Sashe 23
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga can ɓangaren aka ce "Yallaɓai anan ne Zinder, mun kama su ne a mota suna tuƙin ganganci, kuma Yallaɓai babu takarda ko ɗaya tare da su, hasalima shi Fahad da ke tuƙin shekarun shi basu cika sha takwas ba, da aka dakatar da su kuma sai suka nemi yin rashin kunya ga jami'anmu, Shiyasa suka kawo su nan."
Shiru yayi, tunanin abubuwa da dama yake a lokacin, Fahad dai, Fahad dai, kullum Fahad, ba shi ya fara haihuwa ba, amma dake shine auta a gidan sai yake neman ya zamar musu dodo, Allah ma shaida ne basu mishi rainon da za' a ce laifin su bane, tunda ba akan shi suka ɗanɗani daɗin haihuwa ba, kasancewar shi auta bai sa suka masa sako-sakon da za'a ce matsalar daga su bane, yara shida suka haifa kafin shi na bakwai, Bilal ma dake babba bai wahalar da su ba, suka zo kan *Murjanatu* mai sunan mahaifiyar shi, lokacin da Mukhtar ya zo duniya kuma Bilal ya ƙara sanin ciwon kan shi, dan haka da taimakon shi ma suka raine shi, har zuwa kan su *Marfu'a* da *Sabeer* kafin shi Fahad ɗin. Saida ya ɗan sosa gaban goshin shi kafin ya feso zazzafar iska daga bakin shi yace "Shikenan, zan wakilta wanda zai je kuyi sulhu da shi, kasancewar ba gari ɗaya muke ba, hasalima ba mu san ya tafi can ɗin ba."
Hankali Hajia Radiya ne ya sake tashi har ta matso daga zaman da tayi cikin kujerar tana ta kallon shi, tana ganin ya aje wayar tace" Alhaji lafiya? Wai abu ne ya samu Fahad É—in ? Yana ina ne?"
Kallon ta yayi irin kallon shirun nan kamar mai nazarin abinda zai faɗa mata, miƙewa a hankali ya na lalubo ɗaya babbar wayar tashi daga aljihu, da sauri ita ma ta miƙe tsaye tana matsowa kusan shi da sake tambayar" Alhaji, wai me yake faruwa ne? Me ya samu Fahad ne?"
Ba tare da ya kalle ta ba yana neman lambar manajan shi dake kula da gidajen man shi dake garin yace" Me kuwa zai same shi, yana lafiya."
Da zumuÉ—i tana gyara gilashin ta tace" Amma ai naji akan shi ake magana, har da maganar sulhu da Zinder... Dan Allah sanar dani me yake faruwa?"
Ɗan ɗaga idanun shi yayi ya kalle ta tare da kai wayar a kunnen shi saboda ƙara da ta fara yi alamar kiran na shiga yana cewa" Yana Zinder, wai an kama su suna tuƙi, yaushe ma Fahad ya koyi tuƙin mota ne ban sani ba? Ko ke kin sani?"
Da tsananin mamaki ta zaro idanun ta da a zahiri basu da wata matsala face fara dakushewar ganinta har sai ta saka tabarau tace" Tuƙi? Mota? Fahad ɗin?"
Wayar da aka É—aga tashi yasa shi É—an takawa zai bar falon yana faÉ—in" Ki kwantar da hankalin ki, idan ya dawo gidan zamu yi magana da shi."
Da kallo ta bishi har ya fice, sai kuma ta dafe goshin ta tana sauke ajiyar zuciya tace" Yaushe ya koyi tuƙi ban sani ba?"
Rashin mai bata amsa ya sa ta kallon Kabil da ya É—auko tamolan shi daga waje ya rumgumota ya shigo falon, kama hannun shi tayi tace" Muje ayi wanka ka canza kaya ka kwanta, yau dai zaka kwana anan ko?"
ÆŠaga kai yayi ya kalle ta yace" Abbu fa?"
