Sashe 8
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin sa'a yana shiga gidan ya ci karo da Ummansu tana ɗaukan itace daf da shiga ƙofar, da fara'a da sakin fuska suka gaisa kafin a saiɓance ya shiga nuna mata ciwon dake ƙafarshi yana faɗin "Umman Lukman, dama ciwo ne Naji, to ƙafata sai kumbura take kuma tana yin ruwa, shine nace dan Allah idan kin san maganin da zan yi anfani da shi ki faɗa min?"
Cike da kulawa da tausayawa ta duƙa tana duba ƙafar tana faɗin "Subhanallah! Jabir me ya sameka a ƙafar?"
Kafin ya bata amsa kuma sai tayi saurin É—agowa tana kallon shi tace "Kai! Jabir ai wannan shegen ciwon ne, wani abu ya cijeka ne?"
Gaban shi ne ya fara faÉ—uwa jin ta ce shegen ciwo, sai kuma tayi saurin fara takawa tana faÉ—in "Biyoni Jabir, akwai magani a wurina ma."
A hankali ya shiga takawa yana binta yana kuma gaishe da matan dake gidan suna ta hayaniya, har cikin falonsu ta umarce shi da ya shigo, bin umarni ta yayi ya shiga ya zauna bakin ƙofa akan tabarma dake ba kowa a ɗakin, uwar ɗaki ta shiga jim kaɗan ta fito ta fita waje jim kaɗan ta sake shigowa riƙe da ludayi a hannun ta, tana zuwa ta zauna kusanshi tace "Mu ga ƙafar?"
Zuro ƙafar yayi yana kallo ta laƙato maganin a yatsarta sannan ta rufe ido tana motsa bakin ta alamar wani abun take faɗa, sai kuma ta riƙe ƙafar tashi kusa da ciwon ba tare da ta buɗa idon ba, ta jima haka kafin ta buɗa idanun ta sannan shiga shafa mishi maganin tun daga kan ciwon har zuwa zagayenshi, saida ta gama shafa mishi sannan ta miƙo mishi wani ƙullin tace "To ga wannan, idan zaka kwanta sai ka sake shafawa, gobe ma haka zaka yi, in sha Allah zuwa jibi za ka ga ya ƙame tare da maganin..."
Sai kuma tayi murmushi tace "Wannan maganin na ɗaya daga cikin laƙaninmu, wannan ciwon naka zai warke ne ba tare da yayi ruwa ko jini ba kamar yadda aka saba gani, zai ƙame ne kawai kuma zai kashe wanda ke cikin jiki ba idan ya sakar maka wasu dafin a jiki, sannan kariya wannan ciwon ba zai sake harbin ka ba sai dai wani ciwo daban kuma."
Da jin daÉ—i sosai Jabir kamar zaiyi kuka yace" Nagode sosai Umman Lukman, Allah ya saka da alkairi."
Murmushi ta masa tana kallon fuskarshi cike da tausayawa tace" Ba komai Jabir, sai dai har sanda ciwon zai warke kar kayi ta'ammali da abincin da ya shafi wake da hatsi."
Jinjina kai yayi sai kuma ya shiga miƙewa yana faɗin" To Umman Lukman, kuma shi ma wannan ciwon zan iya shafa mishi wannan maganin...?"
Yayi maganar yana ƙoƙarin ɗaga rigar shi sannan ya ci gaba da faɗin" Shima kwana biyu kenan yau nake jin ciwo a wuri kuma kamar ya kumbura shi ma."
Miƙewa tayi tana kallon bayan nashi can sama kusa da kafaɗa, dai dai lokacin kuma *Ummu Kulsum* ta fito daga uwar ɗaki ta sauke duban ta kan bayanshi da kaso biyu cikin uku duk raɗo raɗon shtin bulala ne da ya masa baƙi abun ka ga fatar dake da haske. Daga Ummu har Mama dukansu sun san zaman da yake a gidan uban shi, dan haka ba wacce tyi magana face tausaya masa da sukayi, Mama n dubawa kuma tace "Jabir ai shine har ya sakar maka wani bakin, amma bari na shafa maka na yanzu a bayan."
Tana daf da laƙato maganin ta shafa mishi wata matashiya duk da kuwa mata ce ga ƙanen margayi mijinta, amma dake su ɗin Fulani akwai ƙaramin jiki ya sa zaka ɗauka budurwa ce, ba tare da sallama ba ta faɗo ɗakin saboda albishir ɗin da ta zo yi wa *Hafsat* ɗin da zumuɗi tana ganinta bata ma kula da me take yi ba cikin harshen fulatanci tace "Adda Bulo, ki zo kiga abun arziƙi?"
Dakatawa tayi daga shafa masa maganin da take shirin yi ta kalle ta tace "Lafiya dai ko?"
Cikin dariya ta saki labulen tana cewa "Ke dai ki zo, kar su tafi baki basu tukuici ba?"
Jin abinda ta faɗa yasa maman dakatawa ta fuskanci Jabir, amma kafin ta faɗa masa ya mata uzuri ta je ta dawo sai ta ga Ummu da tunda ta fito take tsaye tana kallon bayan Jabir ɗin duk ta yi takwaf takwaf da fuska alamar tausaya mishi. Murmushi ta mata sannan tace "Yawwa Ummu, zo mana ki ƙarasa shafa masa maganin nan a baya, hannun shi ba zai kai ba ai da ya saka da kanshi."
A ladabce sosai Ummu ta saki labulen uwar É—akin tana tahowa ta amsa da "To Mama."
