← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 151 OF 168

Sashe 151

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Basu sake ganin juna ba tunda abun nan ya faru, ya fita amma abata sani ba bata kuma san yaushe ya dawo ba, ita ma bayan ta kwashe duwatsun ta tana faÉ—an ya cire mata abar da tun bai da wayo take É—aure da kayan ta, amma dai rainin wayo rana guda ya tsinka mata dan bai tsoron Allah.

*Da asuba* ma da ya ji motsin alamar t tashi sai bai damu da sai ya tashe ta ba kawai ya tafi masallaci, kamar jiya ya dawo kuma bai gan ta ba ya koma ya kwanta kan sofa ya lumshe idanun shi.

Yau ma bacci suka sha abun su ba mai tashin su saida ya farka dan gaban kan shi, a kasalance ya miƙe ya shig ɗakin shi kafin ya fito da shirin wanka... Har yayi ya gama Ummu bacci take da gasken gasken saboda ta jima ba ta yi bacci ba daren jiya tana tunanin yadda za ta sake kama kan ta yaron nan ya daina ganin damar ta.

Madafa ya wuce dan duba me ta dafa? Ganin babu komai yasa ya dawo falon yana tunanin abun yi, gidan su zai je wajen Hajia ya ci? Ko wajen siyar da abincin zai je ya siya? Ba dai zai iya juriyar yunwa ba gaskiya, dan yanzu ulcer din shi za ta motsa ya zo kuma yana rakin ciwo gaban waccen *ƴar*, sauran kayan marmarin da ya zuba fridge ya ɗauko ya ƙara sha, yana gamawa ya koma ɗakin shi ya ɗauko kwalin madara da baya rayuwa babu ita tunda ya samu wadata, cokali ya sa yana shan saida ya ji ta isheshi sannan ya kora ruwa, hamdala yayi ga ubangiji sannan ya kalli ƙofar ɗakin ta, girgiza kan shi kawai yayi ya fita, yana so yayi koyi da manzon rahama ta hanyar shiga ɗakin ta duk asuba ya tabbatar tayi sallah sannan su gaisa, amma ba yanzu ba, dole sai sun saita zaman ta ta fara gane shine mijin ta sannan zai fara, amma yanzu idan ya fara za ta ɗauka ai dan ta girme shi ne yake mata haka.

*Wunin* ranar haka suka yi shi basu wani haÉ—u da juna ba sai sau É—aya, shi ma da ta fito daga madafa ne ta wanke kwanukan da tayi anfani da su ta dawo É—akin ta same shi zaune, shine ma da za ta shige ciki ba tare da ya kalle ta ba shima yace "Zuba min abinci."

Ba tare da ta kalle shi ba ita ma, kuma ba ta tsaya dan bshi gamsashiyar amsa ba kawai ta ci gba da tafiya tana faÉ—in "Idomie ce na dafa, kuma babu."

Shiru ya mata kawai ya haɗe, dake ba baƙon yi wa kan shi abu bane tsaf ya miƙe ya shiga madafar dan wuni yayi da yunwa ta yadda ba zai ma yarda ya kwanta bai ci ba, idan kuma ya kwanta ɗin ya san dole zai tashi.

Ummi na saka kayan bacci za ta kwanta ta ɗan ji kamar ƙamshin ana soya ƙwai, sai kayi tayi tunanin hancin ta ne, imma kum Jabir ne dai ohon mishi, ita dai ba zata masa wahala ba gaskiya dan kar yaji a ran shi ita matar sa ce bare har ya ci gaba da yi mata abinda ya ga dama, so take kafin ma kawu Bilal ya aiwatar da shirin shi shi ya haƙura da ita ya sake ta, tunda ai ta san shi bai da juriyar yunwa in ji Aliyu. Ƴan magana suka ce wai *wanda ya iya ya huta*, bayan ya ci ya ƙoshi saida ya rage soyayyen ƙwai saboda sahur, dan haka yana tashi ya ci abu shi ya sha ruwa yayi alwala ya wuce masallaci.