Da fara'ar da ta ƙaƙarota ne kawai ta amsa mishi da" Abbun ka ai baya gari, amma ya yi alƙawarin zai dawo gobe, sai ka kwana tare da shi." Jinjina kai yayi alamar gamsuwa har suka shiga ɗakin nata.
*Alhamdulillah.*
29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
*RUBUTACCIYA*
👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
_NA_
*SAMIRA HAROUNA*
_SADAUKARWA GA_
*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_
_Bismillahir- rahamanir-rahim._
*11*
Rintse idanunta ta ƙara yi saboda raɗaɗin ciwon kan da ta ji ya fara ziyartar ta tun bata buɗa idanunta, sai kuma jikin ta da shi ma ta ji ya kwashi na shi ciwon sakamakon faɗuwar da ta yi a ƙasa sosai sa'ilin da komai na jikin ta ya daina aiki, sannu sannu ta dinga yatsina fuskar ta tana ƙoƙarin buɗa idanunta, buɗewar farko dishi-dishi ta gani, sai da ta ƙara rufe su ta buɗe kafin ta ga Mardiyya zaune kusa da ita tayi taguma tana kallon wayar ta. Saida ta fara motsa bakin ta sannan ta ɗaga laɓɓanta da ƙyar ta furta "Aunty..."
Da sauri Mardiyya ta juyo ta kalle ta, sai kuma ta aje wayar ta akan cinyoyinta ta riƙo hannun ta tana faɗin "Nuriyya, kin farka? Sannu, ya jikin naki?"
Cikin lullumshe idanu da buɗa baki da ƙyar haɗe da yamutsa fuska tace "Aunty..., me ya faru ne?"
Girgiza kai Mardiyya ta fara yi sannan tace "Nuriyya, ke zamu tambaya ai, me ya sumar dake a madafa?"
Ƙara yatsina fuska tayi tana kallon Mardiyyar cike da son tuna abinda ya faru da ita ɗin, a nutse ƙwaƙwalwar ta ta fara taro mata abinda ya wuce wasu awanni baya. *Tabbas* tana madafa tana gyara kayan cincincin wanda yanzu shi ta fi son ci dan bata sha'awar komai, a faffaɗar tvn dake madafar can saman bango kawai ta ji waƙar da ko a mafarki ta ji ta tasan ta me ce ce, tana ɗaga kanta zuwa ga tvn ta ga hotunan da aka ɗauka taron sunan Eesha, hakan ne ya saka ta jin wannan yanayin da aka tabbatar mata wai hawan jini ne da ita tunda take jin wannan alamun, gashi ta kafe idanunta akan tvn tana kallon hotuna bila adadi da aka ɗauki Eeshar har zuwa sanda ta fara wayo. Bata san idanunta na fito da ruwa ba saida ta ji lema a hannun ta, sam ba ta yi tunanin ya aka yi tvn ta kunnu ita ɗaya ba, ganin hoton yarinyar na ƙarshe tana ɗauke da ita da kuma kayan da aka karɓe yarinyar daga hannun ta da ita yasa aikin komai dake jikin ta sake ninkuwa har saida ta ji idanunta sun rufe sannan jiri ya ɗebe ta zuwa baya... Daga shi bata sake sanin komai da ya faru ba sai yanzu.
Yunƙurawa tayi za ta tashi zaune da sauri Mardiyya ta miƙe ta kamata har ta zauna tana faman jera mata sannu, cikin kulawa tace da ita "Na kawo miki ruwa ne?"
A hankali ta jinjina kai alamar e, da sauri ta miƙe gefen gadon ta ɗauki jug ɗin ta kwalba ta tsiyaya mata ruwan a kofin tangaran, kusanta ta zauna ta miƙo mata sannan ta zuba mata idanu tana shan ruwan, saida ta sha ta miƙo mata kofin, karɓa tayi ta aje sannan ta sake duban ta tace "Abinci fa?"
Yatsina fuska tayi tana lumshe idanu, sai kuma ta kalle ta da kyau cikin sanyayyar muryar dake É—an disashe kamar mai mura tace "Aunty, Æ´aÆ´ana, Æ´aÆ´ana aunty, suna ina? Ya suke yanzu? Wa ya... Wa ya *É—auke min* yarana ? Aunty wa ye yake son ganin bayana? Me nai masa?"
