Sashe 9
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai kawai ta raɓashi kaɗan ta duƙa ta ɗauki jug mai ruwa wanda dama ita ta fito ɗauka, tana ɗauka koma ta juya zata koma ɗaki dan bata iya fita saboda mutanen dake nan kuma saboda sabgarta ne. *Tunda* ta duƙa tarin jigidar dake ƙugunta tayi ƙara kacacauuuu sakamakon doguwar riga ce a jikinta ga kuma cikin ta da yunwa, hakan yasa tana duƙawa jigidar ta zubo mata tana tashi tsaye kuma ta sake komawa kan ƙugu ta zauna... Wannan saurin sosai ya so ɗaukar hankalinshi, amma sai ya gaggauta fita daga ɗakin shi ma, dan da fari ya fara tunani me ye a jikinta ke ƙara haka? Sai kuma ya tuna cewa akwai jigida da mata ke sakawa, dan haka kawai ya share abun ya fita.
A ƙofar gida ya samu Nabila tsaye tana son shiga amma tunani Jabir na ciki kuma bata san me yake yi yasa bata shiga ba, kallon ta yayi ya ɗan taɓe bakin shi yace "Ki shiga, ban faɗawa kowa ba, amma ki sani mutumcin ki ya fi komai daraja a gareki, idan kika yarda suka lalata miki ƙuruciyarki, wata rana za kiyi nadama."
Yana gama faɗa mata haka ya wuce zuwa na su gidan, da sallama ya shiga, amma kamar yadda ya sani ba amsawa take ba, don haka a ɗar ɗar ya ɗan ƙarasa cikin filin farfajiyar yana satar kallon ta tana zaune gaban tukunya tana girkin da sai ranar da ta ga dama take bashi musamman idan Baban shi na nan, Uzei da ya gani zaune cikin bahon wanka na yara cike da ruwa tana wasa ya tsuguna gabanta yana mata wasa tare da aje ledar nan gabanta yace "Gashi, na siyo miki kayan daɗi ke kaɗai."
ÆŠan satar kallon Bara'atu yayi amma ko kallon inda suke bata yi ba, hakan yasa ya É—an juya sosai ya kalle ta cikin taushin murya yace "Aunty, dan Allah kada ki faÉ—awa Abba abinda ya faru, wallahi na daina daga yau."
Juyowa tayi ta kalle shi a hasale ranta a ɓace tace "Kar na gaya masa? Jabir ka zubar mana da mutumci kuma shine zaka ce kar a faɗa masa? Me ka nema ka rasa a gidan nan? Kawai salon ka sa a zageni a ce ni muguwar matar uba ce, sannan a zagi mahaifinka a ce na fi ƙarfin shi?"
Jinjina kai tayi irin Haba É—in nan sannan tace" Ba damuwa, ni tuni na kira na gaya masa abinda kake a unguwar nan, idan ya zo shi ka masa bayani dalla-dalla, amma ba zan É—auki wannan iskancin ba."
Ƙarasa durƙushewa yayi gabanta yana haɗe hannaye alamar roƙo yana faɗin" Dan girman Allah aunty kiyi haƙuri ki kira shi ki ce wasa kike masa, aunty wallahi kusan kasheni zaiyi, ke ma kin sani ko? Dan Allah ki bashi haƙuri wallahi na daina, kuma har kuɗin ma dana tara nayi alƙawari zan kawo miki su duka ki ɗauka na baki, amma ki ce masa wasa kike yi dan Allah aunty."
Sama da ƙasa ta galla masa harara tace" Kuɗinka ɗin banza, ni za ka ba cin hanci Jabir? T ka jira idan ya zo shi uban naka sai ka bashi kuɗin dan ya ƙyaleka."
Rufe tukunyar ta tayi tare da miƙewa tana jan dogon tsaki, kusa da Uzei ta ƙarasa ta ɗauketa daga cikin ruwan sannan ta wuce ɗakin ta fuuuu kamar an tura ta.
