Sashe 20
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba ita da aka ba amanar Aisha ba, har su Zarah saida mamaki ya nemi halaka su, sai Sabira data rufe bakinta da tafin hannu tana son yin dariya har ma tayi rawa ta girgiza ta faÉ—i da babbar murya cewa _" Yau dai Allah ya yi, bayan ma shigowa da ake da su yau har da ba wa gyatuma ajiyar É—aya daga ciki."_
_Hajia Uwani, kai tsaye ba zamu ce ga yadda halina yake ba, amma dai muga aikin ta kai tsaye sai mu san wace irin mata ce_, Cikin yanayin faɗa ta shiga kallon shi da ma Aishar da ke ta sinne kai tace" Na tambaye ka wacece, ba ka amsa min ba, shine kake ce min na ajiye maka ita wai baƙuwar ka ce, wacece ita ɗin?"
Cike da nuna gajiyawa yace" Mama, cewa fa kawai nayi baƙuwata ce ta zauna wurin ki, kuma na ce zamu yi magana daga baya, a dole sai kowa ya ji har ma a saka mana ido?"
Cikin hargagi da faɗa tace" To ba zan riƙeta ɗin ba, ka ga ka gaggauta fita da ita a gidan nan, ba dan kana son ka nuna mana lalacewar ka ba? Macen za ka kawo mana gida ka ce baƙuwar ka ce, kai ba matar ka ba, ba ƴar uwar k ba? Ba komai na ka ba haka kawai."
Sai kuma ta maida kllonta ga Aisha ta shiga nuna da hannu tana cewa" Ke, dube ki fa dan Allah? Ƙaramar yarinya da ke, amma ki sa kanki rayuwar bin maza..."
Da ƙufula da son katse numfashi ta Sa'ad yayi gaggawar faɗin" Mama..., ba fa haka take ba."
"To ya take? Da ta biyo ka nan karatu za ka koya mata?" Sai kuma ta sake kallon Aisha tace "Ke, fita a Gidan nan kafin na saɓa miki kamanni."
Aisha data fara hawaye tunda ta ce tana bin maza d sauri ta juya za ta bar falon, tana jin muryar ta tana ci gaba da faɗin "Aikin banza, banda lalacewar zamani, yarinya ƙarama da ke har ki biyo namiji cikin gidan su, wannan ai rashin kunya ce da fitsarewa, idan ma iskancin ne kuyi à can waje mana wa ya hana ku? Amma a cikin gida ziƙam-ziƙam ki biyo shi, mtssssss!"
Juyawa Sa'ad yayi ya ga ta fice a falon, sai kuma ya kalli su Zarah dake ta haɗe kawunansu suna son tattaunawa, haka ƙannenshi dake ta kallon rikicin mahaifiyar tashi, hakan ya s ake hasala shi ya kalle ta a zafafe yace" Har abada ni ba zan iya yin abun arziƙi ba a gidan nan, ina ganin ke kaɗai ce wacce ke gareni da zan tunkara da wannan lamarin, amma kema kin watsa min ƙasa a ido, yarinya ce fa da bata fitsarar ƴar ki ba, bata san a ina take ba, ɓata gari ne suka kawota nan da alama siyar da ita zasu yi ko dai wani mugun nufin ne da su a kan ta, shine kawai fa na taho da ita nan, amma dake ni bunsuru ne kowa ma kulawa nake, shine da kanki za ki zargeni da fasiƙanci..."
A hassale ya juyawa shi ma ya fita a falon, sai dai yana fitowa ya ci karo da Kakar shi tare da Aisha tsaye tana goge hawaye, a saiɓance ya ƙaraso ya samu Hajia na tambayar ta wacece ita sannan me aka mata? Yana zuwa da ladabi yace mata" Ina wuni Hajia?"
Kallon shi tayi da kulawa da kuma fara'a ta amsa da" Lafiya lau Sa'ad."
Kafin ta sake cewa komai yace da ita" Hajia, nasan ke kaɗai ke ƙaunata a gidan nan, dan Allah ki min taimako ɗaya?"
Da murmushi da kuma dattako tace" Sa'ad, bana son kana cewa haka, kowa a gidan nan yana ƙaunar ka, rashin fahimta ne kawai kai da su, yanzu faɗa min? Wane irin taimako zan maka?"
Aisha ya fara kalla sannan yace" Wannan yarinyar yanzu muka haÉ—u da ita a hanya, bata san kowa da ko ina ba anan, ta ce wasu ne suka kawota garin nan kuma bata da kowa, shine na kawota nan ta zauna na kwana biyu sai a mayar da ita gidan su, haka yayi Hajia?"
FaÉ—aÉ—a murmushi tayi ta kalli Aisha tare da dafa kafaÉ—arta ta rumgumata a jikinta tace" Ba komai Sa'ad, sai ta zauna a wurina ai, zan kula da ita fiye da zaton ka, Kaga nima na samu Æ´ar raino."
Murmushi yayi yana jin hankalin shi na kwantawa, har zai tafi sai kuma ya dakata saboda jin Kakar ta ce" Ya sunan ki Æ´an mata?"
Cikin shasheƙar kuka Aisha ta furta" Nana A'isha."
Murmushi Kaka tayi tace" Suna mai daÉ—i, sunan uwar muminai kenan, Allah ya azurtaki da halayen mai sunan."
Sa'ad kam taɓe baki yayi ya kalli Hajia yace" Hajia, zan shiga ciki na shirya, zan dawo in sha Allah."