Tana zuwa ta karɓi ludayin Mama kuma ta fita, tunda ya juyo sau ɗaya ya kalli fuskar Ummu bai sake kallon ta ba bai kuma ce mata uffan ba, haka ita ma ba ta ce masa komai ba sai laƙatar maganin da tayi cikin saiɓi sosai ta kai yatsarta tana ɗan shafa mishi maganin wanda ke nuni da tana yin hakane saboda ba ɗan uwanta bane na jini.
Sosai take ci gaba da duba jikin shi da duk ke farfashe tsabar suka, wani wurin m har yanzu a birdinshi yake bai baje a jikinshi ba, gani take me yasa mahaifinshi ke masa haka? Me yasa shi kuma Jabir ba zai dain abinda yake yi ba har ake dukansa? Sannan me yasa mahaifinshi bai lura cewa É—ansa yayi girman da ya wuce duka ba?
*A* wajen Jabir kuma nasa tunanin sam bai bi hanyar tunanin Ummu Kulsum ba, tunaninshi bai wuce yadda sam a unguwar nan babu yarinya mai nutsuwa, hankali, kunya kamar Ummu, shi dai duk iya ganinshi da ita a waje to za ta tafi islamiyya ko kuma ta taso, idan ba haka ba sai dai gidan su, sau goma idan za ka shigo zaka sameta tana aiki ne. Abun burgewa a tare da ita shine, yadda ko islamiyya da makarantar boko da take zuwa bayan tayi shigar mutumci har da niƙab take sakawa, hakan yas wasu ma basa ɗauka budurwa ce sai dai a mata kallon matar aure.
Tunda yake bai taɓa ganinta a haya tare da ƙawa suna tafe suna dariya da buɗar baki a titi ba, kusan kullum ita kaɗai za ka gani musamman ma a dai nan erea unguwarsu, a sanyaye kum a nutse za ka ganta tana tafe, idan ta ga wanda ta sani sai dai ka ji ta gaisheshi da ina kwanan ku? Amma shi, shi dai gaskiya a rayuwarsa ma maganar da sukayi da ita ƙidayayya ce, shi a titi ma basu taɓa ko da gaisawa ba, ita bata mishi magana bai san me yasa ba? Shi kuma miskilanci ke hana shi gaishe ta duk da kuwa yana sane sosai ta girmeshi a ƙalla da shekaru *uku* ko ma fiye da haka.
Gefenshi data koma tana kallon shi tace "An gama." Ya sa ya gyara rigar shi tare da kallon fuskar ta shi ma, fara ce sosai, ga ta kyakkyawa da manya idanu farare tas, ga ta kuma doguwa, don yanzu haka da suke tsaye ta fishi tsayi dan bai wuce kafaÉ—arta ba.
*Kallon* cikin tsakiyar idanun shi da tayi da niyyar yi masa magana ya shi saurin ɗaga idanunshi sama ya kalli daga goshinta zuwa sama kaɗan, luwai luwai ɗin baƙi ƙirin ɗin gashin da ya kwanta a goshinta luf-luf yake kallo, dan tana kallon idanunshi gaban shi ya faɗi sannan ya ji ta masa kwarjini sosai, haka kuma sai yake hango *yarintar ta* a cikin idanun nata da har yake ji a ransa anya kuwa wannan *auren* da za ta yi tayi ma kanta adalci? Shin ta ina suka dace ita da Alhaji Kabir? Amma da ya tuna ita ɗin fara ce sol kuma kyakkyawa, su kuma masu kuɗi burinsu kenan su kwashe kyawawan mata su ɓoye a gidansu, sai ya ga ai hakan ba wani abu bane.
Ummu kuma dake wasa da maganin cikin ludayin da nutsuwa sosai tana kallon fuskarshi kamar wacce za ta rarrasheshi tace "Dan Allah, ka daina ɓatawa Abbanka rai har yana dukanka, idan ka ga zai dakeka kayi gaggawar bashi haƙuri, ko dai baka san ka wuce duka da bulala bane? *Jabir*?"
Duk da ya so sadda kanshi sanda take magana, dan ita yanzu ai babbar Hajia ce tunda gobe za'a ɗaura aurenta da mutumin da shi kansa bai san adadin dukiyar daya tara ba. To amma yadda take magana tana dakatawa hutu, da yadda take yin maganar a nutse matuƙa sannan kamar wacce ke jin bacci, sai hakan ya ɗauki hankalinshi har ya saci kallon leɓunanta da na ƙasan ke kalar jajir na saman kuma yana da haske sosai.
Sosai maganar ta ta so bashi dariya har ya ji kamar ya tambayeta _"Shin baki san mahaifina yana dukana bane ko babu laifi? Ko baki san ya kan dakeni bane idan matarsa ta faɗa masa ƙarya a kaina? Sannan baki taɓa tunanin ina bashi haƙuri ba, amma baya ji saboda bushewar zuciya?"_
Madadin ya mata wannan tambayoyin, sai kawai yayi murmushi, ko ba komai ya ji daÉ—in shawarar ta gareshi, kuma zai iya cewa wannan rana ta musamman ce gareshi, yau har Ummu ta yi masa doguwar maganar da ta ci sakanni kusan ashirin. Da fara'a ya rusuna ya É—auki ledar alawar da ya siyowa Uzei tare da maganin da Mama ta bashi sannan ya sake kallon fuskar ta sannan ya buÉ—i baki shi shi ma a nutsen yace "Tom, nagode... *aunty*."
Sai kuma ya gyara tsayuwarshi a ladabce yace "KuÉ—in maganin fa? Nawa ne ake biya? Sai..."
Da sauri amma a hankalce kamar mai raɗa ta ɗaga masa hannu tarie da cewa "A'a, ba'a karɓan ko sisi..."