← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 168

Sashe 13

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ma fi aksarin su duk ɗaga kafaɗu sukayi alamar ba komai a yi ɗin, inda suka juya suna fita daga ofishin nashi, matar nan mai ƙiba ce kaɗai jikin ta yayi sanyi take tafiya kamar wacce ƙwai ya fashe ma a ciki, da kallo ya bisu har suka fita sannan ya koma ya zauna yana lalubar wayarshi dan kiran aminin nasa kamar yadda ya faɗa.

*Matar* nan kuwa mai ƙiba na fitowa cikin sauri ta fita waje kamar za ta yi wani uzurin ta shiga banɗaki, wayar ta ta jawo ƙarama ta danna wa wata lamba kira, ana ɗagawa cikin ladabi da yin ƙasa da murya tace "Yallaɓai, ni ce ke magana, *Lami*."

Daga can ɓangaren cikin wata ƙosasshiyar murya da dattako haɗe da jan aji a taƙaice aka amsa da "Me ya faru?"

Sosai ta sake sauta muryarta sannan tace "Yallaɓai, duk da dai ban san manufar da tasa kake sa ana ɗaukar ƴan matan da suke gidan tallafin da ka gina, amma dai ya kamata a ɗauki mataki akan manajan *Buhari*, dan yanzun nan daga ofishin shi nake, kuma yayi kirarin damƙa maganar nan ga jami'an tsaro, Shiyasa na kira dan na sanar da kai kayi wani abu, yallaɓai ka da asirina ya tonu."

A daƙile cike da rashin son can zancen yace "Shikenan, zan yi wani abu a kai."

Yana faÉ—an haka ya yanke kiran, ita ma tusa wayar tayi cikin rigar Mamanta sannan ta fito cikin sanÉ—a tana waiwaye waiwaye da fatan kada kowa ya ganta bare a zargeta.

*HY* Hospital, a keɓantaccen ɗakin gwaji na musamman aka killace ƴan matan tare da kwantar da su kan gadon aka ɗauresu gudun matsala, kan ta farkon wani likita mai fararen kaya ya ƙarasa tare da soka mata allurar kashe zafin jikin da ta saka ta yin siririyar ƙara sai kuma ta rufe idanu, a hankali a hankali bacci ya fara ɗaukarta har dai tayi nisa sosai.

Ɗaya matashiyar na kallo ta ga yayi tsaga a tsakiyar rigar ɗayar gefen cibiyar ta daga ƙasa kaɗan, tana kallo ta ga yana ta gabato da kayayyakin aiki a gabanshi har saida ya kawo komai sannan ta ga ta ɗauki wata ƙaramar wuƙa irin ta likitoci ya daidaici inda ya shafa wani alcohol a ƙasan cibiyar yarinyar gefen hagunta ya ɗora ya fara yankawa... Ita duk wannan abu da ta ga yana yi bata ɗauka cutar da su zaiyi ba, duk da tana da yaƙinin inda suke akwai haɗari, dan basu ma san a ina suke ba, amma dai bata ɗauka cutarwar ta kai haka ba har saida ta ga jini na fitowa a jikin yarinyar da ita ko a jikin ta sai wani lullumshe idanu take dan ba wani nauyayyen bacci ne ya ɗauketa ba duba da allurar ba ta bacci bace.

Ƙodar yarinyar ya cire duka biyun, saida ya fara killace su dan sune abu mafi soyuwa da daraja a gare su kafin ya dawo dan yi mata ɗinki, yana gamawa ya nufi *Nana Aisha*, take ta fara ihu da fizge fizge tana jijjiga gadon tamkar za ta kwance ta gudu, kuka take kwarai da gaske tana kiran "Kayi haƙuri, kayi haƙuri dan Allah Babana, ka yafe mana laifin da muka maka ba zamu sake ba, Wayyo, Wayyo Allah na, taimako, jama'a taimako, zai kashe mu jama'a a taimaka mana."

