Sashe 51
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes.
*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata.
Sayen na gari mai da kuɗi gida, sai an gwada akan san na ƙwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a ƙasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI- SIRRIN MANYAN MATA)._
_Bismillahir-rahamanir-rahim._
*24*
Suna cikin sake gaisawa da jami'in nan motar Alhaji babba ta tsaya tana oda, ganin Sa'ad yasa Alhaji babba sauke gilashin baya inda yake zaune yana leƙowa, da girmamawa Sa'ad ya matsa kusan motar yana rusunawa, sai lokacin ne Alhaji ya gane shi sosai, da girmamawa shi ma ba tare da tuna wasu abubuwa ba bayan alkairin da ya musu ya buɗe motar gaba ɗaya ya fito yana bashi hannu suna gaisawa sosai har da tambayar shi yaushe ya zo? Ya kuma ya ganshi a nan? Daga amsar da ya bashi yasa Alhaji faɗin "A'a ai bai kamata kana tsaye ƙofar gida ba, muje ciki ko?"
Da girmamawa ya fara takawa à bayan Alhajin kamar yadda Alhajin ke takawa a ƙafa bayan ya ma dreba umarni ya shiga da motar ciki, suna tafe suna ɗan hira yana ƙara tambayar shi, dake gidan akwai girma kuma Sa'ad na tafe ne da yanayin tafiyar Alhaji, hakan yasa ko rabin isa kusa da falo basu yi ba aka danna oda motar Sabeer ta shigo gidan, amma dake tare da Abbu Mukhtar suke yana ganin Sa'ad tare da Alhaji suna nufa ciki ya sa Sabeer dakatawa bai ƙarasa can ba.
Yana fitowa ranshi ɓace yana kallon Sa'ad yace "Kai, ya aka yi ka shigo nan? Ba na ce kar a barka ka sake sh..."
Kallonshi Alhaji yayi da mamakin yadda Mukhtar É—in ke neman zama mafaÉ—aci bayan ko magana ba cika yi yayi ba yace "Mukhtar, lafiya ? Me yake faruwa? Ban gane ka hana ya shigo ba? Baka gane shi bane?"
Sai lokacin ya kalli Alhaji a tausashe da ladabi yace "Abbu, wannan yaron ne bana son ganin shi a nan, ban ɗauki abinda ya ma Eesha a matsayin taimako ba, saboda Dalilin abinda ya mata saida aka ɗorata à magani, sani ne kawai ba kuyi ba Abbu, yanzu haka jarabawar da take yi nake jira ta gama zamu sake komawa a duba ta dan a ga ci gaban da aka samu."
Girgiza kai Alhaji babba yayi a tausashe yace" Koma me ye Mukhtar ka nutsu mana ka ji me ya kawo shi, ya ce min tun jiya yake zuwa ana hana shi shiga."
Da tausasawa ya dubi Alhaji babba yace" Abbu, dan Allah ka bari mutumin nan ya fita daga gidan nan."
Tsare shi yayi da idanu yace" Shin bai taimaki Eesha ba?"
Kai tsaye ya bashi amsa da" Abbu tarkon shi ta faÉ—a."
Da sauri amma cikin ladabi da tausasa murya Sa'ad ya tari numfashin su yace" Ba haka bane, haɗuwata da Aisha ba shiri bane, *Abba* tun jiya nake zuwa ina son yin magana da kai mai mahimmanci, haƙiƙa ni mutumin banza ne amma a baya, na kasance mai siye da siyar da miyagun ƙwayoyi, amma shigowar Eesha rayuwata wallahi na canza, na tuba daga aikata duk wani abu marar kyau sannan na nemi gafarar ubangijina..."
Numfasawa yayi yana kallon fuskar Abbu ɗin da ya ci magani sosai ya kawar da kai ya ci gaba da faɗin" Tabbas nayi cinikin wasu ƙwayoyi da aka ce min za'a min safarar su a cikin wata yarinya marainiya, sannan sun bani ita ne da zaran na cire kayana a cikin ta na mayar musu da ita dan zasu dinga safara da ita, ban san komai a kan ta ba, suna ko hoton fuskar ta bare wani abu da ya dangance ta, ban san komai ba wallahi, a ranar da nake jiran ganinta sai yaran suka kirani kan cewa ta ɓace musu, ni kuma a lokacin na haɗu da Aisha tana neman taimako saboda ɓata garin da take ta haɗuwa da su, na taimaka dan Allah ba tare da na san ko da sunan ta ba a lokacin, saboda abu biyu dana yi duba shi, na ɗaya *tsaran ƙanwata ce*, na biyu kuma *da wa za ta haɗu a gaba idan na bar ta*? Wannan ya sa na tafi da ita gidan mu, gaskiya ne a ranar na san ita ce yarinyar da aka turo ɗauke da kayana, sanadiyar hoton da aka turo min dan muyi neman ta, amma..."
