Sashe 71
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wata uwar harara ta watso mishi wanda tun shigowar shi ko kallon arziki ba ta mishi ba sannan ta ja tsaki tace "Ban da lokacin ku, ai ina da waya, kuma ina ganin kiran shi, ban yi niyyar É—auka bane, idan kuma akwai ubana a cikin ku kusa in yi magana da shi."
Taɓe baki Ja'afar yayi yace "Jaraba."
Maida wayar yayi a kunnen shi yace "Ta ce tunda ba ubanta bane kai ka shafa mata lafiya."
Daga wajen Fahad bai kama yarda ba ita ta faɗi hka ba dan yasan za ta aikata, amma dake yasan lagon ta sai yace ma Ja'afar "Ce mata abubuwa sun tsananta a nan, a taƙaice ma Abbu ya hanani fita ko ina, ya ce *auren haɗi* zai min."
Yana faÉ—in hka ya kashe wayar, kallon ta Ja'afar yayi yace "Kin ji ya ce a faÉ—a miki wai dagus É—in shi ya saka shi a mari, kuma suna daf da É—aura masa aure da Æ´ar dangin su."
Wani irin mummunan faɗuwa ne gaban ta yayi, cikinta ya hautsina da ƙarfin bala'i, tsigar jikin ta ta tashi da wani irin bala'en'en yanayi, take zufa ta fara tsatsafo mata, amma fa duk wannan tashin hankali da ruɗun da ta shiga tsaf ta ƙi nunawa, sai ma basarwa da tayi ta kalle shi tace "Sai me ? Ina ruwana to?"
Da mamaki ya sake wara idanu ya kalle ta, sai kawai ya juya ya fita a ɗakin yana faɗin "Hayaƙi ya fara yawa a kan ki."
Saida ta tabbatar ya tafi, ta tabbatar yayi nisa, tasan ba zai ji ta ba, sai kuwa ta yi tsal ta tashi zaune ta fashe da wani irin kuka mai cin rai tana laluban wayar ta dake kan kujerar tana faɗin "Na shiga uku na lalace, Fahad kar ka ci amanata, kar ka ci amanata Fahad dan Allah, wallahi kai kaɗai nake so, Fahad kai kaɗai nake kulawa, duk ƙawayena sun san ni da kai kaɗai, idan bamuyi aure ba Fahad bakin duniya kashe mu zai yi....maza mana ka ɗaga." Ta ƙarashe faɗa saboda kira da ta aikawa Fahad ɗin, saida ya ɗan basar sannan ya ɗaga, kafin ta ce wani abu yace" Mun shirya kenan?"
Sake fashewa tayi da kuka, hakan yasa Fahad zabura ya miƙe tsaye hankali tashe yana faɗin" Nabila, me aka miki? Wa ya saka ki kuka?"
Cikin fitar hayyaci tace" Ban sani ba, da gaske ne za'a maka auren haÉ—i?"
Wani shaƙiyin murmushi yayi dan ya gane dalilin da ya sakata kuka, dan haka saboda ya wahalar da ita yace" E, Abbu ma fa ya kulle ni a ɗaki."
Tana jin haka ta ja majina tace" Shikenan, zaka gani."
Take ta yanke kiran ta miƙe tsaye ta nufi uwar ɗaki tana faɗin" Zaka gani, Fahad Saheeb baka san wacece Nabila ba har yanzu, shima kuma tsohon bai san wacece ni ba, wallahi gidan zan je na fito da kai, yadda na ƙi jin maganar iyayena na ƙi auren kowa, kai ma baka isa ka zauna da kowace mace ba idan ba ni ba."
Ƙwarai da gaske take, dan kuwa kaya ta haɗa a jakar ta matsakaciya sannan ta canza kayan ta ta fito da niyyar zuwa ta ciro ticket ɗin tafiya inda Fahad yake da daren ranar, dan so take kafin ya farka baccin safe ya gan ta gaban shi.
*WASHE GARI*
Da safe sosai Mama ta zo duba jikin Alhaji da Ummu t faɗa mata bashi da lafiya, har ɓangaren Hajia Asiya ta raka ta suka dubo shi, basu jima ba saboda rashin kyakyawan tarbe da Maman ta samu a wajen Hajia Asiyan suka miƙe dan tafiya, har za su tafi Alhaji dake zaune cike da rashin jin daɗin yadda ya ga Asiya ba ta saki fuska suka gaisa da Mama ba yace "Maman Kuwailat."
Da sauri ta juyo cike da ladabi ta amsa da "Na'am."
Da fara'a à fuskar shi yace "Munyi waya da yaran nan, in sha Allah zuwa bayan azahar suna isowa, na ce ko zaki iya saka tukunyar ki dasu?"
Wani ƙayatacen murmushi ta saki da ladabi tace "Me zai hana? Ma sha Allah, har sun taso kenan? To Allah ya kawo su lafiya, sai sun zo ɗin."
Jinjina kai yayi da farin ciki da kuma son ya ce shima yana buƙatar fura, amma kuma sai ya ƙyale kawai saboda gudun rigima, Mama ma barka ta mishi da fatan su iso lafiya sannan suka fice. Tana raka Mama ta koma ɓangaren ta ta shiga aiki ba ɓata lokaci, abinda ya shafi gashi da soyawa kawai tayi sai lemu da ta haɗa na zoɓo da cucumber, kafin azahar ta kammala komai dan Kuwailat ma da ta taso ta taya ta aikin, hakan yasa sukayi saurin ƙarasawa sannan suka shirya sukayi sallah.
