancewar shi mutum mai jama'a kala-kala sai ya ɗaga saboda jin cewa koma wanene to na kusa da shi ne ko wanda ke kusa da wanda ke kusa da shi, dan ƙaramar wayar sa ce aka kira kuma babu mai wannan lambar tashi sai ahalin shi kawai.
Yana ɗaga daga can ɓangaren aka fara da "Assalama alaikum?"
Cike da dattako muryar shi na fita É—ai-É—ai yace "Wa'alaika salam warahmatullah wa barkatuhu."
Cikin muryar ladabi aka ce "Alhaji barka da dare? Kana magana ne da sifetan jami'an tsaron Zinder4, na kira ne dama dan na sanar da kai mun kama *É—an ka*."
Cike da dagiya da ƙarfin hali dattijon ya lumshe idanun shi, ba tare da ya buɗe ba a ƙasan zuciyar sa yake faɗin "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!"
A zahiri kuma cikin murÉ—aÉ—iyiyyar murya yace " Subhanallah! Wane yaron nawa?"
Daga can ɓangaren aka bashi amsa da "Alhaji *Fahad* ne."
Idanunshi ya buÉ—e tare da zuba su ya kalli Hajia Radiya dake gefen shi ta zuba masa idanu tunda ta i ya ambaci tsarki ya tabbata ga Allah, É—an É—auke wayar yayi daga kunnen shi tare mhsa kai tafin hannun shi ya rufe daidai inda sauti ke shiga da fita cike da son samun tabbaci yace "Radiya, ina Fahad?"
Da rashin tabbaci da kuma mamaki take bashi amsa da "Rabona da shi tun safe, ya ce min zai je gidan abokin shi *Ja'afar*, wani abu ne ya faru?"
Girgiza mta kai yayi alamar a'a tare da maida wayar a kunne cikin nutsuwa yace "Ina jin ka sifeta, a ina ne kuka kamany shi?"