← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 168

Sashe 117

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fahad da ƙarara Abbu Mukhtar ya fahimci kamar abun ya fi yi masa daɗi, dan wannan kiran da yayi yanzu haka suna kallon juna shi da Abbun na biyar ne, kuma Ummu yake cewa a bashi dan Allah ya sake ganin ta, ashe dai ƴar sa ce ita? Ashe ƴar sa ce Ummu? Ashe duk shekarun da sukayi da Nabila Ummu jinin sa ce bai sani ba? Sai kuma wata kalma da ya taɓa faɗa akan Ummun lokacin da Nabila ta zo da maganar za ta bata magani ta ba mijin ta, yana jin kunyar hakan, musamman da sukayi magana da Nabila ma akan gano Ummun da aka yi, har saida ta tuna masa ita ma da cewa "Ka gani ko? Amma kai ga ɗan duniya har da faɗin wai a ara maka ita na d..." Bai barta ta ƙarasa faɗa ba ya shiga bata haƙuri da alfarmar ta manta da wannan maganar, shi kanshi yana jin kunya da kuma takaicin kan sa. Bayan Abbu ya ba wa Ummu wayar sun sake gaisawa ne Ummu ke faɗin" *Abbuna*, kafin na san ka haushin ka nake ji saboda soyayyar ka da kuke yi da ƙanwata, amma yanzu, sai..."

Katseta yayi da sauri yana dariya yace" Yanzu sai nake birge ki ko?"

Dariya tayi ita ma tace" Ba haka ba, sai dai nake ji a jikina dama kun haÉ—u ne kawai dan ku haÉ—amu, *RUBUTACCIYA* tasa sai abinda ya faru ya faru kafin zamu haÉ—u."

Jinjina kai Fahad yayi cike da gamsuwa yace" Hakane, dan ubangiji da ya bayyana mana ke tun a waccen lokacin, da aure na so Nabila tun haÉ—uwar mu, amma sai sheÉ—an ya rinjaye mu muka shiga wata rayuwa ta daban, da ubangiji ya so mu haÉ—u tun lokacin, da iyaye sun shiga maganar mu da gaggawa, kinga kuma ta haka za'a gano abinda aka gano yanzu."

Murmushi Ummu tayi tace" Hakane, ina alfahari da kai Abbuna."

Kafin ya bata amsa Yaya Bilal ya taɓe baki yace" Wai Fahad take cewa Abbu bayan tsaran ta ne, shekarar ku ɗaya fa."

Fahad da ya ga basu ganin juna shi ma taɓe baki yayi yace" Haka kawai mutum sai ya ji yana baƙin ciki da ci gaban ka, kai ma dake Yayan Alhajin (Abbu Mukhtar) ta kira ka Abbu bare ni dake ƙane gare shi mafi soyuwa."

A kausashe Yaya Bilal yace" Ina jin ka, ina jin me kake faÉ—a marar kunya kawai."

Da sauri Fahad ya É—aga ma Ummu hannu yace" Sai anjima Æ´ata ta gaban goshina, zamu sake waya idan kowa yayi bacci."

Ummu dai dariya take ita da sauran mutanen ɗakin har da shi kan shi Yaya Bilal ɗin, Abbu Mukhtar kuma shi tunanin Hajia ne ma ya zo masa a rai da ta fara ikrarin za ta zo garin nan saboda ta ba Mama haƙuri da kan ta, dan lokacin da sukayi wayar kuka take na tuna abinda ya faru, ta ci mutumcin Nabila, ta tozarta ta, ta ƙyamace ta tare da yi mata korar kare. Ashe yarinyar nan ƙanwa ce ga jikanyar ta, ashe yarinyar da take ganin fitsararriya ce marar tarbiyyar da iyayen ta suka kasa riƙe ta, ashe mahaifiyar ta ita ta riƙe musu ƴar su har ta aurar da ita? Ƙwarai ta yarda da Fahad ya ce iyayen ta dattawa ne, kuma suna ƙoƙarin su kan tarbiyyar ta, kawai dai hali ne na ƴaƴan zamani da aka ce ka haife shi baka haifi halin shi ba, gashi yanzu tana jin kunyar kallon mahaifiyar Nabila, uwa uba kuma Nabilan da take ganin ba zata sake iya haɗa idanu da ita ba har abada.

Dan haka take so ta zo, duk da tana takaba, amma ai abun nan da ya taso muhimmi ne da zai iya fitar da kai waje, dan haka gobe za ta taso ta zo, idan har ta samu yafiyar su to zata sake jadadda neman auren Nabila g Fahad, idan ta samu amincexar su ba zata bar nan ba sai an saka musu rana da yardar Allah, hakan da suka tattauna ya sa Abbu rusa maganar tafiya gidan mijin Ummu dan nemo izinin tafiya da Kuwailat, sun jira har sai Hajia ta zo sai ta su tafi ko ina tare.