Tana kan sallaya aka yi sallama ƙofar ɗakin, Kuwailat da ta riga ta ida wa ta amsa tare da nufa dan ta gane muryar mai gadi ce, jim kaɗan ta dawo da ledaa hannun ta ta aje gaban Maman ta tace "Mamie, Idi ne ya ce wai Abba ya ce ki dama mishi furar nan yanzu."
Da kulawa ta amsa da "To, É—auko min tasar da nake damu da ita."
Ba ta zauna ba ta wuce madafar dan É—auko abinda ta aike ta, jim kaÉ—an ta kawo ma ta tasar da ludayi ta aje, juyawa tayi ta sake É—auko ruwa da zuma ta aje, a tsanake ta shiga damun furrar nan har ta kammala sannan ta kai fridge tare da kama hanyar É—akin ta dan ta canza kayan ta kafin nan furar tayi sanyi ko kaÉ—an ne sai ta kai mishi.
Kuwailat ce ta fara jin odar mota, da sauri ta miƙe tsaye da zumuɗi da kuma fara'a a fuskar ta tace "Lahh! Ga su Yaya nan."
Da gudu ta tunkari ƙofa za ta fita, hakan yasa jigidar dake ƙugun ta kaɗawa sosai tana bayar da sautin cacas cacas, da mugun sauri Ummu da ta ji haka saboda yadda ta yi wayo ta ga jigida a ƙugun ta da na Nabila to ta a ganin ta kamar jigida kwalliya ce da take cika adon cikakkiyar mace, dan haka Kuwailat na fara zama ta fara saka mata, ba dan ma Nabila da duniyanci ya sa ta cire ama ta ce tana saka wa ba kullum ba dai.
Da sauri ta katse ta da "Ke dakata."
Dakatawa tayi tana kallon ta da tunanin to me ta yi kuma? Cike da gargaÉ—i tace mata "Kina mace kina gudu kamar tsuntsuwa, malama tafi a hankali."
A ladabce ta amsa da "To Mamie." Sai kuma ta ƙarasa fita da sauri fuskar ta fal da murmushi na za ta ga Yayun ta biyu wanda Jabir har yau ba ta san shi ma ba ɗan gidan nan bane dan ba wanda ya faɗa mata. Ummu kuma shigewa tayi ɗaki dan ta canza kayan ta sannan ta fito.
*Tana* fita motar su na tsayawa, tsaye tayi ita ma tana ƙurawa motar idanu, Yaya Khamis ne ya fara fitowa bakin shi har kunne yana faɗin "Yau ai saraki kuke, motar ma ni zan buɗe muku."
Yana buɗe motar ƙafa Aliyu ya fara zurowa kafin ya fito gaba ɗayan sa fuskar shi fal murmushi yana kallon Khamis cikin wani tattausan harshen da sai ka yi da gaske gane hausar yace "Kai dai ka sani Khamis, ka maida mu wasu Kakanin ka ko?"
Idanun Kuwailat tsaf a fuskar shi, mamaki take? Al'ajab take? Farin ciki take? Sai ta rasa me za ta ji game da hakan, ita fa balarabe take gani ya fito daga mota, ana haka kuma sai Jabir da ya fito ta ɗaya ɓangaren ya zagayo inda suke cikin wata sassauƙar shiga ta doguwar riga kalar fara tas, ba hula a kan shi bayan dogon wandon da kake iya gani ta ƙasan ƙafafun shi da kuma wasu lafiyayyun takalmi ƙirar Turkey da suka fito da kan yatsan shi ɗaya, sai agogo kawai irin ta fata baƙa da ta kama tsintsiyar hannun nashi.
Ƙara sake bakin ta tayi tana ayyana _"Dukansu larabawa ne."_ Da gaskiyar Kuwailat, dan kuwa dukansu jajir da su basu da maraba da larabawan, babu wanda bai gane ta ba a cikin su, dan hoton Kuwailat ne ma a profil ɗin Alhaji kasancewar ta auta kuma yarinyar da yake so ƙwarai a cikin yaran shi, dan haka suka gane ta musamman ma Jabir dake jinjina girman yarinyar da kuma hango irin tarbiyar da ta samu duba da hoton da Alhaji ya ɗora tana sanye da hijab, yanzu ma gata da hijab à jikin ta duk da bai ga wani abu ba a jikin ta da yake kyautata zaton shi take ɓoyewa. Aliyu ne ya fara matsawa kusan ta tare da dafa kanta yace "Autan Abbanmu, ashe kin fi girma a zahiri?"
Cike da kunya Kuwailat ta rufe fuskar ta da hijabi, wanda hakan da tayi ya sa Jabir tsurawa *bakin ta* idanu yana ganin kamannin mahaifiyar ta a fuskar ta sak, ba wanda ya tanka masa, ba wanda ya saka shi dariya, sai kawai tsintar kan shi da yayi da yin murmushi saboda kawai murmushin da Kuwailat tayi mai cike da kunya da nutsuwa, Aliy ma dariya yayi tare da dafa kafaɗar ta ya juya da ita zuwa ɓangaren mahaifiyar shi yna faɗin "Kina lafiya autanmu?"
Sauke hannayen ta tayi tace "Lafiya lau Yaya, an zo lafiya?"
Amsawa yayi da "Lafiya lau, ya jikin Abba? Yana wurin Mama ko?"
ÆŠaga kai tayi ta dube shi sannan tace "Lafiya lau, jikin shi ma yayi dama."
Khamis dake janye da jakunkunansu cike da tsokana yace "Kuwailat baki gaishe da *Alaramma Jabir* ba kinga fa sai kumbura yake."