Sashe 64
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rashin son magana da hayaniya yasa Jabir kallon Aliyu, amma ƙala bai ce mishi ba kamar b da shi yake ba, a zaman da sukayi yanzu babu wanda ya san Jabir sama da Aliyu, dan sun zama aminan juna da basa ɓoyewa juna komai, dan haka Aliyu bai ji komai ba sai ma kawar da kai da yayi yace "Ba zai yiwu ba wallahi, kuma zan sanar da Abba yasan abinda kake shiryawa."
Jabir ma ba tare da yana kallon Aliyu ba yace "Um um, kar ka faɗa." Daga haka bai sake cewa komai ba har suka isa masaukin su, wanka suka fara yi suka shirya, Jabir na cikin kayan da ya fi so wato baƙar doguwar riga da tattausan wandon yadi fari daya saka daga ciki, suna zaune kan kujera suna fuskantar juna Aliyu ya kira wayar Abban. *A lokacin* shi da Kuwailat ne Ummu na ɗaki cikin rashin jin daɗin yanayin da take ciki har bacci ya fara ɗaukar ta mai cike da mafarkai barkatai.
Bayn sun gaisa Aliyu kam yake faÉ—a mishi abinda Jabir É—in yake shirin yi, a take Alhaji yace "Bani Jabir É—in ?"
Jabir da ke kallon Aliyu tunda ya fara magana bai ce komai ba, yana miƙo mishi wayar ya karɓa da girmamawa suka gaisawa, cikin tuhuma Alhaji yace "Jabir, gidan haya ka sa a kama maka bayan kana d gida? Wani abu aka maka da baka san zama da mu?"
Saida ya lumshe idanu ya jingina sosai a kujerar sannan ya furta "A'a Abba, ba komai."
A take Alhaji yace "To in dai hakane kada na sake jin maganar kama gida a bakin ka, ku dawo tare da Aliyu ku zo gidan mahaifin ku, ina da wurin da zan sauke ku."
"Shikenan Abba." Ya faÉ—a a tausashe kafin ya gyara zama yace "Abba, kana kula da shan maganin ka?"
Murmushi Alhaji yayi na jin daÉ—in yadda Jabir ke kulawa da shi yace "Sosai Jabir, ina kulawa, Allah ya maka albarka."
Duk da idanun shi a rufe suke kamar bai bacci bai hana shi faÉ—in "A gaida *Maama*...da kuma Kuwailat."
Da kulawa Alhaji yace "Za su ji." Dan kuwa Ummu ita ce Maama, da yana kiran ta da aunty, amma bayan wasu shekaru sai yake kiran ta da Maama, a cewar shi ai ita ta zama uwa gare shi, dan haka ta cancanci haka. Suna gama wayar Jabir ya cillawa Aliyu wayar da jin haushin sanar da Alhaji da yayi abinda yake shirin yi tare da sake rufe idanun shi, tsawon lokaci Aliyu ya san Jabir na yawan rufe idanu yana kallon sama, baya takura masa a irin wannan lokacin, saboda ya faÉ—a masa yana tunanin mahaifin shi ne da yana so ya neme shi, amma kuma ya fi so sai ya zama mutum kafin mahaifin shi yasan da yana raye.
Jabir kuma tunanin shi bai wuce lambar wani abokin mahaifin shi da ya samu a fecebook wato Hisham, ya mishi magana tare da sanar da shi shine Jabir ɗan Mu'az, yanzu haka ya bashi lambar mahaifin nashi, to tunanin shi shine ya mishi magana yanzu? Ko ya bari sai sun koma gida? Daga haka har ya shiga tunanin yarintar shi, abubuwan da suka faru, matar Baban shi, ƙanwar shi, Kakanin shi, komai da komai sai yake zuwa mishi a ƙwaƙwalwa tamkar yana kallo a allon bango.