Duk da ya ga hagagi take, kuma yasan ba zai wuce na bashi haƙuri kar ya taɓa ta ba, amma shi Sam ba ya ma jin me take faɗa da harshen hausanta, dan haka ya daidaici hannun ta ita ma ya soka mata allurar nan... Wata ƙara ta sake ƙwallawa har lokacin da ya cire tsinin allurar, amma bayan haka sai ta ci gaba da fizge fizge tana bashi haƙuri.

Shi kuma ɗan gefe kaɗan ya koma ya bata mintunan da sinadarin zai fara aiki kanta, minti ɗaya ya shuɗe, biyar haka har ya ga an kwarari minti goma, da yanayin tashin hankalin da ya fara ziyartar sa ya kalli agogon hannun shi sannan ya yi sauri ya ɗauki ƙaramar kwalbar dake ɗauke da sinadarin da ya zuƙa ya zuba mata ruwa yana ƙara karantawa.

Da gaske ruwan ne, kuma tabbas sun shiga jikinta, hakazalika sune aka zubawa waccen É—ayar da ba yanzu allurar za ta sake ta ba, sanin da ya yi idan ya ce ya sake mata wata a nan take babban haÉ—ari ne ga lafiyar ta yasa shi komawa da baya ya nufi inda wayar shi take, É—auka yayi ya kira ogan nasa.

Bugu uku aka É—aga cike da zumuÉ—in son jin labari mai daÉ—i aka ce "Dr. Emanuel, ya ake ciki? Anyi nasarar aikin?"

Da sigar tashin hankali Emanuel yace "Sir, da matsala fa."

Amsawa aka yi da "Wace irin matsala kuma Ema?"

Saida ya zuba idanu shi kan Aisha da ke kallon shi ita ma tana tunanin to ko dai ya ji roƙon da ta masa ne sannan yace "Ɗaya yarinyar yallaɓai."

"Me ya same ta? Ƙodar ta na da matsala ne?" Ya tambaya da son sanin me ye matsalar, cikin rashin sani da tabbas Emanuel ya shiga faɗin "Sir, na mata allurar kashe jiki, amma sai naga sam allurar ba ta yi tasiri a kan ta ba, har yanzu fa jijjiga take a gadon bayan kuma an samu shuɗewar minti goma yanzu da yi mata allurar."

Da son gasgatawa mamallakin asibitin kuma mamallakin gidan marayun da aka É—auko yaran yace" Ka tabbatar?"

" E yallaɓai." Ya faɗa da alamar cike yake da mamaki sannan ya ɗora da" Da haɗari babba idan na sake mata wata yanzu ba tare da an ɗauki wani tsawon lokaci ba, shiyasa na kira na gaya maka."

Ajiyar zuciya *Hambali Ya'u* ya sauke sannan ya bashi umarni da" Ka sake mata wata allurar Ema, ta hakane zamu tabbatar wane rukuni ne jininta, na san kasan akwai wanda jininsu ke da ƙarfin da ba magani ke musu kai tsaye ba."

A tsanake Emanuel yace" Sir... Are u sûre about that?"

" Yes Ema, do it." Ya faÉ—a cike da tabbaci, jinjina kai yayi sannan yace" OK sir." Ya kashe wayar tare da sake tunkarar Aisha da ta É—an yi lamo tana sauraren shi duk da yaren da yayi da farko bata san komai da yace ba bayan tambayar tabbaci da yake daga wajen abokin hirar sa sannan kuma ya ce shikenan.

Ganin da gaske ita zai sake wa allura ta shiga ci gaba da jijjiga gadon tana kiran a taimake ta zai kashe ta, yanzu ma allurar ya mata, amma ya sake bata wasu mintuna shiru ba alamar ma ita aka wa bare ta ji. Hakan ya tsorata shi ya kafe Aisha da idanu, gaba É—aya shekarun yarinyar ba zasu wuce *16* ba, to amma ya aka yi bata jin wannan allurar?

Ba tare da ya sassauta kallon tsoro da mamakin da yake mata ba yace da ita a harshen turanci "Wacece ke?"

