← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 168

Sashe 83

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai kuma ya kalli Alhaji da ke ta kallon shi jikin shi na tsuma yace" Duk girman gidan nan da kuɗin ka da alfarmar ka da ikon ka wa ka taɓa ɗaukowa a gidan marayu ko cikin ƴaƴan ƴan uwa ka raina har ya cimma wata matsaya a rayuwar sa ? Babu Abbu, kai dai kullum daga mu wanda ka haifa sai iyalen mu da jikokin ka, akan su kaɗai kake tayar da hankalin ka, amma wa yake neman taimako? Wa yake cikin matsala, wa ya kwana bai ci ba? Wa ke buƙatar kuɗin magani? Duk bai shafe ka ba, ban ce baka taimako ba, ina so ne dai na nuna maka dattakon iyayen Nabila, sai sun fita suke nemowa su kawo a ci, suna iya kwana basu ci ba kafin yanzu, amma a haka suke sake ɗaukar ragamar kula da wasu ba tare da tunanin yadda za su yi ba..."

Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ci gaba da kallon kofin shayin shi yace" Ko ma dai menene Nabila yarinyar kirki ce kafin ta haɗu da ni, ni na fara keta rigar mutumcin ta, ni na fara miƙa mata zaren shisha a hannu, ni na fara bata kwalbar sirup ta sha, sannan ni na fara koya mata shan sigari, bayan wannan har...har c..."

Ƙara sunkuyar da kanshi yayi sosai yace" Kuyi haƙuri idan na ɓata muku rai, amma har ciki nayi wa Nabila kuma na umarce ta aka zubar da shi, rayuwarta ta shiga garari a wannan lokacin, amma haka ta samu lafiya kamar ba abinda ya faru, ni na sa Nabila take shan maganin hana ɗaukar ciki, yanzu saboda Allah ya dace na juya mata baya."

Wani irin kuka mai sauti Hajia ta fashe da shi, wanda hakan yasa Sabeer jan wani wawan tsaki tare da ture kujerar shi a zuciye ya bar falon, dan idan ya ci gaba da zama tsaf zai taka wuyan Fahad ya yanka shi, da kallo matar shi ta bi shi tana ayyana _" Ran maza ya sosu fa, yau sai yadda ta yiwu."_

Mama Nuriyya kuma Fahad take kallo, wani mugun tunani ne ya ɗarsu a zuciyar ta, wannan tunanin kuwa shine _" Yanzu idan fa Kuwailat ɗin ta ta haɗu da namiji irin Fahad, shikenan haka take rayuwa a gurɓace?"_, Ƙwarai ta ji tausayin yarinyar da iyayen ta ya kamata, musamman ma dai mahaifiyar ta da take ganin za ta fi shiga tashin hankali, hakan yasa har tayi kuskuren tsoma bakin ta ta hanyar kallon Abbu da yayi kamar baya da rai tace" Abbu, dan Allah ka barsu su auri junan su, tunda ya ji ya gani ita yake so, auren ya fi alkairi akan rashin yin auren."

Saida ta dire Abbu ya juya a hankali kalle ta, da mamakin kalaman ta yace" Nuriyya, na bari ya aure ta fa kika ce? Ina alkairi a auren da aka ɗaura bayan rashin sanin darajar juna? A ganin ku auren su zai zama alkairi ne? Ko yayi ƙarkon da ake da buƙata a kowane aure? Ba zai yiwu ba, saboda auren ƴan tasha ne, ni kuma in dai ina raye ba za'a yi wannan auren ba, dan duk inda aka je a ka dawo za'a nuna wannan ƴar duniyar ne a matsayin surukar Ahlan, ba zai yiwu ba na faɗa muku."

A kausashe Fahad ya miƙe tsaye shima yana kallon Alhajin yace" Shikenan, tunda ka ce haka ni zan bar maka gidan ka sai na je a ɗaura mana aure da ita, zan goge sunan Ahlan daga gaban sunana, ka ga kenan sai a kirani da sunan mahaifin Nabila, tunda shi dattijo ne."

Duk da rashin zuciyar shi kamar ta Sabeer, saida ya jefe shi da cokalin hannun shi ya kira sunan shi a kausashe, suna haɗa idanun nan nashi masu maiƙo da charme Fahad ya nemi fitsarar nan ya rasa, Shiyasa ma fa tun farko yake ta rusunawa yana tausasa murya, dan idan Abbu Mukhtar na wuri ya fi ƙarfin yayi rashin kunya. Kafin ya ci gaba da yi masa wannan kallon ya dubi Hajia da ta rufe idanun ta da tissue tana share hawaye ya dafa kafaɗar ta a raunane yace "Mamie, na wa Nabila alƙawarin za ta zo ta gaishe ki yau saboda yadda haɗuwar ku ta jiya ta kasance, dan Allah Mamie ki nema min mutumci a gurin ta ta hanyar tarban ta da mutumtawa, daga yau ba lallai ki sake ganin mu a kusa dake ba, bare har mu saka ki kuka."

Da sauri ta ɗago ta kalle shi da mamakin kalaman shi, amma da ya juya ya fice daga falon da sauri sai ta sake fashewa da wani sabon kukan, Fa'iza da abun ya fi ƙarfin tunanin ta, da ƙyar ta taso ita da matar Sabeer suna rarrashin Hajia kan tayi haƙuri. Abbu Mukhtar kuma da idanu ya ma Yaya Bilal nuni da Abbu, hakan yasa suka tashi tare suka kama hannayen shi suka nufi ɗakin baccin shi da shi, dan gaba ɗaya jikin shi ya saki baya cikin nutsuwa.