Dare na yi Ummu ta ce zasu koma gida ita da Kuwailat Mama ta nemi fashewa da kuka, dan haka hankali tashe Ummu ta kama hannun ta tace "A'a Mamie, shikenan fa tunda ba kya so, na fasa tafiyar, anan zamu kwana, shikenan?"

Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi sannan tace "Nagode aunty, ina so ne na kwana tare da ke na yau kawai."

Murmushi Ummu tayi tace "Mamie, ba aunty ba dan Allah, Ummu Kulsum."

Maƙale kafaɗa tayi tace "Um um, ban da kunya aka ce miki da zan dinga faɗin sunan ki kuma gaban ki? Ki barni da aunty kawai."

Murmushi Ummu tayi tace "Shikenan, tunda hakane nima zan ci gaba da kiran aunty kawai."

Da yanayin raha Mamie din tace "E ba zan ji haushi ba, ki kirani aunty É—in, na fi son haka ai."

Cike da farin ciki suka rumgume junan su, tsawon dare, ko na ce raba dare sukayi a falon nan suna hira, yadda Ummu ta fasa tafiya haka Aisha ta buga kai ga ƙasa ta cewa Sa'ad ba inda zata je tana ganin Maman ta da ƴar uwar ta, ba kuma yadda bai yi ba dan su tafi amma ta ƙi, sai da dai Yaya Bilal yace la Sa'ad ɗin "Wai Sa'adu me zata maka a gidan da ba zaka ƙyale ta nan ba? Ba fa gutsirar maka mata zamiyi ba."

Shafa kai yayi yana satar kallon Aisha yace "Kawu, kai dai ka barni da ita kawai, Allah kaÉ—ai yasan wahalar da Æ´ar tahlikar nan take bani idan dare yayi, ka san ba bacci take yi ba saboda mugayen mafarkai?"

Taɓe baki Aisha tayi tana murmushi tace "A dai dinga jin tsoron Allah wallahi."

Haka dai cikin raha y tattara yaran suka tafi Aisha ta yi zaman ta, su huɗu suka fara kwantawa kan gadon, Mamie, Ummu, Kuwailat da kuma Aisha, sai kuwa ga Abbu ya shigo, Mamie ce ta fara tashi zaune dan tasan me yake nufi, amma ganin gadon ba zai ishe su ba sai ya zauna gefe yana kallon su, lura da hakan Ummu ta tashi zaune ta tankwashe ƙafafu, haka yasa dukan su sukayi yadda tayi sannan suka ce Abbu ya zo ya zauna, da farin ciki kuwa ya zauna yana fuskantar Ummu, duk da dai tana jin kunya da yin wani abu, amma da ta fahimci su wayayyu ne da babu ruwan su, har ta kai bata jin nauyi ma yanzu, dan haka da Abbu ya tambaye ta ya rayuwar ta kafin yau? A hankali ta shiga sanar da su tun daga ƙuruciya har girman ta da kuma rayuwar auren ta. A duk labarin da ta basu sun fahimci mijin da ta aura babban mutum ne mai mata, sai dai basu iya ƙiyasto shekarun sa ba, duba da akwai matasan da suke ɗaukar aradu a kai su tara mata dan birgewa ko ra'ayi, babban abinda ya musu daɗi fahimci shi ɗin adali ne kuma ta rayu da shi cikin aminci, duk da dai bata faɗa musu komai game da rabuwar su ba, sai kawai ta ce dai basu taɓa samun saɓani mai tsanani har jiya da auren su ya ƙare.

*Alhamdulillah.*

[21/08 à 23:50] MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*RUBUTACCIYA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

_NA_

*SAMIRA HAROUNA*

_SADAUKARWA GA_

*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_

_Bismillahir- rahamanir-rahim._

*55*

Alƙawarin da Jabir ya ma Hajia na tsaraba shi ya zo cikawa, har ga Allah ita ta saki wannan magana, hasalima ta manta da ta haɗu da shi, amma shi tunda ya ambata bai manta ba kuma ya zo cikawa, abinda ya saka ta jin daɗi kenan duk da bata san me ye a farar kyakyawar ledar da ya bata ba, tayi murmushi sanda ta kalli fuskar shi har tana ayyana _"Ina ma tana da ƴa? Da ta ba wa dattijon yaron nan ita."_

Da ace Kabil mace ce ai da ba abinda zai hana ta miƙawa Jabir ita, amma duk da haka ta mishi godiya sosai, saboda fatan ɗorewar zumuncin su kuma har sukayi musayan lambar juna tana faɗin" Zamu dinga waya in sha Allah, sannan idan na dawo daga tafiya da zanyi zan kira ka mu sake zama mu sha hirar mu kyakyawan dattijon."

Bai san soyayyar kakani ba, haka kuma bai san wasar kaka da jika ba, dan haka yake É—aukar Hajiar a matsayin kakar sa, babban dalilin da ya sa ma kenan ya sake dawowa. Cike da kulawa Jabir ya tambya" Tafiya *annashuwata* za ta yi? Shine ban sani ba sai yanzu?"
Chapter 117 · 0% Book details