← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 168

Sashe 10

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariyar da Hambali yayi mai nuni da jin daɗin lamarin yasa Emanuel ma darawa jin tsaran shi na kan daidai, cike da jin daɗi Hambali yace" Ema Ema, Shiyasa nake masifar son aiki da kai, Emanuel, idan wannan sabon tsarin namu ya tafi daidai ko? Na maka alƙawarin zan baka duk abinda ka tambaye ni."

Da fara'a Emanuel ya amsa da" Nagode yallaɓai, kenan na fara mata gwajin kayan mayen?"

Cike da tabbaci Hambali yace" E mana Ema, ka fara aikin kawai, idan komai ya tafi daidai sai ka kira ni. "

" Shikenan yallaɓai." Ya faɗa yana aje wayar tare da maka mata harara, dan wannan ne karo na farko a rayuwar aikinsa da Hambali da ya ji ya tsane shi har ma kamar ya kasheshi.

*GDN ALH KABIR*

Ummu na É—aki suka shigo, dan haka ya ma Jabir umarnin zama kan kujera ya ce da shi "Ina zuwa, bari na kira uwar gidan."

Jabir dai da ido kawai ya bishi, saida ya shiga wani ɗaki bayan ya ƙwanƙwasa sannan ya maida duban shi kan tsaruwar ɗakin da ƙayatuwar shi. Alhaji Kabir kuma na shiga ya samu Ummu na saka siket ɗin ta na kayan kanti, da sauri ta juyo da ladabi saboda ita idan ta kalli fuskar nan tashi sai ta ga ai wannan ya ma wuce uba a gareta sai dai Kaka, cikin nutsuwa tace masa "Sannu da zuwa."

Shi kuma baki har kunne cike da fara'a ya matsa daf da ita ya jawo ta jikin shi yace "Yawwa Ummuna, har kin tashi kenan?"

Jinjina masa kai tayi dan ita ko komawar ma bata yi yadda yake tunani, ɗan ƙoƙarin ƙwace kanta take daga jikin shi shi kuma ya fara lalubar zif ɗin dake bayan siket ɗin yana faɗin "Bari na taimaka miki mana amaryata."

Murmushin yaƙe kawai tayi ta sakar masa ragamar komai ɗin dan ba zata iya jayayya da shi ba, yana saka mata ya sake rumgumeta a jikin shi yana shaƙar ƙamshin turaren nan irin na Saudia a wuyan ta idanunshi a rufe yake faɗin" Ina ƙaunarki Ummuna, Allah ya miki albarka."

Ummu dake son fita daga jikin shi a É—arare ta amsa da" Ameen, nagode."

Raba jikin shi yayi da nata amma hannayen shi na riƙe da nata hannayen ya kalli fuskar ta da bata shafa komai ba sai zallar mai, amma yadda gashin ta mai sulɓi ya kwanto kan goshinta da kuma yadda girar ta tayi zar zar zar baƙi ƙirin yasa tayi kyau sosai, cikin nutsuwa yace mata "Ina da baƙo fa a waje, an kawo miki abinci ne?"

Saida ta fara jinjina msa kai alamar e sannan tace "E, an kawo É—azu."

Sai kuma ta sake tausa muryarta tace "Baƙo? Yanzu da safe?"

Murmushi yayi cike da zolaya yace "Uhum! Ko ba kya so wani baƙo ya zo ya ga tafiyar ki ta sauya dalilin daren j..."

Kunyar da ta kamata ne yasa ta saurin kai tafin hannun ta a bakin shi ta rufe masa tana sunkuyar da kanta duk ta shagwaɓe fuska alamar za ta yi kuka, dariya yayi tare da janye hannun nata yace" Shikenan to na daina."

Sai kuma ya gyara tsayuwarshi yace" Wallahi wani yaro ne na gani zaune ƙofar gida, to ina tambayar shi me yake yi anan sai kawai ya fara amai, na ɗauka bashi da lafiya ne, amma sai na kula aman na yunwa ne dan babu komai a cikin shi sai ruwa, kuma ya ce min tafiya zaiyi wai wani gari ko me ne ban dai fahimce shi da kyau ba, shine na ce ya zo cikin gida ya ci abinci sai na ji ina ya nufa, idan ma bashi da kuɗin mota ne sai a bashi ai."

Fuskarshi ta kafe da kallo, ƙwarai zai kai shekara 65 ko ma sama da haka, gemun da ya tara sai ka ce wani malami, ko da yake za ta iya kiran shi da malami, dan kwana uku da tayi gidan shi ta kula tsufan shi ya zo mishi da son addini matuƙa, dan daga bayan magrib zuwa isha'i ma ɗaukar karatu yake zuwa masallacin dake jikin gidan nashi wanda shi ya gina, kafatanin gashin kanshi da gemun duk yayi fari tass, duk da hakan ba dan tsufa bane wasu halitta ce haka. Tsantsar ƙaunar shi da jama'a da son taimakon su take hangowa a fuskar shi, ta tabbata hakan ma dalili ne da ya isa ya baka nagartaccen tsufa, bata taɓa jin wanda ya faɗeshi ba da alkairi ba a unguwar su da ma wajen ta, dan haka da ya zo da buƙatar auren ta ma bata bari mariƙanta sun hana masa ba saboda nagartar tasa.

Jinjina masa kai tayi tace "Shikenan, bari na saka hijab sai naje a zuba mishi."