*Washe Gari*
Da yanayin gaggawa ya shigo falon, wanda hakan da yayi yasa Aisha da Mamie har da Abbu kallon shi da mamaki dan ko sallama bai yi ba, kai tsaye wurin Aisha dake shirya Yusrah ya nufa dan ya ce mata sammako zasu yi, ta ɗauka ko à kan fitar ne, amma sai ta ji yace "Bani lambar aunty Fa'iza."
Da matsanancin mamaki ta dube shi tace "Aunty Fa'iz..." Tun bata kai ƙarshe ba tace "E ita, maza bani dan Allah?"
Miƙewa tayi tana faɗin "Wayar na ɗaki, kuma ban da lambar a kaina, bari in ɗauko."
Bai amsa mata ba sai bin ta da kallo, hakan yasa Abbu matsowa kusan shi da doguwar riga dan ko shirin fita bai yi ba yace "Me ya faru ne Sa'ad?"
Kallon shi yayi da girmamawa yace "Za ka sani Abba, zan kira ta ne."
Suna nan tsaye har ta fito tana gaya mishi lambar yana É—auka, yana gama É—auka ya tura kira, ba jimawa kuma Fa'iza ta É—auka, suna gaisawa da hanzari yace "Aunty Fa'iza Sa'ad ne, dan Allah ko zaki iya zuwa gida yanzu?"
Da mamaki tace "Gida kuma? Nan wajen su Hajia?"
"E." Ya bata amsa kai tsaye, da mamaki ta sake cewa "Lafiya? Wani abu ne ya faru?"
A hankali yace "Ba komai aunty, dan Allah ki zo idan kina iyawa."
Gabanta sai ya faɗi, zuciyar ta ta raya mata ko dai Alhaji ne ya rasu? Dan haka ta bashi amsa da gata nan zuwa, gaba ɗaya hankalin ta ya fi bata kan Alhaji ne ya rasu, dan haka da damuwa da zulumi ta tuƙo motar ta zuwa gidan nan.
A falon Alhaji ta same su, kowa na zaune saboda Sa'ad ya buƙaci da su zauna sai shi Sa'ad ɗin dake tsaye yana kai da kawowa, da Hajia kawai ta iya gaisawa dan har Alhaji kallon ashe ba shi bane ya mutu take masa, kafin ta numfasa Sa'ad ya tsare ta da idanu yace "Aunty Fa'iza, kin san Rabi'u?"
Har ga Allah ta manta da shi, sai kawai ta kalle shi da mamaki tace "Wanene hakanan kuma? Rabi'u?"
Da alamar ƙaguwa Sa'ad yace "Aunty Fa'iza, ba wasa na tara mu muyi ba, Rabi'u wanda kika sa *sukayi garkuwa da Fahad* nake magana a kai."
La'ilaha illalah! Gaba ɗaya yasa kayan cikin ta sun murɗa, hankalin ta ya tashi ƙwarai da gaske, dan wallahi ita ta manta ma da wannan abu da ta aikata, gaba ɗaya yanayin rashin gaskiya ya bayyana a tare da ita, gashi kuma kowa ya kalle ta ana mamaki, Abbu kuma dama bai yi mamaki ba yasan za ta aikata ai, dan haka Sa'ad ya sak faɗin "Aunty Fa'iza, da bakin shi ya gaya min, idan kina so zan iya kiran shi ya zo, bayan shi ma har da Rabi zan iya kira dan ta faɗa gaban ki cewa ke kika sa ta kai Eesha gidan marayu na HY."
Cikin tashin hankali Fa'iza ta furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un !"
Harara Abbu ya zabga mata yace "E mana, kya faÉ—a, tunda asirin ki ya tonu ba."
Kallon shi tayi idanun ta taf da hawaye tace "Na yarda ka kira Rabi, dan za ta faÉ—a muku bani na sa ta É—auke Eesha ba, ni kawai na faÉ—a mata inda za ta kaita ne."
Cikin jin haushi Abbu yace "Ka ji wani rainin hankali kuma."
