← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 168

Sashe 124

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda ya hange ta dama yake ta murmushi yana sake ƙare maya kallo, tun rannan dama bai ga wata makusa ba duk da da hijabi ya gan ta , da aka faɗa masa bazawara ce sai ya ji shi fa ya samu kalar matar da yake so, fara kuma doguwa sannan kyakyawa, zahiri kuma ya nuna tana da nutsuwa da hankali sosai. Ummu na ƙarasowa tayi sallama ya amsa a mutumce shima yana gyara tsayuwar sa, gaisawa sukayi sosai da girmamawa kamar sun san juna, kafin daga bisani ya sake gyara tsayuwar sa ya faɗa mata abinda ya kawo shi tare da buƙatar jin ta bakin ta.

Ummu da kanta ke ƙasa, wani irin yanayi ne take ji, bata taɓa tunanin akwai ranar da zata risketa bayan Alhaji Kabir zata iya tsayuwa da wani namiji haka ba bayan ba dwan uwan ta ba, kai gaskiya Alhaji Kbir ya cuce ta, gashi kuma basu haɗu sosai ba bare ta masa ɗanyan kan da ta saba.

Ba tare da ta ɗago kai ba cikin wannn nutsatsiyar muryar ta ta tace "Ban san me zn ce ba, wannan yanayin, wannan rayuwar, komai sabo ne a gare ni, amma kayi haƙuri idan ba haka ya kama na faɗa ba."

Murmushi Alhaji Haris yayi yace "Ba damuwa gimbiya, ai girman ki ne hakan ma idan kikayi, ko shiru kika min ai ni nayi nasara tunda na samu ganin ki ma, bare kuma na ji muryar ki, sai dai zan so a zauna ayi tunani game da lamarina, sai a bani lokacin da zan sake dawowa dan naji amsar da gimbiyar tawa ta yanke."

A hankali Ummu ta saci kallon shi, a sakanni ta gane dattijo ne da bai kai tsaran Alhaji Kabir ba, hasalima wannan bai wuce tsaran su Mama ko dai shekara hamsin haka, shirun da tayi ba ta amsa mishi ba yasa shi cexa" Sai dai kuma na manta da wani abu, ban faÉ—a miki ina da mata biyu ba da kuma yara takwas."

Numfashi ta sauke tana sunkuyar da kai tace" Ma sha Allah, Allah ya sanya maka albarka a cikin iyalin ka, sai dai nima ya a shari'ance ya kamata kasan nima me ya fito da ni daga gidan tsohon mijina, sannan ina da Æ´a mai kusan shekara sha uku zuwa sha huÉ—u."

Murmushi yayi yace" Ba ki da matsala, idan na sake dawowa ma tattauna sosai akan haka."

A hankali ta jinjina kai alamar to, dan haka ya tamabaya to yaushe zai dawo? A taƙaice ta bashi amsa da" Zuwa jibi ma."

Da haka sukayi sallama, ta kuma yi sa'a yana shirin tafiya Yaya Luƙman ya zo, saida suka gaisa sannan ya tafi, to shi yake sanar da ita mutumin kirki ne shi dai a sanin shi, amma zai yi bincike a kan shi dan su san wanene shi sosai.

Ummu sun ci gaba da shirye shiryen su, inda shirye shiryen ke tafiya da kyau, kuma duk abinda ke faruwa anan a can ahalin Ahlan suna sane, haka suma suna sanin labarin nasu shirye shiryen a wajen Ummu, hatta da Fahad da ke shirin tasowa dan ya zo a yi É—aurin aure da shi. Wani abu da Ummu ba ta sani ba shine abotar da ta haÉ—u tsakanin Jabir da Fahad sanadin Hajia, kusan ma za'a iya cewa Jabir ne babban abokin Fahad wanda ke ta zirga zirgan tarban Fahad da abokanan shi da zasu taho, gidan su yayi niyyar sauke su madadin kama wani masauki, hakan ya sa duk da babban biki ne amma labaran komai ke yaduwa tsakakkanin su tamkar dukansu ahali guda ne.

Furuncin da Yaya Luƙman yayi cewa Alhaji Haris mutumin kirki ne ya sa da wa'adin da zai dawo ya cika Ummu har tayi shirin tarban sa cikin doguwar rigar abaya da ta fito da ita tamkar balarabiya, a farfajiyar gida suka zauna ta tarbe shi da abun sha, iya haka ma kawai ya nuna masa ta amince da shi kenan, sai dai Ummu ba wai ta amincr bane kai tsaye, za ta so su ɗan fahimci junan su ta gane wane mutum ne shi? Kafin za ta yarda har maganar aure ta shiga tsakanin su. Sun ɗan jima suna hira wannan karan kafin ya gaisa da su Mama, daga nan sukayi sallama bayan ta faɗa masa za dai suyi waya, amma ba za ta ganu ba gaskiya saboda hidimar bikin ƙanwar ta.

*Ranar Alhamis*

Duk da Ummu ta ga dangin Mama da na Abba sun fara cika gidan saboda bikin Nabila, har ranta ba ta ji komai ba bare ran ta ya ɓace wai dan basu zo a bikin ta ba.

Saboda cikar gidan da hayaniya ya sa ta shiga maƙotan su aka mata kitso da lalle, ana idawa daf da la'asar ta shiga girkin da Kawun nata Fahad ya buƙaci da tayi dan tarban baƙin shi daa zasu zo tare, suna hanya ya ce zuwa magriba suna shigowa in sha Allah, dan haka a nutse ta shiga sarrafa girki kala kala da taimakon wanda take aikin a gidan su dake akwai ƴan mata.