*Alhamdulillah.*
[05/09 à 13:58] MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*RUBUTACCIYA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

_NA_

*SAMIRA HAROUNA*

_SADAUKARWA GA_

*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_

_Bismillahir- rahamanir-rahim._

*70*

Da wuri ya shirya zai fita saboda Mansur da suka taso shi da Aliyu kuma yau zai wuce zuwa Niamey daga nan ya ɗaga zuwa ƙasar shi, yau baki da baki yake so ya gaya mata girki yake so, dan shi haro yanzu bai ga tayi girki mai sunan girki ba, ɗakin ya wuce a nutse tare da tura ƙofar a hankali yana yin sallama, kwance ya same ya tana bacci... Ko da yake bai da tabbacin baccin take tunda ta rufe fuskar ta da filo kamar mai neman kashe kan ta, saida ya ƙarasa ya sa hannu ya ɗauke mata filon sannan ya ga idanun ta rufe bacci dai take yi, aje filon yayi yana ƙare mata kallo, riga da wando ne jikin ta, kula wandon har ƙasa yake sannan bai kma jikin ta ba sosai, sai rigar dake da siraren hannaye ta fito mata da fararen hannayen ta, garin kalle kalle ya kai duban shi kan wuyan ta dake shafe sumul fari ƙal, a hankali ya yo ƙasa da idanun shi sai kan wasu abubuwa da ya ga sun yi wani irin cirko cirko haka kamar zasu huda rigar, kamar wanda aka bashi assignement akan su sai ya shiga duban su da kyau yana so ya gane wai su ne ko dai abar nan ce da mata ke yin ciko? Tunda ai maama ita ta shayar da Kuwailat.

Ya dai kasa ganewa kawai sai ya zura yatsun shi biyu ya ja hancin ta, ba wai yayi dan wata manufa bane, yayi ne kawai saboda yana sha'awar yin wasa da matar auren shi ko ba ita ba, yatsina fuska tayi ta sauke idanun ta kan shi dake tsaye, a nutse ta gyara kwanciyar ta sannan ta tashi zaune tana ƙare mishi kallo, da salon faɗa ta buɗa baki tace "Jabir wai ya kake neman maidani wata kakar ka ne? Saboda Allah ni tsarar kace da zaka dinga min abinda ka ga dama? Me ye haka wai? Shi wanda ya sa ka ka aure nin ne ya ce ka dinga min haka?"

Zuba mata idanu yayi kawai yana kallo, saida ya sauko ƙafafun ta tana shafa fuskar ta ya miƙo mata kuɗin hannun shi, kallo shi tayi sannan tace" Na me ye?"

A tausashe yace" Girki nake so, zanyi baƙi."

Gyara zaman ta tayi irin zaka rufe ɗan ka da masifa sannan tace" Wanda ka bayar jiya ma banyi komai da su ba, kuma ina ga ai zai fi idan zaka saka ni aiki ka roƙe ni alfarma ko?"

Azumi yake, amma tunda na nafila ne ba matsala, ya san wa ye shi, haka Allah ya halicce shi abun tayar da sha'awa ba ya masa kaɗan, ya san zai yi wuya idan ya taɓa jikin ta azumin shi ya ci gba da zma lafiya lau, amma gaskiya baya son rainin nan na Maama fa. Miƙewa tayi a ɗan hassale ta raɓashi ta wuce wajen kayan ta za ta ɗauki towel dan ta yi wanka kafin ta samu abinda za ta saka ma cikin ta, takon shi ta ji a bayan ta da ya saka ta saurin juyowa, sai ta ga da gaske shi ɗin ne kuma har lokacin nufo ta yake yi da yanayin da ta kasa tantancewa, dakewa tayi ba ta nuna alamar mamaki ko tsoro ba ta ɗauki towel ɗin sannan ta sake niyyar raɓa shi za ta wuce.

A gadarance ya kamo hannun ta, kafin ta ankara ya haɗata da bango sannan ya matse ta ta hanyar yi mata shamaki ta kowace kusurwa da hannayen shi, inda idanun shi kuma ke cikin nata idanun dake kallon shi cike da masifa tana faɗin "Jabir na faɗa maka bana son irin haka ko? Ka daina taɓa ni dan ni ba sa'an wasan ka bace."

Ba tare da ya daina kallon ta ba cikin dakakkiyar murya yace "Me ye kike so namiji ya mallaka kafin ki fara kallon shi a namiji?"

Yatsina fuska tayi da sauri tana kallon gemun shi tace "Me? Ban gane ba?"

Sai kuma ta gyara tsayuwar ta fuska a haÉ—e tace "Jabir matsa daga kaina kar na ji maka ciwo."

Ɗaga girar shi ɗaya yayi yana ƙara tamke fuska yace "Jaraba."

Da mamaki ta kalle shi tace "Na jaraba me?"

Cike da shaƙiyanci ya kanne mata idanu yace "Ji min ciwon mana."

Iska ta huro daga bakn ta tare da waina idanun ta irin ka dame ni ɗin nan sannan tace "Wallahi da gaske nake maka, matsa daga kusana Jabir, saboda Allah ko kunyar taɓa ni baka ji? Kana kirana da Maama amma kana min duk iskancin da ka ga dama, ina ce ni ɗin matar Abb..."
Chapter 151 · 0% Book details