Murmushi yayi na jin daɗin abinda ta faɗa, saboda matsalar rashin saka hijab din nan Atika ma da suka shekara ashirin har da ɗaya kullum fama yake da ita, amma saboda fifita sabgoginta sai ta ga ai wayewar kenan, tana siyar da kayayyaki na mata ta ya zata dinga fama da manyan hijab? Ko da yake ai ranar da ya ga Ummu har da niƙab ya gani tare da ita, Shiyasa ma ya tambaya wacece da ya ga ta shiga ɗaya daga cikin gidajen da yake ba wa marasa shi su zauna, da ya tabbatar budurwa ce kuma ya ce dole sai ita.

Tana saka hijab din tace masa "Muje?"

Kama hannun ta yayi suka nufi hanyar fita, jira take ta ga ya saki hannun ta idan suka kusa isa inda ya san ya aje baƙon nashi, amma sarautar Allah tsaf Alhaji Kabir ko na ce Baba😌 ya tamke hannunta har suka kai inda Jabir ke zaune ya na kallon taga da hasken rana ya fara ɓullowa. Ba Ta tabbatar ba zai saki hannunta ba saida yace da Jabir "Malam..."

Da sauri Jabir ya juyo yana amsawa da "Na'am."

Take idanunshi suka sauka cikin na Ummu da ita ta ƙara waro idanu da mamakin dama yaron Jabir ne? Mamakin hakan har ya sa ta faɗin "Jabir? Dama kai ne ?"

Da fari ƙurawa fuskar ta idanu yayi dake ta ƙyalli amarci, sai kuma ladabi da nutsuwa ya saka shi sauke dubanshi zuwa ƙasa sannan yace "Ina kwana aunty Ummu?"

Da mamaki Alhaji Kabir ya kalle su musamman ma Ummu yace "Kun san juna ne dama?"

Kallon Alhajin tayi da ladabi tace "E, É—an unguwar mu, ai gidan mu da nasu babu nisa."

Da matsanancin mamaki ya sake cewa "Haba? Kenan dai da gaske ne da ya ce ba almajiri bane? To kuma nan garin kake naji kana maganar kuÉ—in mota da tafiya?"

Da mamaki a fuskar ta ita ma ta kalli Jabir É—in tace "Tafiya? Ina zaka j kuma Jabir?"

A hankali ya sunkuyar da kan shi cikin ladabi yace "E, tafiya zanyi, Abbana ne..."

Sai kuma yayi shiru, hakan yasa Ummu fahimtar ba zai iya faÉ—a ba, kallon da Alhaji Kabir ke mata ya sa ita ma ta kalle shi sannan ta masa alama da idanu ya biyo ta a baya, ba jayayya ya bi bayan nata bayan ta kalli Jabir tace masa" Ina zuwa Jabir, bari a kawo maka abinci."

Suna shiga É—aki kafin tayi magana yace" Me yake faruwa wai? Me ya sa kika ce na zo?"

A tausashe ta kalle shi tace" Jabir yana cikin matsala ne."

Da kulawa yace" Wace irin matsala?"

Gyara tsayuwarta tayi tace" Yana zaune ne tare da matar Baban shi d..." Duka labarin Jabir ta bashi da irin matsalolin da yake fuskanta da yawan dukan shi da mahaifin na shi ke yi, girgiza kai yayi cike da rashin jin daÉ—i yace" Kuma kin tabbata shi ya haife shi?"

Da tabbaci tace" Shi ya haife shi mana, kawai dai matar sa tafi ƙarfin shi ga kuma zafin kai,dan na tabbata ba duka sojoji ne haka ba."

Girgiza kai yayi cike da rashin jin daÉ—i yace" Allah ya kyauta, amma wannan sam bai kyauta ba, ta ya zaka biya ta abinda mace take faÉ—a maka, sannan yau idan yaron nan ya lalace wa ya lalacewa? Ita tana da wata asara ne? Ita fa ko a jikin ta."

Sai kuma ya sake girgiza kai ya juya zai fita yana faÉ—in" Ki kawo masa abincin ya ci dan Allah."

"To." Ta faɗa suka fito tare ita ta nufi wajen teburin cin abinci shi kuma ya koma in da Jabir yake, sai dai yana isa wurin Jabir baya nan, babu shi babu alamar sa? Da sauri ya kama hanyar fita dan ya san yaron ya tafiyar sa ne, tun bai isa ga ƙofar ba yake ƙwala kiran sunan Ilya dake bakin ƙofar, amsawa yayi tare da ƙoƙarin shigowa, amma sai ya dakatar da shi da cewa "Yaron da muka shigo tare ina kaga ya nufa?"

Da ladabi yace "Yallaɓai ai yanzun nan ya fito ina ga bai yi nisa b..."

Kafin ya kammala yace "Maza kirawo min shi, kar ka bari ya tafi Ilya."

"To." Ya faÉ—a da gudu yana ficewa daga gidan, Jabir har ya fara nisa Ilya ya dawo da shi, ya so yi mas tirjiya dan sosai baya so ya sanar da kowa lbarinshi da kuma abinda yake shirin aikatawa, amma Ilya ya dage sai fa sun zo dan shi umarni Alhaji ya bashi, ba dan yana so ba ya biyo bayan Ilyan suka dawo gidan.

Suna samun Alhaji tsaye farfajiyar gidan ya taresu da faÉ—in "Jabir ya haka? Me ya sa ka tafi? Wani abu aka maka da baka ji daÉ—i ba?"

Girgiza kai yayi cike da kunya yace "A'a."

"To me yasa ka tafi?"

Yadda ya tsareshi da kallo yasa ya sadda kai, da idanu Alhaji Kabir ya ma Ilya ya tafi shi kuma ya sake kama hannun Jabir sukayi hanyar komawa ciki, Atika suka haÉ—e da ita za ta fita aikin ta cikin kyakyawan ado da mayafi a kafaÉ—ar ta.
Chapter 10 · 0% Book details