Duk da cikin firgici take da É—imuwa, amma É—abi'arta na nan ba abinda ya sauya, sanyin magana kamar mai raÉ—a tare da lullumshe manyan idanunta dake farare tass tace " *Nana Aisha Mukhtar Saheeb Ahlan*."

Sake tsatsarta da idanu yayi kamar zai haÉ—eta yace" Alhan? Ahlan? ÆŠaya tak na sani a rayuwata, attajirin mai ikon faÉ—a aji, babban ahalin da zai yi wuya a rasa wanda ya san su, kina nufin shi dai dana sani?"

Manyan idanunta ta fara yin luuuu da su tamkar dai wata wacce ke cikin maye, sai kuma ta sako da wasu hawaye ta girgiza masa kai a sanyaye sosai tace" Ban sani ba, ban san su ba nima, na dai san kawai sunana Aisha Mukhtar Saheeb Ahlan in ji *Mother*."

ÆŠan jinjina mata kai yayi alamar gamsuwa sannan yace" Ke Æ´ar *Agadez* ce?"

Girgiza kai tayi a marairaic tace" Ban sani ba, ban san ma ina ne haka ba, ni a gidan marayu na tashi."

Sak kafeta yayi da ido kamar zai faɗa cikin fuskar ta, dan shi sosai yake hango wani abu a fuskar ta, sai dai kuma abun ya shige masa duhu ƙwarai, a rashin sani, a rashin me bakinshi ya furta ba tare daya daina kallon ta ba yace" *Da buƙatar ki waiwayi tarihin ki*... A'isha."

Ita ma manyan idanunta masu kama da na Æ´an maye ta zuba masa tare da furta" Tarihina?"

Sai lokacin ya tuna suɓul da bakan da yayi, da sauri ya juya mata baya yana sake lalubo wayar sa ya kira oganshi, yanzu ma ba ɓta lokaci aka ɗaga ana tambayar sa ya ake ciki? Da kiɗima da kuma saranda yace" Yallaɓai, gaskiya yarinyar nan ba mutum bace, yallaɓai na sake mata allurar nan, amma fa ba wani abu da ya nuna sinadarin zai yi anfani a jikinta, ina ga mu barta haka."

Cikin gigita Hambali ya miƙe daga inda yake cikin hargagi yace" Ba zai yiwu ba Ema, ka sanni ka kuma san yadda nak kasuwancina, rashin jin allurar kashe jiki ita ya shafa, ni abinda na sani kawai shine ka cire min duka Ƙodar ta biyu ka adana min, idan ta rayu zamu kula da ita ne har lokacin da za ta kasa rayuwa sakamakon rashin wasu muhimman sassa a jikin ta, idan kuma ta mutu daga nan wurin, ta hutar da kanta da wannan rayuwar marar tabbas, dan haka kayi aikin ka kawai."

Dafe kai Emanuel yayi da hannu ɗaya yana ɗan sosa ƙeyarshi har sanda Hambali ya kashe wayar, yadda Aisha ta ƙura masa ido haka shi ma ya ƙura mata suk kallon juna, ba zai iya aikin nan akan yarinyar nan ba, shi wata sanayya yake ji game da yarinyar, ga kuma abun al'ajabin dake tare da ita. Dan haka kwatsam wata dabara ta faɗo ran shi, da sauri ya sake bugawa Hambali dan dol sai ya sanar da shi, idan ba haka ba ya taimaki Aisha ta gudu to fa kai tsaye shi zai tunkaro, ya kuma san waye Hambali tsaf zai raba shi da rayuwar sa.

*ME CE CE DAMUWARKI*?

Rashin ni'ima?
Rashin gamsar da mai gida?
Warin gaba?
Bushewar gaba?
Ƙaiƙayin gaba?
Kurajen gaba?
Zubewar nono?
Cikowar nono ?
Shin kin san da akwai garin da ba'a baki sai an tabbatar baki da kishiya saboda kar ki É—auki alhakinta?

*Kina buƙatar...*
Chapter 13 · 0% Book details