Sashe 67
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_
_Bismillahir- rahamanir-rahim._
*32*
Cikin zafin rai har idanun ta sun yi jajir tace "Yayar tawa? Aunty Ummun kake faÉ—awa haka?..."
Sai kuma ta shaƙo wuyan rigar shi a haukace tana faɗin "Kamar uwa fa na ɗauketa, kenan akuyancin ka har ya kai ka ji kana sha'awar uwata? Allah ya tsine maka albarka Fahad, wallahi b zan taɓa yafe maka ba, sai naga bayan ka Fahad dan ban ga anfanin rayuwar ka ba."
Ko gezau Fahad bai yi ba, e ya san bai kyauta ba da ya faɗi haka, amma ya za ta mare shi? Suna samun saɓani sosai, amma basu taɓa kwatanta dukan juna ba, dan haka ma ran shi ya ɓace kawai ya ɗauketa da marin da ya saka ta faɗawa kan gado, a gigice ta kalle shi dafe da kuncin ta tana tashi zaune tace "Ni ka mara? Fahad ni ka mara?"
Da shaƙiyanci yace "Fuskata ba fuska bace kenan? Sai ta ki uwata Nabila?"
A haukace ta yunƙura zata tashi tsaye tana faɗin "Allah ya tsine ma..."
Da ƙarfi ya tura ta ta sake faɗawa kan gadon, cikin zafin nama ya tausheta tare da rirriƙe hannayen ta yace "Ni ba ɗanki bane ko sakarai da zaki dinga tsine min, ki san me kike faɗa min, banza wawuya."
Kallon shi tayi tana sauke numfashi, yanzu nan da ta sake ɗaga mishi murya ya ɗauko ƙwayoyin nan ya haɗa, sai idanun shi su rufe ya duƙar da ita ya fara caccaka ba tausayi, dan haka sanin halin shi sai kawai ta sassauta murya tace" Na ji, ɗaga ni."
Saida ya harare ta sama da ƙasa sannan ya ɗagata ya ci gaba da shirin shi, tashi tayi ita ma a tsanake ta buɗa wani cof da ta ga yana aje magungunan shi, ta kuwa yi sa'ar ganin wanda take nema, dan haka ta zari sashe ɗaya tare da juyawa ta fita ko kallon inda yake ba ta yi ba, dan tayi niyya sai ya gane kuren shi ya kuma bata haƙuri sannan za su shirya, idan ba haka ba kuma to sun fara gaba kenan da ita da shi.
Tana fita falo jakar ta da ɗan kwalin ta ta ɗauka tayi gaba ko sallama, Shima yana fitowa ya ga bata nan taɓe baki yayi dan yasan me hakan ke nufi, an fara gabar kenan sai kuma bayan wasu kwanaki, ama ba zai yarda su jima ba dan rashin ta na saka shi tashin hankali da jin ba daɗi. Fita yayi ya rufe gidan dan wasu uzurrrinkan shi kafin gobe tayi yana so zai je gida dan kuɗaɗen shi sun yi ƙasa, da ya je kuma ya samo ko ta halin ya ya zai sake dawowa ne ya ci gaba da rayuwa da Nabilan shi.
********************
A karo na ba adadi kenan ta sake dafe marar ta dake mata ciwo sosai kuma ciwo ne ba irin na al'adar ta zata zo ba, hasalima ko sati biyu bata yi ba da gamawa, runtse idanu tayi sosai saboda ciwon ba daÉ—i, kama yake da na wanda wani abu ya maka nauyi a mara, hakane yasa har tayi tsaki ba tare da sanin ya fito fili ba. Kuwailat dake kusa da ita suna aiki tare ne tace "Mamie lafiya? Ko baki da lafiya ne?"
A hankali ta buɗe idanun ta ta kalle ta, sai tayi murmushi ta girgiza kai tace "A'a, lafiyata ƙalau."
Cikin kulawa yarinyar tace "Amma Mamie naga kamar za ki yi kuka, har idanun ki fa sun yi ja."
A wahalce Ummu ta girgiza mata kai tare da É—aukar cokalin miyar za ta juya tace "Ba komai, marata ce kawai ke É—an min ciwo."
Da kulawa Kuwailat tace "Sannu Mamie, Allah baki lafiya."
"Ameen." Ta faɗa a taƙaice. Ba ta sake cewa komai ba har Alhaji Kabir ya shigo madafar da sallama, amsa mishi sukayi inda ya ƙaraso da fara'a yana cewa "Ashe duka anan kuka tare kuka barni can ni ɗaya."
Ji take kamar laulayi take, hakan yasa daga can ƙasan zuciyar ta tana jin farin ciki na zata sake samun haihuwa bayan duk wannan shekarun, to amma yaushe ne cikin ya shiga, sati biyu da ya gabata ta ga jini, ranar da tayi tsarki Alhaji ya bar ƙasar, kafin nan ya ɗan sadu da ita, bai dawo ba sai jiya, to kenan cikin bai yi sati biyu ba? Rashin kuzari da kasala ba daga ita bane, dan haka yanzu ma ba alwawala tare da ita kawai ta amsa mi shi da "Muna nan muna maka girki."
Murmushi yayi yace "Kuna min girki ko kuna mana?"
Ba fara'a a fuskar ta tace "Duka."
Kallonta yayi, kawai shi yasan akwai abinda yake damun ta tun jiya, maganar da sukayi ce ko kuma dai wani abun na daban? Shine kuma bai sani ba dai, yajin da ta ja tare da riƙe robar hannun ta gam ta furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!"
