← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 168

Sashe 144

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kiran Aliyu ya É—aga dake ya san nacin Aliyu, yana É—agawa cikin tsokana kam Aliyu yace "Tonton, wallahi ka dawo daga in da ma ka tafi, ka ganni dai na gama gayawa duk wani da nasan ka sani cewa auren ka gobe ne, kai *Mansu Sadiq Abdallah* yau yake tasowa, kasan dake akwai abun ba matsala bane a gurin shi kuÉ—in jirgi, ya ce dai baa za'a yi auren ka baya wurin ba, kuma ma sai ya ci tuwon amarya ya koma, dan Allah tonton ka dawo muna jira, kai mata sune ke guduwa idan za'a musu aure ba a so, na farko a rayuwata da naga namiji ya gudu, sai tonton, Allah dai ya ja zamanin ka, wallahi auren nan zai É—auru gobe da izinin Allah."

Yana gama faÉ—a ya kashe wayar, shi dama ba wai ya ji ina yake bane, kawai ya dai sanat da shi da mutane fa suna ankare game da auren nashi, haka zai sa ya shiga hankalin shi ya san da gaske ake masa ba da wasa ba.

********************

Shigar Eesha gidan ya sa Ummu da ita suka fashe da ƙara ta murnar ganin junan si suna rumgume juna duk da tsohon cikin Eesha ɗin da ya shiga wata na bakwai, cikin jin haushi Hajia Mammie ta harare su tace "Dallah kuna wa mutane ihu kamar ba mata ba, sai kowa ya ji muryar ku."

Shiru sukayi tare da juyawa zasu shiga ciki suna ɗan turo baki da jin ita fa haka take tsohuwar nan, ita ba wani wai jika da zai ce yana da shaƙuwa da ita bare ɗa, haka kawai take ita, juyawar da sukayi ta sa ta faɗin" Ai kin san da mai lalle ke take jira ko?"

Ummu da tasan da ita take juyowa tayi tace" Ina zuwa yanzu Mammie."

Suna shiga Eesha ta kalli Ummu da kyau tace" Aunty, wai kinga yadda kika sake komawa? Wallahi kamar ba ke ba, har É—aukar idanu kike."

Sai kuma ta matse baki da irin rahar nan tace" Wannan idan *Jabir* ya gan ki a daren farko ai haukacewa zai yi."

Haraa Ummu ta maka mata tace" Mahaukaciya, Jabir din me? Jibril yake."

Da sauri Aisha ta dantse leɓen ta da ta ji ya so saka ta a uku yau, sai ta wayance tace" To ai na ɗauka duk ɗaya ne."

Hararen ta ta sake yi tace" Da bambamci, Jibril kuma ya fi daÉ—i."

Murmushi Aisha tayi tana taɓe baki, hakan yasa Ummu faɗin" Tare da wa kuka zo?"

Da hannu Aisha ta fara lisafa mata" Ni da tawagata (ƴaƴan ta), da Maman Abbu (maman Sa'ad) da autar su Abbu (Leila ƙanwar Sa'ad), da wata matar aminin mahaifin Jabir, da kuma Maman Fadila (matar kawu Hisham) sai kuma Kuwailat ɗin ki."

Da mamaki Ummu tace" Lallai tawaga, duk auren nawa ne suka zo wai? Kamar wani auren fari?"

Taɓe baki Aisha tayi tace" To ai na farko ne mu a wajen mu, kinga shirin da Mamie take yi kuwa? Yanzu haka gida na can ɗinke da jama'a baki gani ba, na baro masu aiki na ta aikin abinci, Kuwailat ma ganin su Fauzan da Mubaraka ya sa ta ƙi biyo ni, gobe fa biki ne da aka ci masa buri, kuma kowa so yake ya ga me zai faru a bikin ƴar farin Abbun mu."

Girgiza kai Ummu tayi tace" Lallai, to amma ita wata matar aminin Abban Jabir da naji kin ce, me ya haÉ—ami da ita?"

