← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 168

Sashe 42

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai ta karkace a raunane ta ɗora da" To amm Hjia kaka ko ni ban san me ke damuna ba, kema haka baki taɓa sanin ina da fashi a cikina ba, sai shi kawai ya ce sai mun je asibiti, sai gashi dalilin zuwan nan har saida aka sake farkani, shin Hajia Kaka idan ban zarge shi ba me zan yi? Ko ya faɗa miki abinda aka ciro a cikin nawa ne? Ko kuma ni da ke ya nuna mana abinda aka ciro ɗin? A sanina ko ɓari mace tayi ana nuna mata abinda ya fito daga cikin nata dan tasan menene ko kuma a nuna ma wani nata, haka ma idan ciwo ne ana nunawa dan a ga menene, amma ni dai ban iya tuna an gwada mana ba."

Kallon Sa'ad Hajia Kaka tayi da tambayoyi fal a ranta, amma kafin ta ce wani abu Alhaji Ibrahim da kunya da nadama suka bakbaye shi ya kalli Sa'ad yace" Na sha gaya maka ka daina wannan banzar É—abi'ar taka, amma baka saurarata saboda ka raina ni, ga irin ta nan."

Aisha ya kalla ya É—an dafa kanta yace" Kiyi hakuri kinji Æ´ar rainon Hajia, zan iya kiran haÉ—uwar ki da Sa'ad a matsayin mummunar *RUBUTACCIYA*."

Matsawa yayi inda Aisha ta bishi da kallo tana ayyana _" Ya kuwa san yadda take ji akan Abbun ta?"_ Kusan Alhaji babba ya karasa sukayi magana da babu wanda ya ji, daga haka sukayi musabiha ya nufi hanyar shigewa ɓangaren shi, da kallo Sa'ad ya bishi kamar ya ƙwala ƙara koma duk ya fita ran shi, fata kawai yake a barshi da DG a wurin nan yayi ƙuli-ƙulin rakiya da shi a gidan nan. Da wani sabon makircin na son ganin ya kai Sa'ad ƙasa DG ya kalli Alhaji babba yace "Alhaji, ina ga da mun sa jam'i..."

Hannu Alhajin ya É—aga mishi fuska a gimtse, saida ya fara zura hannu ya jawo Aisha ya runguma ta jikin shi tare da sumbatar kan ta, sannan ya kalli mutanen wurin yace "Koma me ya faru mu alkairi ya mana, abinda kake faÉ—a kula zan sa a bincika min, idan da gaske ne zan bar hukuma tayi aikin ta, yanzu kuma zamu tafi da Eesha, dan dama ita ta kawo mu gidan."

Daga haka ya kalli Hajia Kaka yace "Mun barku lafiya."

Juyawa yayi da Eesha jikin shi da ta juyo tana kallon Sa'ad da ke bin ta da kallo kamar zai fashe da kuka, sai kuma ya sauke huce tare da kawar da kan shi, duk sallama suka ma Hajia Kaka da ita ma ta juya tana kasa amsawa tana jin dacin wannan rabuwa da suke yi da Aisha da bata taɓa zaton za su yi irin ta ba.

Sannu sannu sai idanun shi suka fara ƙyabtawa da sauri sauri kamar yadda idan ran shi ya ɓace yake yi, yana kallo duk suka juya suka dinga shiga mota har suka gama shiga tsaf amma DG na tsaye gaban shi, saida suka fara fita daga harabar gidan DG ya matso kusa da shi yana murmushi yace "Oga kenan, ya Kaga wasan? Shin ban faɗa maka ba dama sai na ƙwaceta daga gare ka?"

Sai kuma ya haɗe fuska yace "Karka ɗauka a nan aka zo ƙarshe, ka ci gaba da taka tsantsan, dan ba zan barka ba har sai na ga shari'a ta yi hukunci a kan ka, sannan kuma..."

