Sashe 34
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zubawa idanun ta nashi idanun yayi, dolen shi ne fa ya kula da ita har ya ga ta koma garas yadda take, shine silar wannan halin da take ciki, shine musababbi, ba dan shi ba wataƙila tana ƙasar su tana karatun ta, dan haka yake ɗaukar komai nata da matuƙar mahimmanci, yake kuma *jin ta sosai a zuciyar shi*, shirin shi a kan ta shine ta samu lafiya sosai ya tabbatar ba wata matsala, sai ya ɗauketa da kan shi ya kai ta garin su wajen iyayen da aka ce mishi sune nata.
Kafin ya ce wani abu Hajia Kaka ta fito da irin kwandon nan na zuba kayan datti a ciki tana ƙwala kiran "Kai Inusa, kana ina?"
Da ƙarfi almajirin ya amsa da "Na'am Hajia."
Tana tahowa tace mi shi "Zo ga kayan."
Wanda aka kira da Inusa ne ya shigo da sallama, lokacin da Sa'ad ya miƙe tsaye yana kallon Hajiar yace "Hajia, wanki za'a miki ne da safiyar nan?"
Tana kallon shi ita ma tace "Wanki za'a min Sa'ad, tun jiya na sa aka kira shi na gaya mishi, shiyasa na ce ya zo da sassafe dan kayan da É—an yawa tunda har da na Aisha."
Da wani irin mamaki a fuskar shi yake kallon Hajiar ya maimaita kalmar "Aisha?"
Kallon shi tayi sa'ilin da take miƙawa Inusa kayan ya amsa ya nufi hanyar fita tace "E, tunda Kaga ba lafiya gare ta ba da zata yi wankin, ni kuma dama ba iyawa nake yi ba yi min ake."
Juyawa ya fara yi ya kalli Inusan dake daf da fita, à tsanake ya juyo ya sake duban Hajia Kaka cikin wata irin murya kamar wanda zai faɗi abun arziƙi yace "Hajia, kuma saboda Allah waccen ganɗamemen ne zai wanke kayan wannan yarinyar?"
Haɓa Hajia ta riƙe tana faɗin "Laha'ilaha illallahu ! Sa'ad, yo Inusa bargo ma ɗan Libiya ba yana wankewa ba bare kayan ita ƴar taka? Me ye a kayan nata da ba zai iya wankewa ba?"
Ƙura mata idanu yayi sai kuwa ya fara wani marmarmar ɗin da ido dake nuna mata ran shi ya fara ɓaci cikin saurin magana yace" Ba wannan nake magana ba Hajia, ta ya waccen balagaggen zai wanke kayan budurwa, zai ga surarta, zai ga komai nata har ma ya ji ƙamshin tufafin ta, to ni gaskiya bana so, wanki ne tunda ke ba zaki iya ba ni zan muku wankin..."
Ya faÉ—a yana juyawa tare da faÉ—in" Kai, bani kayan nan?"
Da mamaki Hajia ta kalli Aisha da ita ko a jikin ta tana dai kallon su ne, sai kuma ta bi bayan shi da sauri tana faÉ—in" Sa'ad, da gaske kake? Har da kayan nawa? Ko iya nata kawai?"
Duk da ya fita saida ya dakata ya juyo ya kalle ta, to me take nufi da na Aisha kaÉ—ai? Ko har da nata? Idan ya ce ban da nata yayi abun kunya gaskiya, to wai ma ku dakata? Me ya faÉ—awa Hajia a É—aki ne...? Sala-sala ya shiga tariyo abinda ya faÉ—a, sai kuwa ya tuna tsaf, amma sai yake mamaki da tambayar kanshi anya shi yayi maganar nan? Kai aiki ne dai irin na iblis la'ananne kawai, dn haka ya basar dan yasan Hajia ma ai ta gane komai, fuskar ta ya kalla yace "Harda nakin."
Murmurshin farin ciki Hajia ta saki ta kalli Inusa da ya aje kayan gabanshi tace "Tafiyar ka kaji Inusa, dama rashin mai min wankin yasa nake kiran ka, yau kuma kaga zan ci albarkacin Æ´ar rainona Sa'ad ya min wanki."
Bakin Hajiar ya bi da kallo da tayi maganar, sai ya ji ya tsargu da abinda ta faɗa har ma kamar ya ce ya fasa, amma kuma ai hakan ba girman shi bane, musamman ma da yake a gaban yaron nan da yarinyar can... To a ida gizo yake saƙar shine, shin zai iya wankin kaya masu yawa haka? Gaskiya ya jima rabon da yayi wanki, hatta fa ɗan kamfanshi cikin kayan wanki yake tattarawa ya haɗa, dan haka shi bayan bakin shi da jikin shi ba abinda yake wankewa. *An ɗebo ruwa kenan*?
Ai ko dai maza an ɗebo ruwa, anyi wanki amma a wahalce, ba dan rashin iyawa ba sai dan jimawa ba'a haɗu ba, sai dai daga wannan wankin ya koyi wasu darusa a rayuwar shi, na farko shine _yana da kyau bawa ya dinga hangen gaba da kuma baya yana yin abun da ko da kuwa ya fi ƙarfin yin shi_, na biyu kuma shine _zai dinga ƙoƙartawa ko da a wata uku ne yana ma Hajia Kaka wanki_, dan farin cikin da ya gani a fuskar ta ba kaɗan bane dan kawai yana mata wankin nan, na uku kuma shine _wahala bata da daɗi ko ya take kuwa_, sai darasi na ƙarshe da ya kasa tantance me zai auna a kan shi shine _me yasa ya ma yarinyar nan wanki_? Rashin sanin wannan amsar yasa har ya gama wankin ya shirya jiki a sanyaye ya fita yana son gano wannan amsar, me yasa ya yi? Me yasa ya damu har ya dinga faɗa dan wani zai mata? Me ye na ɓacin ran wai? Amsar da ya samu har ta saka shi sauke ajiyar zuciyar dake nuna ya samu nutsuwa ya kuma gamsu da amsar ita ce *saboda kai ne silar zuwan ta nan*.