Murmushi Aisha tayi tana ayyana _" Ba zaki saka ni sakin baki ba."_ A zahiri kuma sai tace" To ke ko ai akwai zumunci sosai tsakanin su da malam Adam, kuma Abban Kuwailat ne duk ya gayyace su."

Ɗan tsaki tayi tana kawar da kai tace" Wai shi Alhajin nan na rasa gane mishi, ya sake ni amma sai wani wurin zama yake nema a cikin ahalina, shifa tun shekaran jiya yana nan, ni wallahi tsoro nake kar ya hana aure na yiwuwa, in ba haka ba wa ya taɓa zuwa auren tsohuwar matar shi."

Aisha dai dariya take yi kafin tace" In sha Allah ba abinda zai faru, wataƙila ma shi zai ɗaura auren."

Tsaki Ummu tayi tace" Allah ya sawaƙe."

"Ameen." Aisha ta faɗa suka ci gaba da hirar su, ganin zasu ɗauki lokaci ta fito aka fara yanka scoht ɗin da za'a mata lalle da shi, dan tun jiya aka mata wani irin kitso ƙanana sosai.

_*RANAR LAHADI*_

Aliyu da Fahad yake kallo da suka zage suka shirya wata ƙwarya ƙwaryar walima a cikin harabar makarantar Aliyu, shi fa abun mamakin yadda mutane suka amsa gayyatar su su, kamar dai sun zo nedan su ci gba da ƙular da shi, harabar makarantar nan timjim take da matasa ƴan 25years zuwa 40years saboda karada kuma zumunci.

Da gayya Aliyu da Fahad ke ta kai da kawo, shi Aliyu yna kiran shi da tonton, wato irin ga mijin auntynka nan ko? Shi kuma Fahad yaketa wani faɗin *mijin yarinya*, a ƙufule yakeda su, a cike fa yake da su wallahi, dan ya kula rayuwar shi ce suka mayar banza suke masa wasa da hankali, yaji ya yarda an ɗaura mana, amma menene na su dinga yi masa izgili? Bai yi zagi ba fa, amma wallahi daf yake da ya rurruga musu ashar yaran nan.

Hular da tunda aka dawo daga ɗaurin aure ya cire ta ya aje gefe ya kalla, ƙwafa yayi yada kasan hular ta masa auren nan da yake kira *auren dole*, Aliyu da ya zo giftawa ta gaban shi yana ɗauke da lemuka a hannun shi masu sanyi zai ba baƙin da suka zo yanzun ya dakata, sunkuyowa yayi cikin raɗa yace "Tonton, dan girman Allah haba ka dinga murmushi, ka wani kama fuska ka tsume haka? Mutane suka lura ba sai ka sa a ɗauka baka farin ciki bane da auren auntyna."

Irin kallon nan ya ma Aliyu, na wallahi ka kiyaye ni fa, sai kawai ya riƙe haɓa a tausashe yace" Aliyu, kuma yanzu nan kai baka jin haka kana jin kunyar hidimar nan da kake? Tunda ai kaga auren dole aka ma abokin ka ko?"

Dariya Aliyu ya saki yana girgiza kai yace" Ko kaÉ—an wallahi bana ji."

Gyara zama Jabir yayi yana girgiza kan shima yace " To kuma ba ka jin irin kunyar nan na kun haÉ—a É—a da uwa zaman da bai dace ba?"

Nan ma girgiza kai Aliyu yayi yana ƙyalƙyala dariya yace" Ko kaɗan, me zai sa naji kunya? Bayan nasan nan da wata tarain sha Allah wannan ɗan zai ma maaman shi ciki ne ta haihu."

