← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 168

Sashe 77

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Uzeifatu na zaune da waya a hannun ta tana ta danne danne, cike da takaici Aba ya raɓa ya ɗauka musu kujeru cikin ɗaki ya kawo musu suka zauna, duk gaisuwar da suke mata ba wani yabo ba fallasa take amsawa ciki-ciki, Uzei kuma Aliyu da ya matuƙar birge ta ta tsare da idanu tunda ta fahimci Jabir ne Yayan ta, da irin yanayin rashin kamun kai ta washe baki tace "Ina yini?"

Wani arnan kallo Jabir ya mata, mai tattare da saƙonnin dayawa, na farko shine ki kama kan ki, na biyu kuma zan yi maganin ki, na uku kuma bana son iskanci, na ƙarshe kuma shine tashi daga nan saboda suturar jikin ki. Take Uzei ta ji murɗawar ciki, kwarjinin shi ya kamata, ko ba Yayan ta bane ya mata kallon nan dole ta kimtsu, bare kuma Yaya ne da tasan zai iya falle ta da mari, dan haka ta miƙe tana kallon Aliyu da shi wallahi bai ma kula da ita ba bare ya ga tsiyar da take, Aba kawai dake ta zube musu kayan ci da sha yake kallo, irin farin cikin da yake ciki, da zumuɗi da murnar ganin ɗan sa, za ka rantse yanzu ne aka haifo Jabir a duniyar.

Jabir mamaki yake sosai da yadda matar Baban nashi ta tarbe shi, me ya mata? Me ya sa bata ƙaunar shi? Shin ya taɓa mata wani abu ne a zaman su? Ko laifin Maman shi ne ya shafe shi? To amma ai basu zauna tare ba bare har wani abu ya haɗa su, ko dai halin ɗan adam ne da shi kanshi yake ƙin abu ba'a bisa tsari na koyarwar addini ba? Share zancen kawai yayi suka ƙara gyara zama suna cin abinda mahaifin nasa ya tanadar musu duk da basu jin yunwa, wasa wasa basu bar nan ba sai da sukayi sallah magrib, da ya ce zai tafi Abansa kamar zai yi kuka saboda rashin so, dan kuwa har ɗakin da ya ware mishi ya kuma sa aka gyara saida ya nuna ma Jabir ɗin, amma sai ya rarrashe shi da zai dawo, matsalar ya ce ma Abba zai zauna tare da su ne, yanzu kuma baya da lafiya, bai kamata ya bijiro masa da maganar komowa nan ba, amma zai so idan ya samu lafiya sosai, shi kan shi Aban sai yaje ya ganshi har ya masa godiya kan taimkon da ya ma Jabir ɗin, daga nan kenan sai ya dawo wajen Aban shi shi ma, to da hakane sukayi sallama suka tafi suna mai cike da begen juna.

******************

Cikin nutsuwa ta fito daga wankan ɗaure da towel ɗin da ana ɗaurashi a akai ne idan an wanke a ƙugun ta, hakan yasa ya tsaya mata iya cinya wanda da za ta duƙa tsaf za'a ga jikin ta, sai kuma sama da ba ta rufe ba ko alama, wayar ta dake kan gado ce ta ɗauki kuka tare da sake bubbuga ƙofar da aka yi, cikin jin haushin kalar bugun da ake mata wanda bata da tabbacin ko waye duk da tasan Fahad ya ce mata yana zuwa tace "Wai waye yake neman karya wa mutane ƙofa?"

A tsawace Fahad da takaici ya gama kama shi yace "Ke dallah buɗe wa mutane ƙofa, ƴar wulaƙanci."

Ƙarasawa tayi ta buɗe ƙofar tare da hangameta, gyara tsayuwa yayi da niyyar zazzaga mata, amma da ya gan ta hakan sai ta sake ɗaga masa hankali, dan dama tun abinda ta mishi a ƙage ya zo har yana ɗiga a hanya, sai kawai ya auka ɗakin kamar an hankaɗa shi tare da cakumota ya rarumi ƴan biyun ta inda ya sa ƙafa ya turo ƙofar.

*Bayan wasu awanni*; tana kwance kan ƙirjin shi yana shafa kan ta har zuwa fuskar ta cikin sanyin murya dake nuna gajiya yace "Beela."

A tsananin gajiye ta amsa da "Ummm!"

Yana ci gaba da shafa ta yace "Cewa nayi..me zai hana muyi aure? Tunda Kinga da gaske gida maganar aurar da ni suke, kuma bana so Nabila, bana son wata mace idan ba ke ba, dan Allah ki bari muyi aure yanzu, ba laifi munyi rayuwa irin wacce muke so, mu bari yanzu shari'a ta halatta mana junanmu, zamu fi jin daÉ—i."

Tashi tayi zaune ta na lalubar towel ɗin ta tana faɗin" Mun yi alƙawari ba zamuyi aure ba sai nan da shekara biyu, me yasa zaka yi maganar yanzu? Na zo ne dan na dakatar da auren, amma ba dan mu muyi ba."

Tashi tayi tsaye tana tana ɗaura towel ɗin, da sauri ya miƙe ya riƙo hannun ta har ya sauko daga kan gadon yana cewa" Nabila har yaushe zamu yi ta jan rayuwar nan? Ya isa haka mana, son ki nake Beela, kuma da aure, ya kamata muyi aure mana."

Yatsia fuska tayi tace" Gaskiya ban shirya ba."