Ya faɗa yana ɗan juyawa kaɗan sannan ya kalle shi yace "I zuwa yanzu na san kaa fahimci girman matsayin ta, kuma ko ban faɗa maka ba nasan kasan yanzu ta fi ƙarfin ka, Eesha Mukhtar Saheeb Ahlan, a yanzu dai ko tsilin gashin ta ba z aka iya taɓawa ba."

Da dai kam fuskar shi a haɗe take sosai yana kuma tafasa da jin ya kai mishi naushi, to amma a yanzu ban da wannan kuzarin saboda tafiya da kaso ma fi tsoka da Aisha tayi na daga cikin kuzarin na shi, dan haka ya ƙirƙiro murmushi mai ciwon gaske cike da ƙwarin guiwa Sa'ad yace "A ganin ka kenan, amma idan nayi niyya zan ga Eesha sanda nake so, kuma har na taɓa jikin ta a lokacin da nake so."

Wata dariya DG ya ɗauke da ita irin ta haukan nan kafin ya tsagaita yace "Eesha dai? Ka kuwa san a inda take rayuwa? Ka taɓa zuwa fadar Ahlan ka ga a inda suke tasu rayuwar...?"

Girgiza mishi kai yayi da dariya a fuskar shi yace "Kar ka ɗauka gidan su kamar irin naku ne, Sa'd idan ka shiga gidan su Eesha, za ka rantse da Allah baka taɓa shiga gida mai blocx na simitin ba, gida mai ƙofa biyu cike da jami'an tsaro, falo huɗu, jimillar ɗakuna ashirin da huɗu, fafaɗan tabkin ninƙaya, gidan gona ɗauke da mabambamta dabbobin da ake kiwo, ga kuma matsakaiciyar guardin mai fitar da kayan marmarin da kai sun isheka ka kafa kasuwanci, ma'aikata goma sha huɗu dake aikin kula da gidan, a haka, kake jin zaka iya ganin ta duk sanda ka so? Bayan tsaurara mataki da sukayi tunda suka rasa yaran su guda biyu."

Girgiza mishi kai yayi tare da kai hannu zai dafa kafaɗar shi, wani arnan kallo kawai ya mishi da ya saka DG fahimtar me yake nufi, sai kawai ya maƙale kafaɗa alamar oho tare da juyawa yace" Sai sun sake haɗuwa."

Kallon ƙeyar DG ɗin Sa'ad yayi ya ɗan fara takawa yana faɗin" Na san idan na faɗa maka zan zama *siriki* a wannan gidan ba zaka yarda ba, amma zan sa hakan ta yiwu har ka yarda ni Sa'ad zan zama *miji* ga wannan *ƴar*... In sha Allah, sannan daga ƙarshe, kai zan ce ka kula, daga yanzu zan fara buga lissafina a ciki naka ne, DG ba zan bari ka sha iska a doron duniyar nan ba har sai naga ka fara gudanar da sabuwar rayuwar ka a maƙargama."