Kallon shi Sa'ad yayi yace "Ba rainin hankali bane, gaskiya ta faÉ—a."
Cikin duhun kai da ya saka kowa Mamie tace "Kamar ya? Wai me kake so ka faÉ—a ne?"
A nutse ya kalle ta yace "Mama, aunty Fa'iza ba ita tasa a ɗauke Eesha ba, sannan ita tasa aka yi garkuwa da Fahad, amma kuɗin ta bayar da su ne dan kawai *nemo Eesha*, dan a lokacin ta ɓace daga gidan marayun ana nemanta ido rufe."
Alhaji dake zaune ne ya dube shi yace "To kenan wa ya sa a sace Eesha?"
A hankali Sa'ad ya juya kaÉ—an ya kalli Abida da tuni idanun ta suka fito ta fara ruÉ—ewa, haka ma Fa'iza kallon ta tayi tace "Abida ce."
Salallami É—akin ya É—auka, hakan yasa Abida fashewa da kuka ta É—ora hannu a kai tana faÉ—in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un ! Sharrin da zaku min kenan? Sace mutum kuma?"
Wata muguwar tsawa Yaya Bilal ya daka musu dukan su, da jin haushi da takaici daga Fa'iza har Abida yace "Ku min shiru, ku fice ku bar min gida, sheÉ—anun mata kawai da baku san ciwon kawunan ku ba, dukan ku Æ´an ta'adda ne wallahi."
A fusace ya raɓa zai wuce Sa'ad yace "Kawu ka dakata dan Allah."
A ƙufule yace "Me zaka faɗa min? Waɗannan matan basu da imani, me na musu? Daga aure shikenan sai su zame min annoba cikin alhali, babu wacce bata cutar da mu ba a cikin su?"
Cikin kwantar da murya Sa'ad yace "Hakane kawu, amma aunty Fa'iza ba ta yi komai ba, lokacin da ake shirin sace Eesha daga gidan nan, Rabi da zata yi aikin ta same ta ta faɗa mata, wanda Abida ta zaɓeta ne sabo a ta ga suna da kusanci da Fa'iza, da ta sanar da ita sai ta ce ba damuwa ta yi abinda ta saka ta, ban san me ye nufin ta na yarda da hakan ba, amma dai ta umarci Rabi da ta kai ta gidan marayu na HY inda anan Abban Abida yake kula da marayu, sai kuma kuɗi da ta buƙata bata da su wanda ya sa dole ta sa aka kama Fahad dan ta biya DG ya nemo mata Eesha tare da kawo mata ita gidan nan cikin tsaro, na san hakane daga bakunan duka mutanen nan."
Kallon Fa'iza yayi dake kuka har ta zau'a kan kujera yace" Me yasa kikayi haka aunty Fa'iza?"
Cikin matsanancin kuka tace" Ban aikata haka dan ina so Eesha tayi nesa da iyayen ta ba, na yi tunanin Abida za ta sa wasu su mata aikin saboda ta riga da tayi niyyar aikatawa, idan kuma aka ɗauke ta bmu san me za ta ma yarinyar ba, zaku fahimci niyya ta ba mummuna bace daga yadda na sa Rabi ta bayar da yarinyar da cikakken sunan ta, bayan samun labarin ɓatan ta kuma hankalina ya tashi, gashi DG ya gaya min mahaifin Abida na neman ta zasu cutar da ita, na sa ya min alƙawarin nemota ya kawo min lafiya, amma dole zan bashi kuɗin da suka ninka wanda Hambali zai biya si, hakan yasa na yi garkuwa da Fahad aka ban miliyan hamsin, ƙwandla ban anfana da ita ba a kuɗin nan, wallahi na rantse muku."
Hajia da ita ma ke zaune ce tace"...
*Alhamdulillah.*
29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
*RUBUTACCIYA*
👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
_NA_
*SAMIRA HAROUNA*
_SADAUKARWA GA_
*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_
*Tallah, tallah, tallah*
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*