Dafe ƙugu yayi yace" Sai yaushe? Lokacin da kika ga dama kenan? Nabila ba'a ma aure haka, komai da kike gani lokaci gare shi, idan ya zo miki to kiyi anfani da damar ki, idan ba haka ba za'a kai lokacin da kike son shi ido rufe ki kasa samu, sannan Nabila ki yi tunani mana kiga mu misali ne ga mutane dayawa, ƙawayen ki nawa ne samarin da suka zama abokan lalatar su suka ci amanar su ta hanyar auren wasu? Da idanun ki kinga ƙawar ki an dake ta kuma aka jefar akan titi saboda saurayin zaiyi aure ta ce ita ya kamata ya aura ba wata ba, sannan Kinga wanda à ƙarshe har saida alƙali ya raba su saboda ta ce ba zai auri kowa ba bayan shi ya lalata ta, shin me kuma kike nema bayan haka Nabila? Tun farko na faɗa miki ina son ki, kuma har yanzu ina son ki kuma da aure, abinda muka yi bai sa na ji kin fita a raina ba, na yarda dake da gaba ɗaya zuciyata, Nabila nasan da ni kaɗai kike mu'amala, haka kem kuma kin sani dake kaɗai nake rayuwa, to me muke so bayan haka?"

Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi dan ta gamsu da abinda ya faɗa, amma ai tasan shi ba zai mata haka ba, dan haka ta nemi raɓawa ta wuce tana faɗin "Ni ba bana son auren bane, amma dai..."

Da sauri ya fizgota har ta faɗa jikin shi yana cewa "Amma dai me? To ni ne baka so ki aura? Akwa wani abun da kike ɓoye min ne?"

Grgza mishi kai tayi alamar a'a sannan tace "A'a, ba komai."

Ƙara tausasa murya yayi yace "To me ya sa ba zaki amince ba Beela? Muna son junan mu, kuma mun yarda da junan mu."

Wani bahagon kallo ta masa tace "Yarda? Fahad yarda kake magana? Shin ko kasan na ɗaya daga cikin abinda yasa auren ƴan duniya baya ƙarko? Wannan yardar da ka ambata, Fahad ba wai bana so muyi aure bane, amma maganar gaskiya mu faɗawa kanmu ita, wane irin zama zamuyi? Me duniya za ta ce a kan mu? Idan mun haifi yara zasu iya tausaya mana? Ba ma wannan ba, muna da tabbacin ubangiji zai bamu haihuwar? Bayan ni da kai ɗin nan har ciki mun zubar, a bar ma maganar magani da nake sha dan hana ɗaukar ciki, kana ganin bayan duk wannan zamu iya yin zama na gaskiya da amana da kai?"

Girgiza mishi kai tayi tace" Fahad, duk son junan mu sai mun fara tsanar kan mu, idan muka yi aure a haka ni ba zan samu salama ba haka kai ma, duk da dai na sani da iya junan mu kawai muke mu'amala, amma bana jin idan ka fita cikin garin zuciyata za ta nutsu sannan shaiɗan ba zai raya min kana wuraren da muka saba zuwa tare da kai ba, idan kuwa har za ka je wurin da ka saba zuwa sannan kasa duk wani abu da zai sa ka fita a hankalin ka, to fa da yiwuwar ka iya kula kowace mace ma. Sannan kai, zai iya yiwuwa duk sanda zan fita ka ji baka yarda da na tafi ni kaɗai ba, za ka iya tunanin zan tafi wani wurin ne daban, imma wajen ƙawayena, ko biki, ko wani shashancin dai daban, to da haka ta ya zamuyi aure Fahad?"

Ƙanƙance idanu yayi yana kallon ta yace" Abubuwan da kika faɗa, kamar kai tsaye kina so ki ce ba zaki iya aurena ba kenan?"

Da sauri ta girgiza kai tace" Me zai sa nace haka? Zan iya auren ka mana jariri, kai ma fa kasan kai kaɗai nake so, zan iya auren ka, amma idan ka min alƙawarin duk wannan matsalolin da na zayyano zamu kiyaye faruwar su, sannan zamu canza rayuwar mu canzawa kuma ta har abada."

Ajiyar zuciya Fahad ya sauke, a hankali ya ja baya kaɗan daga gare ta sannan ya zube guiwar shi ɗaya yana kallon ta yace" Nabila, ni Fahad na miki alƙawarin kiyaye duk wani abu da zai zama matsala a zaman aurenmu, sannan na yi alƙawari tsakanina da ubangijina kan na daina duk wani abun da nake yi daga yau, ba zan sake aikata wani abu da yayi kama da wanda na aikata a baya ba, in sha Allah."

Sai kuma ya tara mata hannu alamar ta taho tare da faÉ—in" Za ki iya aurena Nabila?"

Rufe bakin ta tayi da tafin hannu cike da farin ciki har da hawayen jin daɗi sannan ta miƙa msa hannun, jawo ta yayi ya zaunar da ita kan cinyar ta, haɗa goshin shi yayi da nata ya sake faɗin" Uhum?"

Cikin kukan farin ciki Nabila ta jinjina masa kai tare da faÉ—in" Na amince mana Fahad, na amince na sake sabuwar rayuwa da kai, sannan na ci gaba da rayuwa da kai har mutuwa ta riske ni."

Sai kuma ta kai bakin ta za ta haɗa bakin su, da sauri ya janye yace" O'o, yanzu fa kika sa na ɗauki alƙawari, ai ba zamu sake kusantar juna ba kuma har sai ranar da aka ɗaura mana aure."

Ɗan dukan shi tayi à ƙirji tare da yin murmushi ta sake haɗa goshin su tace" Ina son ka."
Chapter 77 · 0% Book details