Yana faɗa mishi haka kawai ya raɓashi a sukwane ya bar gidan gaba ɗaya ba tare da tunanin yaushe zai sake dawowa ba dan wacce ke daw da shi gidan kullum bata nan. Da kallo DG ya bishi yana mamakin kalaman shi, sai kuma ya taɓe baki ya kalli wayar da Aisha ta jefawa Sa'ad din, sai kawai ya juya shi ma ya bar gidan yana tunanin Sa'ad bai da lafiya da yake tunanin zai auri Aisha bayan duk abinda ya faru.
*Tun* daga lokacin Aisha ta fara cin karo da abubuwan mamaki daga gurin Ahalin nata, yadda kowanen su ke ta kira yana sanar da ƴan uwa da abokan arziƙi an ga Eesha, da kuma jin yadda suke amsa addu'a da ameen Ya matuƙar bata mamaki, sai Hajia Kaka da ta ji na waya tana amsawa da _"In sha Allah, ita ma bamu cire rai da ganin ta ba a ko yaushe, yadda muka ga Eesha a kusa da mu, muna fata zamu ga Kuwailat haka."_ Ta shiga tunani da tambayar kanta to me ya sa aka raba su da iyayen su? Shin wanda yake ɗauke su ba ya da imani ne? Bai taɓa haihuwa bane? Me iyayen ta suka masa da zafi haka? Da hukuncin su dole ya zama raba su da ƴaƴan su ne har guda biyu? Shiyasa yanzu da suka ganta suke ta naniƙeta a jikin su musamman ma mahaifiyar ta da ƙyar ta yarda ta koma jikin Hajia. *Duk* da za ta iya cewa da ɗan wannan haɗuwar ta mintuna, da kallo ɗaya kuma ta ɗan fahimci kamar akwai wanda basa son lamarin ta, wato kowa ya rumgume ta a jikin shi har da sumbatar ta hatta da kawun ta Sabeer, amma sam ban da matan nan guda biyu da suke binta da ido kawai, sai wacce aka ce ita ce matar farko ga Yayan mahaifin ta (Fa'iza) kawai dake mata murmushi ta ɗan shafi kan ta kaɗan.

Ta taɓa shiga jirgi, dan a cikin shi ta zo wannan ƙasar, amma bata taɓa ganin jirgi mai zaman keɓantattun mutane ba sai yanzu da suke sararin samaniya zuwa na su garin wanda ma fi aksari mota ake hawa, daidai wannan lokacin ne iskan da take shaƙa da jin ta a duniyar gajimare ya bata damar tuno da Abbun ta da ta baro a can, me ya sa yayi haka? Me yasa ya ɓoye mata abubuwa dayawa? Kenan bai da niyyar sadata da danginta? Kenan so yayi ya siyar da ita? Ko ma ya kashe banza ba mai tayar da maganar? Me yasa? Me yasa? " *Me yasa Abbu?*" Har saida maganar zuci da take ta fito fili duk na kusa da ita suka jime ta ce, da sauri Mama Nur ta dafata cike da kulawa tace "Eesha? Lafiya? Me yake damunki?"

Sororo ta kalle ta, sai kawai ta girgiza kai tayi murmushin yaƙe tace "Ba komai... *Mamie*."

Murmushi Mama Nur tayi ta ƙara riƙe hannun Aisha gam har saida Aisha ta kalle ta sai kawai tayi murmushi ita ma ta sake maida duban ta ga taga.
Cikin ƙanƙanin lokacin da bai zarta awa da rabi ba suka isa gidan su bayan tarbar su da aka yi, anan Aisha ta sake kallon ikon Allah tana kuma gode mishi, ashe anan aka haifeta, anan tayi watanni shida da haihuwa, amma rashin imani da tsoron Allah ya sa aka ɗauketa ta rayu a inda take kwana a gadon ƙarfe mai yaloluwar katifa, ta rayu a wurin da kullum suna cin abinci ne dan maganin yunwa ba dan daɗi ba. Maganar da Abbu Mukhtar yake so yayi da Fa'iza ta sa ya kalli mai aikin su da duk suke nan dan taya su murnar ganin Aisha yace mata "Mama *Laura*, dan Allah ki tafi da Eesha ki nuna mata ɗakin ta, tayi wanka ta yi sallah kafin anjima."

Da girmamawa dattijuwar ta amsa da "To yallaɓai..." Take kuma ta kalli Eesha tace "Muje *Hajia ƙarama*."

Wani kallo Abida ta ma mai aiki, sai ta ji zuciyar ta ta sake yin zafi kamar za ta ƙone, amma sai ta dake kawai ta yi murmushi, Aisha dake riƙe da hannun ƙanin nata Kabil tare suka tafi yana mata hira tana amsawa, burin shi dai ta je ɗkin shi ya nuna mata kayan wasan shi.
Chapter 42 · 0% Book details