Kula mai suna kulawa Sa'ad yake ba wa Aisha a wajen jinya, duk da ƙaracin shekarun ta da rashin saka abu a kai saida ta fara jin wani sabon yanayin da yake sakata tunani barkatai, musamman ma canjin da ta fara gani a tare da ita, wato yanzu idan suna tare sai ta fiya jin kunya da nauyin zance saɓanin can da take kiran shi Abbu kan ta tsaye take aikata abu, amma yanzu ko ido bata son ɗagawa ta kalle shi saida dalili, magana kuma ta ke mata wuya sai dai ta furta um! Ko um um ko a'a ko ma ta girgiza kai a wasu lokuta. D sannu sai shaƙuwa ta shiga tsakanin su wanda shi kan shi gogan bai ankare da haka ba sai daga baya, yadda da yake kwanaki bai leƙo gidan ba, yanzu ko wani abu ya ɗaui hankalin shi haa zai dawo gidan ya kwana saboda wani abu da yake ji mai kama da kana da wani muhimmin abu a wurin kuma dole ka na son kasancewa tare da shi, sannu sannu shi ma sai ya zama mai tausasawa à gare ta ba tare da Sanin shi ba, sai ya zama mai kunyar aikata wasu abubuwa a gaban ta, sannan mai jin fargaban aikata wani lamari idan tana usan shi.
Babban wani abun duba shine, yadda ya j sam baya so ma yana tuna cewa shi ɗin ya san *ahalinta*, gani yake idan ya sadata da su zata mishi nisa kenan, duba da yasan wannan ahalin wanda ko ƙafar su mahaifin shi bai kama wajen dukiya, dan haka har yanzu ya ƙi saka ranar da zai kai ta ga Ahalin ta, bai ma faɗa ma kowa ya sani ba, sai dai kuma ya manta da wani abu, wannan abun kuma shine Hambali da DG da *suke neman ta*, gashi kuma yanzu sukan yawan fita ita da Leila wata rana ma da sauran yaran, Hajia kuma dama ita ce abokiyar yawonta.
*Alhamdulillah.*
29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
*RUBUTACCIYA*
👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
_NA_
*SAMIRA HAROUNA*
_SADAUKARWA GA_
*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_
_Bismillahir- rahamanir-rahim._
*16*
Duk da babban falon su guda ne, amma dake kowace tana da nata falon kuma b yara gare u ba yasa ba mai zama yayi wani abu a falon, dan haka kai tsaye ta shigo da shi ta wannan ƙofar da tunanin ba wanda zasu haɗe da shi. Sai dai Kashhh! Sai da suka gama shigowa cikin nishaɗi Abida na faɗin "Amma dai wayar ka ta mutu ko?"
Girgiza kai wani matashin yaro yayi da bai wuce shekara ashirin da biyu zuwa da uku ba yace "A'a aunty, me kika gani?"
Taɓe baki tayi tace "To ai naga ina ta kiran ka ne bata shiga, da fa ban sa a tarbeka ba?"
Murmushi yayi yace "Ba zan gagara gane kwatancen da su Hajia suka min ba ai."
Murmushi ita ma tayi tana nufa hanyar ɗakin ta tace "Da wannan kuma, tunda gidan ba ɓoy..." Cak ta tsaya tare da yin shiru sakamakon ido huɗun da sukayi da Fa'iza zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya tana ta aikin latsar waya, da fari Abida tsoro ta ji dan bta saba ganin wani zaune a falon ba, ko baƙi sukayi kana kai shi falon ka ne amma ba wannan falon ba, kai idan fa sun zauna nan to tare da mijin su ne idan ya buƙaci su yi karin kumallo tare, bayan haka kowace na sashen ta dan babu wacce ke sauke girman kai ta je ma ƴar uwar ta. Da ta gaa fahimtar wacece wurin sai ta sauke ajiyar zuciya ta ɗanyi murmushi yaƙe tace "Sannu aunty, anan kuma ake zaune yau?"
Cike da jin haushin Abida da tsanar ya Fa'iza ta wanka mata wani kallo wanda ƙarara na harara ce da kuma zallar tsana a ciki a daƙile ta bata amsa da "Ummmm!"
Ganin wannan kallo da Abida tayi yasa ta haÉ—e ta ta fuskar ita ma ta mata wani kallo na É—aga gira tamkaro muguwa tana kallon fuskar ta tace "Uhmmm! Allah yasa dai *barewa* ba tana shirin shiga sabgar da babu ruwan ta bane, dan *damisa* bata da sani bare sabo..."
Sai kuma ta shiga mata kallon sama da ƙasa a wulaƙance tace "Bakin rijiya ba gurin wasan makaho bane, tsalle ɗaya zaki yi ki faɗa rijiya, dubu sau dubu kuma ba zai fito dake ba, dan *ni ce zan gina rijiyar*, ni kuma komai nawa da lissafi nake yin shi, saɓanin..."
Wani masifaffen murmushi ta sakar mata kamar wacce ta mata albishir da aljanna sannan ta ɗora da" Saɓanin ke auntyna da kike gayyato idanun kowa a kan ki."