Kai da kawowa Ummu ke yi kasancexar Nabika ba ta da wata ƙawa sai Naja'atu, sai wanda kawai yanzu ne ta yi su saboda bikin, amma duk ƙawayen nata ta raba hanya da su wasu kuma sunyi aure.

Ana kiran sallah ta kammala komai ta killace shi, a lokacin suke waya da Fahad ya shaida mata sun shigo lafiya kuma zuwa bayan sallah isha'i zasu zo su gaishe da Mama da kuma amaryar shi da yake son gani, a haka sukayi sallama ana idar da kiran sallah ta shiga wanka.

*Ƙwarai* Ummu tayi mamaki da Alhaji Haris ya kirata ya ce gashi a ƙofar gidan su ta zo zai bata saƙo, ba ta ji daɗi ba dan ta ga ai jiya ma ya zo, kuma ita a tsarin ta fa ba wannan shirmen da sunan hirar soyayya, ta fito ne da niyyar faɗa masa gaskiya bata son irin wannan bazatar, gashi ya katse mata falon Mama da take ma turare saboda zuwan su Fahad tunda ai anyi sallah isha'i tasan yanzu zasu zo, hankalin shi na ga waya sai ƙamshin sanyayyan humrar ta ne ya sanar da shi ta iso,dan haka ya juyo yana aje wayar tare da yin murmushi yace "Gimbiyata, barka da fitowa?"

Ba tare da tayi murmushi ba ta amsa da "Ina wuni? Nayi mamaki da ka ce kana nan."

Da murmushi ya amsa da "Dole ne, tunda ban sanar dake zuwana ba, amma a gafarce ni, nasan na shiga lokacin ki, dan da alama hidima kike sosai."

Gyara tsayuwa tayi tace "Gaskiya kam, d..." Abinda tayi niyyar faÉ—a ta haÉ—e saboda saurin da yayi ya buÉ—e bayan mota yana faÉ—in "Dama wai tqwa gudumuwar bikin na kawo, na so na turo yaro, na ce dai bari na kawo da kaina."

Ajiyar zuciya ta sauke, it dai kam da yasan hakane gaskiya da ya turo É—in ya fi, saida ya buÉ—e motar gaba É—aya sannan ya É—an juya dama da haunin shi, cikin sa'a ya hangi wasu matasa na zaune, kiran su yayi suna zuwa ya umarce su da su ciro kayan, Ummu na tsaye tana kallo ta ga kowane matashi ya wuce da buhun shinkafa cikin gidan su, ta É—auka shikenan bayan buhu ukun, amma sai ta ga an É—auki jarkar mai da kwalin maggi da wasu ledoji da bata san me ye a ciki ba, saida yaran suka gama ya sallame su suna ta farin ciki sannan ya dawo wajen Ummu yace "To gimbiya, ni zan wuce na bar ki kuci gaba da hidima, sai munyi waya ko?"

Da mamaki Ummu tace "Amma Alhaji, naga kayan kamar sunyi yawa, ai da baka wahalar da kan ka ba haka."

Murmushi yayi yana kallon fuskar ta da yau ma dai babu kwalliya ko ɗis, kafin ya ce wani abu *motar Jabir* ta danno kai layin ɗauke da Fahad a gaba sai wasu zaratan matasan a baya su huɗu, tun yana son ya gano wacece a ƙofar gidan har saida dai jikin shi ya tabbatar masa wacce dai yake tunanin ce, a ƙuntace, a illance, a rikirkice ya ƙaraso da motar ran shi na mugun ɓacewa.

Yadda ya faka motar daf da Ummu yasa ta ja baya tana kallon motar tare da yin tsaki sannan ta ɗauke kan ta ta mayar kan Alhaji, murmushi tayi tace "To shikenan, nagode, idan na shiga zan sanar wa da Mama, nasan zata buƙaci yi maka godiya, sai na haɗaku a waya in sha Allah."

Shima da fara'ar yace "Ba sai kinyi haka ba gimbiyata, Nabila ai ƙanwar mu ce duka, dan na yi wannan a hidimar ta bana jin wani abu nayi na arziƙi."

A haukace, a mugun zafafe Jabir da ya ga wani kallo da ta ma motar sannan ta watsar har saida ya ga kamar bakin ta yayi tsaki, sannan ta kalli wannan garjejen Alhajin tayi murmushi, murmushi fa Maama ke yi gaban wani ba Abba ba, har adon haƙoran ta (haƙorin makka) ya fito yana kallo, me yasa Maama ke yin haka wai? Saboda Allaj wannan wace irin rayuwa ce take son saka kanta a ciki?

Kasa É—auke idannunshi yayi a kanta, duba ne yake yi mata irin wanda yake fatan ta gane me yake nufi ta nufi gida a mutumce ba tare da ta saka shi ya raba wani abin faÉ—a ba da ita salon a ce bai da kunya, amma yarinyar nan da ita da tarin taurin kunnenta sai ta sake juyawa wajen mutumin da yake iya kiransa da Baba shi ma dan a haifen dai zai iya haihuwarsa domin shi bai ga wani bambanci tsakaninsa da Abban shi ba tana murmushi kamar wata wacce ke neman fitina. "Jabir, motar a kulle take." Fahad ya faÉ—a yana duban jabir É—in shi ma ya kai dubansa wajen da jabir É—in ya zubawa idanu.

Buɗe motar yayi suka fita, amma shi ya kasa ciro ƙafarsa bare har ya iya fitowa daga cikin motar, Fahad na ƙoƙarin sake yin magana Jabir yace"Ku je Fahad ina zuwa."
Chapter 124 · 0% Book details