Cikin kulawa ya matsa daf da ita tare da dafa kafaɗar ta yace "Ummu, lafiya? Ƙonewa kikayi?"
A raunane ta girgiza mishi kai tace "A'a."
Da kulawa ya sake cewa "Ko baki da lafiya ne?"
Nan ma girgiza mishi kai tayi tace "Ba komai." Kuwailat da ta ji amsar da ta bashi sai ta dube shi a ladabce tace "Abba, marar ta ce wai take ciwo."
Kallon Kuwailat yayi da tayi maganar, sai kuma ya kalli Ummu ya sake riƙe hannun ta yace "To ko muje asibiti na raka ki?"
Kamar wanda ya mata wani abu sai kawai tace "A'a, bana so, naji sauƙi."
Yadda tayi maganar kamar a kausashe yasa shi É—an yin jim yana kallon ta, lura da kamar ba ta kyauta ba sai kuma ta wayance tace "Shikenan, idan bai daina min ba har aka jima zamu je."
Jinjina mata kai yayi yace "Shikenan, dan Allah fa idan kin ji abun ya tsananta ki faÉ—a min.?"
Jinjina masa kai tayi kafin ya juya ya fita ya bar su dan su ci gaba da aikin su, haka ta ƙarasa aikin à daddafe da taimakon Kuwailat har suka idar.
Suna cin abinci bayan sallah azahar Nabila ta kawo mata maganin da yanayi na sauri saboda adaidaita da ta tsayar a waje, tana bata maganin tace "Gashi aunty, Fahad biyu yake sha, amma kinga tunda ke ai tso..."
Da sauri Ummu ta buge mata baki, maganar da bata ƙarasa ba kenan sai dariya tayi ta juya da gudu ta fice tana faɗin "Sai kin kira ni aunty kin bani labari."
Da kallo ta bita har ta fice, sai kuma ta kalli maganin kamar tana tuhumar kan ta ko maganin, ƙarasa cin abincin sukayi inda Kuwailat ta gyara wurin da wanke kwanukan da aka ɓata dan lokacin tafiya islamiyyar ta ya kusa kasancewar uku na rana suke shiga.
Har ta kammala girkin dare ba ta da wani kuzari a jikin ta, haka ta gama ta yi duk yadda ta saba yi tare da haɗin lemu na ɗanyar citta da lemun tsami, saida ta ware wanda zasu sha ita da Kuwailat sannan ta jefa maganin a na Alhaji ƙwaya biyu da tunanin idan zai iya to su kwana dare yana haƙar ta har ta rabu da abinda ke damun ta, duk da kuwa tunanin ta ya fi raja'a da ƙaramin ciki gareta, amma sai ta ayyana _"Ba abinda zai samu ɗan cikina, sai ma lafiya da zai ƙara."_
*Bayan* sallah isha'i ya shigo kamar yadda ya saba, sai dai da wani yanayi na kasala da kamar damuwa, a gajiye ya zauna kan kujera kusa da ita yana cire hular shi tare da dafe kan shi, cike da kulawa ta kalle shi tace" Abban Ummu, lafiya?"
Saida ya sauke ajiyar zuciya sannan ya kalle ta a sanyaye yace" Wallahi kaina ne kawai yake min ciwo."
Da yanayin tashin hankali ta É—ago daga kujerar ta dafa shi tace" To bari na kawo maka magani."
Girgiza kai yayi a tausashe yace" A'a, ki bar shi ma, na sha magani yanzu kafin na taho, ina so dai na kwanta ne kafin anjima."
Da gamsuwa ta jinjina masa kai tace" To, Muje na raka ka." Tashi yayi da ƙyar saboda nauyin da jikin shi ya mishi wanda shi kanshi fa ya tabbatar shekaru fa sun ja sosai, saida ya shafa kan Kuwailat da ta kalle shi da tausayawa tace" Sannu Abbana, Allah baku lafiya kai da Mamie."
Murmushi ya mata yace" Ameen Æ´ar Abba, mun gode."
Ɗakin suka shiga inda ta taya shi cire babban rigar shi har da ta cikin sannan ya kwanta, zane ta jawo masa ta rufe mishi rashin jiki saboda acn da ta kunna dan baya zama sai da ac shi ɗin, har za ta miƙe ya riƙe hannun ta suka kalli juna, cikin nutsuwa yace "Dan Allah Ummu Kulsum, ki je asibiti gobe a duba ki, idan baki je ba kuma jibi idan su Aliyu suka dawo zan sa Aliyu ya tirsasa ki ki je."
Murmushi tayi saboda tuna yadda Aliyu ke girmama ta shima, sai dai bayan girman da yake bata ma yana iya faÉ—a mata gaskiya kai tsaye sannan kuma ya ce wallahi Mamanmu sai kin yi kaza fa, jinjina mishi kai tayi tace" Shikenan, zan je."
Murmushi shima yayi tare da lumshe idanu, hakan ya sa ta miƙewa ta fita daga ɗakin ta rufe mishi ƙofa, sai lokacin ne da ta ga teburin abinci da kayan da ke sama ta tuna da maganin da ta saka a lemu, wani mlalacin murmushi tayi kawai ta maida hankalin ta gaba ɗaya kan Kuwailat dake biya mata karatun ta.
*******************
Wani tagumin ya sake yi yana ƙurawa lambar da ya aika kira idanu, yana ji tana ƙara har ak yi nasarar ɗauka, cikin wata kakkausan muryar dattijon da daga ji kasan mazan fama ne aka ce "Hello."