Wani irin numfashi Jabir ya sauke, sai kuma ya ƙura ma Aliyu idanu kamar zai haɗe shi, kallon shi ya dinga yi ba ƙyabtawa har saida Aliyu ya fahimci ya fa kaishi matakin ƙarshen nan, sai kawai ya bushe da dariya ya wuce sabgar gaban shi, Jabir kuma saida ya juya ya bishi da kallo saboda ganin kawai Aliyu dai ya zubar da ilimin shi wallahi, sannan abubuwa yake ta yi dai kamar irin na ƴan iska, in ba haka kuma Maaman? Zunubin auren ma da suka ɗaura bai ishe su ba sai sun sake raya wani a ransu da shi ya fi muni ma? Me zai aike shi tunanin kutsa hanyar da Abban shi ma ya gagara iyawa da ita? Wane kalar karen ne ya cije shi da zai saka shi tunanin shiga inda ba zai iya ba? Kai a ƙaddara ma zai iya, ta ya zai iya yi wa maaman shi wannan abun? Wallahi haramiyar shi, ba zai iya yin tsirara gaban maama ba gaskiya, ƴar tsirarar da yayi yana yaro lokacin ta gani ma ya isa ai, kuma ya san ita ma ai ba ruwan ta, ba zata yarda ta ɗauko hankalin shi da wasu abubuwa ba. Kai dakata! Duka ma zaman na kwana nawa ne zasuyi? Ai ba jimawa zasuyi tare ba, zai tafiyar shi Kano ita kuma ta koma gidan su ta samu wani daidai ita ta aura.

Mansur Sadiq dake balarabe ne da yayi tattaki kawai dan wannan sabga gyara zama yayi yana kallon Jabir cikin harshen larabci yace "Ango, ya baka fara'a ne, wani abu yna damunka ne?"

Kallon shi Jabir yayi, to ita wannan fara'a wai dole ce, a sa ka auri uwar ka ace dole sai kayi fara'a? Haba mana! Ɗan yaƙe ya sakar mishi yace "Kaina ne yake ciwo, ba komai bayan haka."

Murmushi Mansur yayi yace "Kar ka damu Jabir *Abu SiddiÆ™* (inkiyar da suke ma Jabir), ba dai kayi amarya ba, ita zata sauke maka gajiyar nan."

Kallon shi Jabir yayi kamar yanzu ya fara ganin shi, Abu SiddiÆ™? Ya ma manta da ana mishi wannan sunan, kafin Jabir ya bashi amsa Fahad da ya zo gilmawa yana waya ya dafa kafaÉ—ar Jabir yace" Ango namu."

Da kallo ya bi bayan Fahad, sai kuma ya kalli Aliyu da ya dawo yana kallon Mansur yace" Maƙwabci, kaga abu Siddiƙ ko?"

Sai kuma ya kalli Jabir cike da son ƙular da shi yace" Ai in sha Allahu ma nasan yadda ka ci burin Siddiƙ ɗin nan, nasan maa wata na bakwai Maaman naka za ta antayo maka shi."

Har ya juya zai tafi Jabir ya riƙe hannun shi gam, hakan yasa Aliyu juyowa yakalle shi da tunanin kar dai ya zabge shi da mari, tunda Jabir ai har ruƙiya yana yi ko, ya dambatu da aljanu ma shi kam ba zai iya dakuwa da shi a taron nan ba, murmushi yayi yace "Tonton ya dai?"

A nutse Jabir ya miƙe sai kawai yayi gaba yana jan hannun Aliyu, bin shi yake yana murmushi har suka haɗe da Fahad da ya shigo da wasu baƙi su biyu, gaisawa sukayi da baƙin kafin Jabir ya ja hannun Fahad shima yace su zo, saida suka fito ƙofar makarantar Jabir ya saki hannayen su ya fuskance su sosai fuskar nan tashi a tamke yace "Kuna ji ko? Kunga dai nan taron da kuka haɗa ne, ku ji da sabgar ku nima ku bar ni naji da abinda yake raina, na rantse da Allah ku daina tsokanata ɗin nan, kunga dai ai Maama ba abokiyar wasan ku bace ko? Ku daina yawan ambatar ta a wurin nan bana so..."
Chapter 144 · 0% Book details