Cike da tausayawa Mardiyya ta matso kusan ta tare da jawo kanta ta kwantar a kafaɗar ta tana shafa bayan ta cike da rarrashi tana cewa" Ya isa haka Nuriyya, kiyi haƙuri kin ji, in sha Allah ina tabbatar miki wata rana zaki ga yaran ki, kuma da izinin Allah a duk inda suke yanzu suna cikin kyakyawan yanayi, wataƙila ma..."
Ta faɗa tare da ɗago kanta ta tallabo haɓarta tana murmushi duk dan ta kwantar mata da hankali tace" Wataƙila ma *Kuwailat* ɗin ki tayi aure."
Murmushi ta saki duk da cikin kuka take, cikin rikicewa da tashin hankali da rashin madafa ta shiga nuna ƙirjinta tana faɗin" Da gaske aunty? Idan hakane da nayi farin ciki marar misaltuwa, amma ni wannan shirun ko? Ɗaga min hankali yake aunty, ni a ƙalla ma wanda ya ɗauke su ya faɗa min halin da suke ciki, a inda suke ba sa fuskantar kowace irin tsangwama? Sai hankalina ya kwanta, amma..."
Sai kum t sake ɓarkewa da kuka mai cin rai tana faɗin" Aunty idan ƴaƴana fa suna fama da yunwa, da matsin rayuwa, da takura, da rashin gata? Bayan kuma su ɗin jikokin Saheeb ahlan ne, mutumin da ba iya gwanatinmu ba, sauran gwamnatoci ma suna karɓan bashi a hannun sa, shi da kansa bai san iya adadin abinda ya mallaka ba, sannan kuma jikoki ne ga Abdus-salam Asgar, tsohon malamin makarantan da ya taka muƙamai da dama har yanzu da yake ambasader na Paris, aunty ba zamu yafe ma kanmu ba idan yaran nan suka kwana da yunwa ko sau ɗaya, ba zamu yafe ma kanmu ba, kin san ko?"
Cike da tausayin halin da ƴar uwar ta ta take ciki ta sake kwantar da ita a jikin ta tana goge ta ta ƙwallar cike da dauriya tace" Yi haƙuri ƙanwata, kiyi haƙuri kin ji? Wannan ita ce *RUBUTACCIYAR KI*, ka da ki gaza cinye ta kin ji? Kiyi haƙuri kin ji, in Allah ya yarda yaran ki na hannu na gari."
Yadda take rera kukan yasa dole Mardiyya ma fashewa da kuka, wanda hakan ma dalili ne da ya sa bata son zuwa in da Nuriyya take kullum, ya za ta yi? Su biyu kaɗai iyayen su suka mallaka a duniya, ba su nemi komai a duniya sun rasa ba, duk abinda suke so shi ake musu, ko ita dake auren wanda ake ganin bai dace da ita ba wato Alka, ita ce ta zaɓi abun ta a haka duk da Tsoho ne kuma mai mata, amma iyayen ta basu hana ta ba suka barta ta aure shi, ita kanta Nuriyya auren soyayya ta yi da Mukhtar, yarinya kyakyawa fara tas da ita, amma rayuwa da yanayin da take ciki ya sa duk ta rame wcce a da kuma jikin ƙiba gare ta.
Ba tare da ta daina shafa bayan ta tace "Ki daina kuka kinji, ki ci gaba da yi musu addu'a, in sha Allah za ki ga yaran ki..."
Duk da ta kai ƙarshe amma da sauri ta ɗago tace "Yaushe? Yaushe aunty?"
Da rarraba idnu Mardiyya tace "Wata rana, in sha Allah nan kusa kaÉ—an, ina ji a jikina kin kusa haÉ—uwa da su dukansu."
Kawar da kai tayi kaÉ—an tana zubo da wasu hawayen tace "Aunty, ko dai na fara haukacewa?"