Saida suka kwantar da shi sannan suka fito, Yaya Bilal da ya ƙufula ya hassala ne ya kalli Hajia yace "Mamie ki daina kuka, ba ya ce za ta zo ba yau? Ba laifi ta zo, zai ga yadda ake tarba, na rantse da girman Allah ɗaure yariyar nan zan yi."

Da sauri Hajia ta kalle shi, haka ma Mama Nuriyya da ta ji kamar ya ɗaure ta kuma? A dake ta sannan a hana ta kuka? Ga mari ga tsinka jaka? Haba dai, rashin adalcin yayi yawa, Abbu Mukhtar ma duban shi yayi a sanyaye yace" Ba zaka ɗaure ta ba, idan kayi haka abinda muke gudu ne zai faru, wato zubewar mutumci, dan Abbu yayi hushi ne sosai, amma ni da za'a ji shawarata a aura musu juna kawai, ba adalci ya lalata ƴar mutane kuma a ce ba zai aure ta ba, haka na faruwa da mata dayawa, idan ya ƙaurace mata zai iya haɗuwa da hukunci tun anan duniya, me zai hana mu musu fatan hakan ya zama silar shiriya gare su?"

A kausashe Yaya Bilal ya kalle shi yace" A amince wai? Ya za ka faÉ—i haka kai ma dai kamar wanda y..."

Da sauri Hajia ta miƙe tsaye fuskar ta a ɗaure tace" Ba Ya ce za ta zo ba, to ta zo ɗin, ni zan tarbe ta, bana buƙatar taimakon kowa akan yadda zan karɓi baƙuawata, dan haka kowa ya min shiru da bakin shi a wurin nan."

Raɓasu tayi za ta bar falon sai kuma ta dakata ta juyo ta kalli Yaya Bilal tace" Ka kira Alhaji Abbas, ka faɗa masa ni nake neman Fati, dan Allah ya turo dreba a kawo min ita anjima."

Da mamaki suka kalle ta, amma sai Yaya Bilal ya amsa da" Shikenan Mamie." Duk sun yi mamakin me ya sa Mamie za ta ce a kawo Fati anjima? Amma dai ba wanda ya zurfafa tunani suka kama gaban su daga wurin suma kowa zuciyar shi a jagule.

*******************

Ya jima tsaye yana so ya samu wanda zai ba wa farantin dake hannun shi ya miƙawa Maama, fita yake so yayi ga shi kuma Aliyu ya riga shi fita ma, ba ya so kuma ya tura mi gadi saboda tunanin ai gwara ma a ce shi ya ki dan shi *ɗan ta* ne, amma mai gadi sam bai dace ba gaskiya.

Gyara tsayuwa yayi ya ɗan taka da tunanin bari kawai ya sallama ya kai da kan shi, sai kuma ya ji an turo ƙaramar ƙofa alamar ana shigowa, yana juyawa ya saki wani murmushi, dalili biyu ya sa shi wannan murmushin, na farko shine yadda ya ga wacce zai iya cewa yana mararin son gani, na biyu kuma ita tafi kowa dacewa da ta kai kwanukan.

Sai dai murmushin nashi bai kai ko ina ba ya tsaya cak saboda ganin ta ɗauke da wata ƙatuwar leda da kuma jug har guda biyu a hannun ta, ƙiri-ƙiri kake gane kayan sun mata nauyi dan da ƙyar take ɗaukar su. Kamar wani bita-zai zai sai kawai ya nufe ta da niyyar taimaka mata, ina dalili a ce ƴar Kuwailat ce ke lailayar kayan nan. Ita ma tana ganin shi ta saki murmushi tare da sunkuyawa ta aje kayan hannun ta tana yarfa hannun ta tana cewa "Washhhh! Wallahi nauyi kayan."

Da fari ƙura mata idanu yayi har ta gama maganar ta, sai ya ga kamar kallon yayi yawa, hakan yasa ya dubi ledar da ta aje ƙasa ya tara hannu alamar ta bashi yace "Kin gaji ne?"

Saida ta kyaɓe fuska cike da shagwaɓa tace "Na gaji wallahi, a daidai kwana na haɗu da Yaya Khalis, shine ya bani wai na kawo wa Mamie kayan ta ne da aka kai abinci shago."

Ledar ta ɗauka ta miƙa masa, hakan ya sa shi yin gaba yana faɗin "Muje."

Bayan shi ta bi da sauran kayan har suka kai ɓangaren nasu, dakatawa yayi sai ita ta shi gaba tare da yin sallama a gajiye, hakan yasa Ummu dake kwance tana kallon sama tayi nisa a tunani sam ba ta ji ba, yaye labulen tayi, dake Ummu na kwance ne kan kujerar dake kallon ƙofar ɗakin baccin ta, hakan yasa ta ba ƙofar shigowa baya sosai, Kuwailat kuma da ta ji ƙamshin girki na fitowa daga madafa sai ta ɗauka tana ciki, musamman da ba ta ji an amsa sallamar ta ba, kai tsaye madafar ta nufa tana faɗin "Yaya Jabir shigo ka aje kayan falo, zan dawo na ɗauka yanzu."

Jin haka sai ya tabbatar wa kan sa ba kowa kenan, dan haka ya yi dubara ya ɗaga labulen tare da yin wata irin sanyayyar sallama can ƙasan maƙoshi...

*In sha Allah Litinin za mu fara darasin.*

*Alhamdulillah.*
15/08/2023, 20:13 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*RUBUTACCIYA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

_NA_

*SAMIRA HAROUNA*

_SADAUKARWA GA_

*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Chapter 83 · 0% Book details