Jinjina kai tayi alamar to sannan ta ja hannun Aisha tana faÉ—in" Bari in shiga da ita ciki."
Kowanensu ɓangaren shi ya nufa musamman Sa'ad da yana shiga ya faɗa banɗaki dan yin wanka, sai da ya kimtsa kan shi ya fito falo ya zauna ya sake ɗaukar wayar shi dan duba ko an turo masa saƙon hoton yarinyar da ya buƙata. Ganin saƙon dake tabbatar masa hoto ne ya danna alamar buɗewa cike da zumuɗin son ganin wannan yarinya mai wayon da ta kubce daga hannun DG.
Kan baƙin kallabin dake ɗaure a kan ta a fara sauke idanu, sai lumsassu kuma shanyayyun idanun mayen ta da ta musu wani iri kamar za ta yi bacci daga tsaye da take, a zabure ya miƙe yana ci gaba da rarako ido yana kallon hoton da son gasgata wai ita ce? Ko dai kama ce? Ko ya mata kallon tsoro ne da har yake ganin kamar ita ce aka turo masa hoton ta a wayar shi? Baƙa ce, sai dai kyakkyawa da ta dace da ita kanta ɗin, a ruɗe ya danna alamar kiran lambar da ta turo masa hoton yana tattaki a cikin falon da ƙaguwar a ɗaga kiran a kuma tabbatar masa ita ce a ka turo masa hoton ta, ko kuma dai waccen yarinyar dake wajen kakar shi ture ne aka masa?
********************
Saida ta ƙara yin ƙasa da muryar ta sosai cikin harshen buzanci kamar marar gaskiya tace "Kana nufin har yanzu ba'a ganshi ba? To ina ya tafi? Dama ya san mutane ne a garin?"
Shiru tayi na wasu daƙiƙu kafin ta sauke ajiyar zuciya tace "Ko me ye ya faru sakacin Mu'az ne, kar ya ga nayi banza da lamarin Jabir, idan fa ba'a ga jikina ba na rantse muku da Allah sai nayi shari'a da shi, ni dama takaicina yadda yana jariri muka nemi ya bar mana shi dan zamu i kulawa da shi, amma tsaf Mu'az ya kalle mu ya ce tunda mahaifiyar shi na raye ita za ta kula da yaron, amma wallahi idan ya salwantar min da yaro sai na ɗaure shi."
Shiru ta sake yi na wasu daƙiƙu, cikin ɓacin rai har ta mance da bata so abokan zamanta su san abinda ke faruwa ta ɗaga murya tace" Ni dai na gaya maka, kuma tunda kai kana waya da shi kace wall..."
Ƙwanƙwasa ɗakin da aka yi ana faɗin" *Hajir*, Hajir kina ciki ?"
Gane muryar yasa ta yi saurin aje wayar akan gado tare da fitowa tana murmushi, kallon juna sukayi ita da matar da kana ganin ta ka ga wayayya sannan mai ji da kan ta, kamar ba kishiyoyi ba saboda yadda suke girmama juna musamman ma dai yadda Hajir ɗin ke rusuna ma *Mardiyya* kamar ba ita ce gaba da ita a shekaru da ma zuwa gidan nan ba. Mardiyya da hankalin ta ke tashe sakamakon kiran da aka mata ƙanwar ta jikin ta ya sake tashi, sai dai duk da fuskar ta ta nuna damuwa da rashin nutsuwa, amma Wani basaraken leshe ne jikin ta mai manyan duwatsun da ke nuna tsabagen tsadar shi sannan ga idon mai kallo sassauƙa ne, ga mahaukacin mayafin da ya dace da shi da kuma jaka data saɓa à kafaɗar ta. Ba kwalliya a fuskar ta ko alama, amma Wani irin sheƙi da walwali da fatar ta ke yi a zahiri za ka gane fatar a nutse take sannan tana samun kulawa, dan kuwa mai ma da Mardiyya ke shafawa sai wanda suke a babban shagon da ya fi kowane a kuma matakin da ya fi kowane, ma'ana a VIP, mayuka ne da ko basu gyara maka jiki don Allahn da ya yi maƙerinsu ba za su gyara maka dan tsadar su ma mai iya saka talaka jin faɗuwar gaba.
Da yanayin tashin hankali Mardiyya tace "Yaya, zan tafi gidan *Nuriyya* ne, an kira ni wai jikin ta ne ya sake tashi."
Da yanayin tashin hankali Hajir ta fito daga É—akin gaba É—aya tana faÉ—in "Subhanallah! Jikin Nuriyya ne? Me kuma ya same ta?"
Cike da damuwa tace "Wallahi nima ban sani ba, sun dai wai ko tana madafa ne ta yanki jiki ta faÉ—i, ni nasan ba zai wuce ta ga wani abu da ya tuna mata da *yaran ta* bane, amma dai zan je na gani."
Cike da tausayawa halin da ƙanwar abokiyar zaman nata take ciki tace "To ba damuwa, Allah ya bata lafiya, Allah ya kuma bayyana mata su, sai kin dawo ɗin, ko a can za ki kwana?"
Da sauri tana ƙara gyara zaman gyalenta tace "A'a, zan dawo ba jimawa, tar..." Odar da aka yi daga ƙofar gida yasa ta canza akalar maganar zuwa "To kin ji ma , har ya fara min oda, bari naje sai mun dawo."
Da mamaki Hajir tace "Au ! Wai tare da Alhaji za ku je ne?"