Dafe goshi yayi yana huro iska daga bakinshi, tunanin mafita ya shiga yi da son sanin yadda zai yi ya kaucewa dukan haukan da yake hangowa maahaifin shi zai masa idan ya zo.
*BAYAN KWANA UKU*
*Ƙarfe 05:47 na safe*
Cikin nauyayyen baccin daya ɗaukeshi ya ji saukar rikitacciyar ɗamarar ƙugun mahaifinshi a jikinshi, a rikice shi ma ya miƙe yana sosa jikinshi da waiwaigawa da son ganin wanda ya dakeshi, bai bashi damar shiga hayyacinsa ba ya kuma zuba masa wata bulalar da ta saka Jabir yin gurnanin zaki ya shiga jikin mahaifin nashi, dan kuwa tsaf ya gane mai dukanshi saboda kirarin da yake na shi zai tozarta a gari? Ruƙumƙumesa yayi tamau a jikinshi, wasa wasa sai ga Mika'il na neman kasa kubcewa a jikin Jabir da shi fa tsabar kiɗima da raraɗi ne ya shiga jikinshi har ya ma mhaifinshi wannan cakumar.
Sosai hakan ya haifar da kaurewar sarƙaƙiyar kokawa tsakanin ɗa da uban, dan Jabir iya ƙarfin da ubangijinshi ya halicceshi da shi ne yasa ya riƙe uban sosai, yayin da shi ma yake ta kiciniyar ƙwatar kansa da ma bulalar da duk Jabir ya haɗesu ya tumurmushe, a zafafe yake faɗin "Saki, Jabir saki bulalar nan? Na ce ka saki ko?"
Cikin kiɗima da rarrashi Jabir shi ma ya ke ihun faɗin "To Abba, zan saki, zan saki wallahi, amma ka ce ba zaka dakeni ba, kayi haƙuri Abba na tuba don Allah da ma'aikinsa."
Alƙawarin daina dukanshi ya ƙi ɗauka masa, dan haka ya ga kenan dai yanzu ma aka fara, dan haka shi ma ya ƙi saki sai ihun kiran sunana aunty yake wacce tana ɗaki zaune tana kallon tv, daga ƙarshe ma a zafafe ta fito saboda jin hayaniyar tayi yawa tace" Wai ni Abban Uzei me yasa kuke takurawa rayuwata?"
Dake yau ran shi ya kai ƙololuwa wajen ɓaci, wani arnen kallo ya mata a kausashe yace" Za ki ɓace min da gani ko sai na takaki a wurin nan?"
Sama da ƙasa ta watso masa harara ta murguɗa baki sannan ta juya ta koma ciki tana faɗin" Kai ma ka san ai tatsuniya ce kake faɗa wallahi."
Har ta zauna sai kuwa ta ji ƙarar faduwar babur ɗin, kuma tabbas tasan kan robar wankan Uzei ya faɗa dan gaf da babur ɗin robar take, a wani irin tsiyace ta fito da gudu tana ihu yadda kasan ita ma dukan nata ne ake tana faɗin" Na shiga uku na lalace ni Bara, wai fisabilillah me kuke son maidani ne? Shi..."
Bata idasa faɗin abinda tayi niyya ba, Mika'il ganin Jabir zai ɓata msa lokaci yasa ya shiga gwada ƙarfi da yaron, sai dai yau ɗin Jabir ƙwarai da gaske ceton kansa yake son yi, hakan tasa shi ma ci gaba da cimimiye mahaifin nashi har saida suka faɗa kan babur ɗin nan kuma Abban nashi ne a ƙasa shi a sama. Samun mijinta kwance kan babur ga ɗan a samanshi yana ƙoƙarin jan wuyan rigar shi da uban ya riƙe tamau ne yasa ta kasa faɗin ƙarshen zancenta. Dama ce yau da Allah ya ara ma Jabir, yana samu ya kubce rigarsi da tsiya da wani irin gudun ceton rai ya fita daga farfajiyar gidan tare da nufa hanyar fita, bai damu da gajeran wandon baccin dake jikinshi ba, bai kula da rigar sa t-shirt data yage da tsiya ba, bare ya tuna cewa babu takalmi a ƙafarsa, haka ya tunkari ƙofa da fatan kar ta tsayar da shi wajen buɗeta a kama shi.
