Sashe 4
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Girgiza kai Ummu tayi tana ayyana" Allah ya shirya ki." A zahiri kuma kuɗin ta nuna mata inda suke ta ɗauko da sauri ta fice ba tare da ta nemi abin karin kumallo ba, hakan yasa uwar marayu ƙwalla mata kira amma ba ta dawo ba dan kar su tsayar da ita.
Mujittafa dake cin nashi É—umamen ne yace" Lallai yau wace rana? Nabila da ba abinci abinci."
Uwar marayu dake tunanin tabbas akwai wani abu, ba dan haka ba Nabila ko me zaka mata bata zuciya da abinci bare kuma ba abinda aka mata, dole sai dai in ta san akwai inda za ta samu abinci, dan so da dama ita ko Ummu ne ke haƙura da nasu abincin su bata ita ta ci, dan in fa bata ƙoshi ba ta kma raki kenan tana kiran cikin ta ba komai. Wannan ne ma yanzu ke haɗata da uwar marayu, dan wata ɗabi'a ta tsira ta shiga gidan maƙwabta ta ɗauki awanni a can tana cin abinci, hakan ya sa take cika dare musamman idan ta san Babansu na wurin sana'arshi.
****************
Tunda asuba Baban nashi ya kama hanyar komawa wurin aikinshi, dama kuma haka yake yi, ko yana bakin aiki kasancewar yana da ɗan matsayi sai ya zo wani lokacin ya kwana gida sai yayi sammakon komawa. Tun da yayi sallah bai koma ba ya tafi ɗebo ruwa dan ya ƙarasa cika abinda babu ruwan, yana kammalawa da ɗauki butar da ta ce dole da ita zai dinga ɗiban ruwan wanka dan kar a ɓata mata ruwa.
Tana hangenshi ta taga kawai ta fito da ƙaramin towel ɗin ko cinyoyinta bai gama rufewa ba ɗauke da Uzeifatu, tunda ya ga abin dake jikin ta ya sunkuyar da kai yace "Ina kwana Aunty."
Harara ta maka mishi sannan ta miƙa mishi Uzei tace "Maza ka shirya min ita wurin aiki zan tafi yanzu kar na maka."
Ba musu ya amshi yarinyar da har so take ya É—auke ta saboda wasa da yake mata, juyawa tayi ta koma É—aki tana faÉ—in "Ka kai min ruwan wanka."
Nan ma ba musu ya gyara ɗaukar da ya yarinyar sannan ya ɗauko bokiti ya cika da ruwa ya kai mata ya ɗauki kwandon sabulu ya kai mata sannan ya zo ƙofar ɗakin ya tsaya a tausashe yace "Aunty na kai ruwan."
Jin shiru ya shi juyawa zuwa ga yarinyar dan ita ma ya shirya ta, yana gama shirya ta yayi daidai da ita ma ta fito kenan ya miƙa mata ita, ruwan da ya ɗiba dan yin wanka ya ɗauka, da sauri ta kalle shi zai shiga banɗaki tace "Me zaka yi?"
A ladabce ya juyo ya bata amsa da "Wanka."
Cike da takaici tace "Kutumar uban can! Kuma a ganinka zan iya zaunawa jiranka har ka gama ko? To banda wannan lokacin, malam fice min a gida zan rufe ƙofata."
Jiki a sanyaye ba gardama ya aje butar ya nufi wurin kayanshi na islamiyya ya ɗauka ya fita hawaye na silalo masa a kumatu, ƙwara yake so yayi wanka ko dan dattin dake jikin shi, a yanzu ba wanda zai ganshi ya yarda cewa wannan Jabir ɗin ne wanda *Fatime* (Fatima) buzuwa ta haifa, dan dalilin da yasa ma kenan kakar shi wacce ta haifi Babanshi take ƙinshi kenan, saboda kawai Bata son Maman shi dan tana buzuwa, ita kuma ta yarda cewa idan ɗanka ya auri buzuwar mace ko babarbara ko zallar bahaushiya to an raba ka dashi kenan, Shiyasa har shi Jabir duk da maraicinshi da shekarunshi lokacin da Maman shi ta rasu bata tausaya masa ba, a cewarta ai saida ta hana Mu'az ya auri Fatime amma bai ji ba, dan haka ba ruwan ta da zuri'ar Fatime.
Wata irin kakkarwa jikin shi ya fara tsabar shekararriyar yunwar dake daskare cikin shi, a ƙalla shi dai ya kai sati bai ci abincin gidan uban shi ba, shi ne kawai ke fafutuka yana samun abinda zai ci ɗin.
Jin yunwa na neman kayar dashi da sauri ya nemi inuwa ya zauna yana sauke numfashi, tunanin abun yi yake yi amma ya rasa, daga ƙarshe zabura yayi ya miƙe da sauri ya kama hanyar zuwa inda malam Sule ke siyar da wake da bredi da safe har da Shayi.
A jigace ya isa wurin nashi, dake safiya ce ko ya samu ana ta msa ciniki, hakan yasa shi rakuɓewa yana hangenshi daga nesa yaa jira ya ga mutanen sun tsagaita, amma da malam Sule ya juyo ya ganshi zaune daga yadda ya ganshi ya bashi tausayi sai ya nufo wurin shi, yana zuwa da kulawa yace "Jabir, lafiya dai na ganka anan zaune? Wani abun za'a baka?"
