← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 168

Sashe 129

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Haka ma a wajen Jibril da ya sake rikicewa saboda ganin yau Ummu ta saka siket É—in da ya fito da surar ta, hakan yasa shi tsare Fahad da tambayoyi a kan ta har saida ya gaji ya kalle shi a fusace yace "Wai me ye na damuwa a kan ta? Ka tsare ni da tambaya a kan ta."

Saida ya sauke nauyayyen numfashi sannan yace "Fahad, ba zan ɓoye maka ba, gaskiya ina son ƴar ka, kuma wallahi so na aure."

Ƙare masa kallo Fahad yayi sannan yace "MC, ka san dai na san ka, kuma nasan komai akan ka, ita kuma ƴata ce."

A ladabce Jibril dake son samun hanyar ratsa Ummu yace "Na sani Fahad, amma kuma ai kasan na jima da daina wanana harkar ta banza da ka sanni da ita, ka tambayi Yusuf da su Lawur, wallahi na daina kuma na jima da tuba, idan ka amince ka shige min gaba wajen samun Ummu, zan baka mamaki saboda canzawata."

E to! A dai ɗan lokacin nan da ya zauna garin nan bai ji ko ganin shi da harkar mata ba, kuma dama ai yana aure duk da bai jima da yin auren ba, ba zai hna shi damar sake zama na gari ba, saboda yana da tabbacin abun da yayi da Nabila Jibril bai yi rabin sa ba, sai dai shi Jibril ba mace ɗaya yake bi ba, dan haka yace mishi "Ban da matsala da haka MC, kamar yadda ka ji Ummu ba yarinya bace, dan zata iya tsarar ka, sannan ƙaddara ce ta raba auren ta da mijin ta, ba yarinya bace da zan maka sharar fage, ka jaraba shigar da kan ka a wajen ta, idan ta amince da kai zan fi ku farin ciki da haɗin nan, fatan nasara aboki."

Wannan magana ta sa Jibril farin ciki da ƙara masa ƙwarin guiwar tunkarar Ummu a wannan yammacin ya sanat da ita abinda yake ji a kan ta, kallon shi tayi irin sama da ƙasan nan, sai ta ga wannan yaro ai ya raina mata wayo ma? Yana tsaran ta a shekaru ne zau ce yana son ta da aure? To wane irin zama zasuyi? Me zai iya yi mata? Me kuma zai ce mata shi yanzu fisabilillah?

Take a wurin Ummu ta bashi amsa da "Kayi haƙuri abokin Abbuna, ban ƙ ba, sai dai ba zan iya soyayya da kai ba saboda wasu dalilai nawa, kuma kaga ni ba ya yarinya bace dan ƴata ma na nan budurwa da ita, ko yau ta samu miji aurar da ita zanyi, kag kai kuma ba lalle ma kayi auren fari ba, idan la kayi kuma kana so na a haka nasan gidan ku la abza'a barka ba, amma dan Allah kayi haƙuri idan maganganuna sun ɓata maka rai."

Kawai dariya ta bashi, to magana ce take irin wai mai shekara goma sha shidan nan ya zo neman auren ta, shi yanzu ne zata dinga faɗa masa maganganun nan? Ka ji fa dan Allah matar nan, girgiza kai kawai yayi yace" Ƴar Fahad, duka nasan da komai kuma na tunkare ki, kar ki ɗauki haɗina dake wani sabon abu ne ko kuma bai dace ba, nasan kina da ilimi da kuma sanin ta kamata, wanda ma bai kai shekarun ka ya aureka kun zauna bare kuma ni da nake kyautata zaton ba zamu girmi junan mu ba, amma zan baki lokaci kiyi tunani, duk wanda kika ga yana da mata kuma yana son ya ƙara wata to yana da hujja, haka kuma duk wacce kika ga ta fito daga gidan mijin ta, to ba'a son ran ta bane, dan haka ki zauna kiyi tunani..."

Raɓata yayi zai wuce yace" Zan kira ki nan da kwana uku dan naji abinda kika yanke, na barki lafiya."