Murmushi yayi shi kaɗai saboda tuna rayuwar da yayi da ita a wannan lokacin, hakan yasa har Sabeer dake tsaye lokacin ko mota bai kashe ba ya zuba mishi idanu ya ci gaba da cewa" Tana da daɗin sha'ani, tana girmama ni, tana da barkwanci, sannan bata da shakkar gaya min komai ya zo bakin ta, kaf gidan mu ba mai iya tsare ni ya tambaye ni *ina naje*? Amma ita haka take tambaya ta kai tsaye, wani lokaci ma har ta ce zata hanani abinci idan ban faɗa mata ba, ban sani ba ashe shaƙuwa nake yi da yarinyar da ban an asalin ta ba, kwatsam sai na fahimci na kamu da soyayyar ta, a lokacin da na fara shirin canza rayuwata saboda ita, sai likitan da ya mata aiki ya kira yake sanar da ni tana cikin haɗari, bayan haka ana bibiyar ta saboda an gano ahalinta kuma ba'a so ta haɗu da su ko ta wane hali ana so a sake yin nesa da ita, a lokacin naji kamar zan rasa raina saboda tabbas idan wani abu ya same ta *ba zan rayu* ba nia, a take na a kaita asibiti kuma aka saka mana lokacin komawa a mata aiki, ban yarda na sake ɓata ko da sakan ɗaya ba har saida na ga an mata aiki cikin nasara."
A zabure Abbu ya kalle shi kamar zai haɗe shi, inda Sa'ad ya marairaice yace" Wallahi ABBA tunani na shine idan na dawo da ita gidan nan mai farautar ta zai iya kamata kuma ya cutar da ita, amma idan tana tare da ni ba mai dawo da hankalinshi kanta bare ma a saka mata ido, sai kuma zuciyata da na ji ba zata iya rabuwa da ita ba, ina ganin zata min nisa kenan na har abada, saboda matsayina da nata ba ɗaya bane, wannan shine dalilin da ya sa na ƙi saurin sada Eesha da ku, amma ina so kuma burina kullum shine na ga kun haɗu, har ayyana irin farin cikin da zata yi nake, musamman idan ya zamana ni na kawo ta da kaina, nasan da na ci gaba da samun darajar da zata ci gaba da kirana da *Abbu*."
Murmushi Sabeer yayi ya matso kusan shi ya dafa kafaɗar shi dan ya burge shi sosai, inda Sa'ad ya ci gaba da kallon Abbu da ya ɗan fara sakin haɗewar fuskar nan yace" Dalili biyu ya kawo ni nan, na farko shine na nemi auren Eesha a wurinku, saboda bayan tafiyar ta na gane ba zan iya anfanuwa ba idan babu ita, na biyu kuma shine na *kawo kawuna ya nemi afuwarku* akan ɓatan ɗaya ƴar taku *Kuwailat*."
Sake É—aure su yayi da mamaki suka sake zuba mishi idanu, gyara tsayuwa yayi ya jinjina kai yace" Dole zaku yi mamaki, amma Alhaji..." Ya faÉ—a yana kallon Alhaji babba da yasan ya isa fara gajiyawa da tsayuwar nan yace" Mu shiga ciki ka zauna, zan muku bayanin ta inda labarin kawuna ya haÉ—u da naku."
Ƙwarai sun gamsu da haka, dan haka duk suka rankaya zuwa falon su Hajia, a falo suka samu Hajia tana kashe abun turaren wuta na wutar lantarki ɗakin sai daddaɗn ƙamshi, wuri sua samu suka zauna inda suka gaisa ita da Sa'ad sosai har da tambayar shi Hajia Kaka ? Abbu Mukhtar da ke ƙaguwa da son jin bayani game da babbar yarinyar sa ne yace "Muna sauraron ka, ta ina kuma kuka haɗu da Kuwailat?"
Gyara zaman shi yayi sosai a ƙasan carfet ɗin sannan ya ɗora da "Ƙanin mahaifina ne uwa ɗaya uba ɗaya, ya faɗa min abinda ya faru shekara goba sha bakwai da ta wuce, matar shi ta samu haɗari..."
Tsaf ya basu labarin kamar yadda kawu Hisham ya sanar da shi, Hajia Kaka ita kaÉ—ai ce mace a wurin, dan haka tuni ta shiga fadin" Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Dama abinda ya faru damu fansa aka É—auka a kan mu?"
Kallonta Sa'ad yayi da ladabi yace" Kusan haka Kaka, amma wallahi tun lokacin da abun nan ya faru baya da kwanciyar hankali, kullum cikin shan magani yake, sannan kullum cikin ganin likita yana duba shi, babu abinda yake buƙata yanzu da ya wuce yafiyar ku, amma mutumin da na faɗa muku yana da hannu a cikin ɗauke ƴar ba kowa bane face sirikin gidan nan."
Wani ruÉ—anin suka sake shiga da ya saka Abbu Mukhtar gyara zama akan kujerar yana kallon Sa'ad yace" Wai dakata! Kana nufin matar da na kaÉ—e shekaru sha bakwai, ita ce mijin ta ya É—auke min Æ´a ? Abun nan da ya faru ni na ma manta da shi a rayuwata, sai yanzu da kake maganar na iya tuna haka ya faru, akan shi ne aka raba ni da Æ´ata, wacce yanzu ban san a halin da take ba?"
Tsaki yaja tare da yunƙurawa zai miƙe Alhaji yayi saurin dakatar da shi, komawa yayi ya zauna yana girgiza kai cike da damuwa da takaici da kuma rashin sanin makama yace" Na kas gane wannan abun? To wa ye mutumin da ya taimaka mishi?"
Sabeer ma gyara zama yayi yace" Hakane, muna so mu sani, wa ye?"