Ai kuwa ƙafa yasa ya hanɓari ƙofar nan, dama kuma Abbanshi bai rufe ba saboda bala'i da ya dawo dashi gidan, dan aikinsa ma baroshi yayi da lamuncewar babban dake kula dasu, hakan yasa bai rufe ƙofar ba da kuma ganin ai har an fara sallah asuba wasu wuraren. Ko da ya samu ƙofar ta buɗu bai yi wata wata ba wajen kama hanyar da zata sadashi da titi ba tare da ya tsagaita da gudun nan ba, Abbanshi kuma saida ya fito har ƙofar gida shi ma da gudun yana ƙwala masa kiran ya dawo fa, wallahi zai yi ajalinshi idan ya kamashi.
*Wannan furuci* yasa Jabir yin nesa da unguwar nan, bai san kowa ba a garin nan, bai kuma san ko ina ba tunda ba su da kowa, mutanen arziƙin da iyayenshi suma kansu ba su haɗa shi da su ba bare yau yaje ya nemi taimakon su, wasa wasa, saboda gudun kar mahaifinshi ya kamashi ya kuma aiwatar da ƙudurinshi a kansa na cewa zai yi *ajalinshi* yasa har ya kai commune 2 ba tare da ya dakata ba.
*Alhamdulillah.*
29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
*RUBUTACCIYA*
👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
_NA_
*SAMIRA HARUN*
*MURA'ATU ULTIMATE COLLECTIONS* shin kin zuba tagumi ne uwar gida da amarya da tunanin ta inda zaki haÉ—a kayan kitchen É—inki? Ko kuma fabrics kike da buÆ™atar canzawa na kece raini a cikin sa'o'inki? Shin kina so ki san a inda gawurtattun mata ke haÉ—a nasu perfumes É—in? Ko lausasan zanen gado da kyawawan electronics gama hawa kike da bukata? To Matso kusa, zan faÉ—a miki inda ba ke kawai ba, hatta mai gidanki zaki iya rakawa dan siyo nashi electronics É—in da sauransu, wato *MUC* mun shahara a saida Kayan *kitchen*, *fabrics* na kere sa'a masu quality, *bedsheets*, *electronics*, *beauty products*, *perfumes* da *kayan kwalliya* . Bugu da Æ™ri Hajia ta akwai data tare da *katin waya* ta kowane network and *catering services*, da wannan nake cewa daku, sai an gwada akan san na kwarai. *MUC* ðŸ¤ðŸ¤ðŸ¤ðŸ§•BAMU DA SA'A.
Ga mai buƙatar tuntuɓarsu, ga lambar WhatsApp: 07038274166
Call: 07038274166 & 07031057802
Location: Kano with nationwide delivery.
_SADAUKARWA GA_
*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_
_Bismillahir- rahamanir-rahim._
*6*
Hambali na É—aga wayar Emanuel yace "Sir, wata shawara ce nayi, shine nace bari na sanar maka, idan ka amince sai a fara aikin."
A daƙile ya amsa mishi da "Uhum!"
Cikin nutsuwa Emanuel ya shiga faɗin "Sir, kaga harkarmu ta fitar da ƙwaya tana neman ta ja baya saboda tsauraran matakan da gwamnati ta shinfiɗa, hakan yasa bamu fiya samun masu kasadar tsallakar mana da ƙwayoyinmu ba, shine nake ganin me zai hana muyi anfani da yarinyar nan wajen turawa *Sa'ad* kaya, dan kasan fa babban mai ciniki ne kuma satin da ya wuce yayi ikrarin daina harka damu tunda mun Gaza, Kaga ko da an samu saɓani an kamata a bakin boda, to indai abinda nake tunani a kanta ya tabbata gaskiya, tana da juriyar ƙwayar da zata iya jure fiye da adadin da kowa zai iya jura sannan ko an mata gwajin shan miyagun kayen maye ba zasu taɓa samun ta a buge ba, amma ya ka gani?"