Ƙwarai ya soke ta da magana ta hankali, to ya zatayi? Kawai zat yi nazarin ta gani, dan daga jiya zuwa yau ta gane wani girma da duniya da ahalin ntaa suke da shi, ta san ko dan arziƙin ahalin ta yanzu ai ba za'a hana yaro ƙarami ba ma auren ta, bare wannan da ya mallaki hankalin shi, ba tsaran ta bane gaskiya, amma dai tunda ai shekarun su ne ɗaya zata iya maleji a haka, madadin wata rana wanda bai kai shekarun shi ba ya fito mata ya saka ta jin kunyar al'umma ta kasa fita cikin mutane.

*Washe gari* baƙi na ta shirin komawar su, Ummu na taya su shirin haɗa kayan su a ɓangaren Nabila suna hirar su, da sallaa Fahad ya shigo suka amsa mishi, duk da sun gaisa haka ya sake gaishe da su tare da faɗin "Ana ta shiri kenan?"

Amsa mishi sukayi da "Wallahi kam."

Murmushi yayi sannan ya kalli Ummu ya mata alama da ta zo, tasowa tayi ta nufo shi shi kuma ya fita verandar, tana samun shi tace "Abbuna, ina ji?"

Kallon ta yayi yana ƙara matsawa daf da ita da mamaki a fuskar shi kamar wani abu ya bashi mamaki ko tsoro haa yace "Wai ƴata in tambaye ki? Dan Allah me ye tsakanin ki da dattijo Jabir?"

Saida ta ji gaban ta ya faÉ—i saboda ita har ta manta da jadawalin shi ma, amma da ya ambaci me ye tsakanin su ya É—aga mata hankali, da mamaki ita ma tace "Ban gane ba Abbu ? Wani abun ne ya faru?"

Saida ya riƙe haɓa sannan yace "Status na ɗora a wayata na bikin nan, shine kawai ya min voice na minti uku yana ja min aya da hadisai wai hakan ba kyau, sannan idan la ɗorawa zan yi wai *na cire na Maama* gaskiya, har da faɗin wai ko bana *kishin ki ne*? Yanzu da na ɗora na san maza nawa ne zasu kalla? Sannan da wace manufar za su kalla? Ki ji fa."

Da yanayin haushi Ummu ta sauke numfashi ta wulwula idanun ta sannan ta kalle shi tace" To kai me ka ce mishi?"

A sanyaye yace" Ni wallahi tsoro ya bani, yo a kausashe yake magana fa da kuma bani umarni wai nayi maza maza na goge kafin a fara gani, sai kawai na goge."

Da jin haushi ta kalle shi tace" Abbu kenan umarnin sa ka bi?"

Girgiza kai yayi yace" Ba wani abu bane ai, ko da dai kamar ƙanena ne amma dai ai gaskiya ya faɗa mana."

Ɗan tsaki ta ja ta juya zata koma ciki, da sauri ya ce" Karɓi nan ƴata."

Enveloppe ɗin da ya miƙo mata yasa ta sa hannu ta karɓa yana fadin" Ki ba wa baƙin mu su sha ruwa a hanya."

Ta ji daɗi sosai dan ta gane enveloppe ɗin akwai nauyi a ciki, ga kuma goma ta arziƙi da Hajia ita ma ta haɗa musu zasu tafi da shi, su da basu zo da kaya dayawa ba sai gashi suna ta gangamar kaya jaka jaka sabda abubuwan da aka haɗa su da shi.

Haka baƙi suka kama hanya musamman a motar gida, inda suka bar amarya da kewar su da kuma halin ta da yi mata fatan zaman lafiya, daga nan Fahad da Nabila suka fara kalar nasu zaman mai cike da kunyar junan su da nadamar rayuwar da sukayi a baya, ilimin da Nabila ta samu a yanzun ya mata anfani sosai musaman wajen zama da mijin ta, ba ta ɗaga idanun ta akan nashi, ba ta ɗaga muryar ta fiye da tashi, ba ta ɓacin rai ga buƙatun shi, suna mutumta juna da kuma salon soyayyar su mai tsafta, sai kuma barkwanci da Fahad kan saka a zaman nasu wanda yakan ƙarawa tarayyar tasu armashi.

*Alhamdulillah.*

👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*RUBUTACCIYA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

_NA_

*SAMIRA HAROUNA*

_SADAUKARWA GA_

*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_

_Bismillahir- rahamanir-rahim._

*61*
Chapter 129 · 0% Book details