Da Yan kame-kame na kunyar abinda bai saba ba yace "Baban Lukman dama, dama islamiyya zan tafi, kuma gashi Babana har ya koma daji...kuma ina jin yunwa, shi ne na zo ka zuba min abincin idan Babana ya zo zan karɓo k..."
Tun bai ƙarasa ba malam Sule yayi dariya ya dafa kafaɗarshi yace "A Haba Jabir, ba komai kaji ko, bari na zubo maka, da kayi magana ma tun ɗazu ai da na baka."
Juyawa yai ya koma wurin sana'ar tashi ya fara ƙoƙarin zuba mishi, Jabir dake kallon shi kuma sai yake jin ba daɗi na alfarmar da ya nema, dan haka ma ya ci alwashin ba zai sake neman irin ta ba a dai duniyar nan, gwara yayi aikin ƙarfin zai fi masa alkairi ya ciyar da kanshi tunda dai namiji ne shi.
Yadda mai wadatattun kuɗi zai siya à zuba masa haka malam Sule ya zuba mishi, nak yayi bawan Allah ya ƙoshi sosai take nutsuwa da hankalin shi suka dawo jikin shi, godiya ya masa ya tafi makaranta duk da ya makara. *Kamar* yadda yake duk sanda ya taso daga makaranta ya kan dinga watangaririya ne a cikin unguwa har sanda matar Babanshi zata dawo saboda gidan a rufe kuma bata bashi makulli, yau ma hakane, sai dai da yaji ya fara jin yunwa tun kafin ta hauka tashi sai ya tafi wajen malam Sule, ya same shi yana kasuwarsa ta rana wacce yake siyar da salade da bredi da dankalin turawa.
Da fara'a malam Sule na ganin shi yace "Jabir har an sauko? Zauna to na gyara maka salade ko?"
Kamar ya yi abinda ya ce, sai kuma ya tuna alwashin da ya ci, sai kawai yace "A'a Baban Lukman, zuwa nayi idan akwai wani aikin da zan dinga yi maka sai ka ding bani abinci, Kaga kenan ba kyauta za'a dinga bani ba."
Dariya malam Sule yayi ya kalli fuskar Jabir ɗin, yaron nan lokacin da ya sanshi jajir dashi kamar ka taɓa jini ya fito, amma tsabar wahala da shatin duka duk yayi duhu kamar ɗan wiwi, ya girmama tunaninshi da yunƙurin son dogaro da kanshi, duk da shi dai ba wani aiki bane gareshi dayawa, amma dan ya ƙarfafa masa guiwa kan neman na kanshi sai yace "Ai ko Kaga da ka kyauta min, dan kullum da rana gyaran salade ɗin nan ma aiki yake bani, ga kuma wanke wanken kwanuka da shara idan na tashi."
Sai kuma ya gimtse fuska yace "kana gana duk zaka iya?"
Dariya Jabir yayi yace "Baban Lukman zan iya mana, har girki fa nake yi wa aunty wani lokacin, duka ba abinda ban iya ba ai."
Cike da tausayawa yace "To shi kenan, amma kana ganin ba wata matsala daga gidanku?"
Girgiza kai yayi yace "Babu, tunda dama idan na taso daga makaranta ma sai dai nayi ta yawo."
Jinjina kai yayi yace "Hakane kuma, shi kenan to, Allah ya bamu sa'a da rabo."
"Ameen." Jabir ya faÉ—a da farin cikin ya samu aiki har da tambayar "To yanzu me zan yi?"
Wani bugun salade ya nuna mishi yace "Kaga salade nan É—auki ka fara gyarawa, wanda za'a siyar da daddare ne."
Da azama kam ya É—auka ya fara aikin inda bai gane ba yana tambayawa, yana cikin aikin mlam Sule ya gyara mishi salade ya bashi ya ci, irin farin ciki da murnar daya gani a fuskar shi bayan ya gama ci ne yasa shi tambayar" Ya dai? Naga sai dariya kake kai kaÉ—ai."
Ba tare daya daina wannan murmushin ba yace" Na manta ranar da na ci abinci sau biyu ne, yau gashi na ci da safe kuma na ci da rana, a hakan ma duk abinci mai rai da lafiya."
Da tausayawa malam Sule ya kalleshi, sai ya ji tsanar uba irin na Jabir, shi ba dan an tabbatar masa da shi ya haife shi ba wallahi b zai yarda ba, dan ko ɗan riƙo iya muguntar da zaka masa kenan.
*Rayuwa* na tafiya da daɗi ba daɗi, a gurin Jabir kuma da daɗi take zuwa masa tunda yana ci yana ƙoshi sannan yayi aikin da ake biyan shi, sai dai *mutuwa* riga ce da kowane ɗan adam sai ya sakata, rasuwar malam Sule ta bazata ita ta sake sauya abubuwa da dama, ga Jabir ma yayi kuka tamkar ɗaya daga cikin yaran shi, haka suma iyalinshi sun yi kukan rashin matallafi a garesu.
Kamar yadda rasuwarshi ta zanca wasu abubuwa, haka kuma ta sake dawowa da wasu abubuwan, musamman ma tsananta rayuwar uwar marayu da yaran su da kuma son auren Ummu daga wajen Alhaji Kabir. Wannan tsoron na abinda ka iya biyowa baya yasa Ummu ce wa ita fa ta yarda tana so, hakan ya ƙona ran uwar marayu dan lokacin data ce ta yarda wanda Alhaji ya turo yana zaune ne, hakan yasa ya ce tunda dai yarinya na so kawai kar su tauyeta.
******************