← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 130 OF 168

Sashe 130

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Kwana* tara kenan yau da tarewar Nabila, kuma yau Alhaji Abbas ya zo da maganar Larwan gidan, yadda Ummu ta ga duka iyayen suke ta farin ciki da lamarin sannan ita kan ta ta ga bata da wani dalili na ƙin shi, ɗan uwan ta ne, sannan yana da mata, kula shekarun shi sun haura nata, yana da ilimi da wayewa ga kuma kyau da tsari, to me ya rage mata ita kam, sai kawai ita ma tayi amanna da shi tare da ƙara watsar da maganar Jibril wanda dama ko da ya kira ta sake faɗa masa yayi haƙuri fa, sai dai baiyi haƙurin ba yana kiran ta, idan ta ɗga zasu gaisa ya sake jadadda mata ƙudurin shi, gane hakan ya sa ma ta daina ɗaga kiran, sai dai saƙo a ƙalla yana turo mata goma ko sama da haka a wuni, tun bata kulawa har kalaman nashi ke ɗan so su kama hankalin ta. To ama da ta haɗu da Larwan da take ma laƙabi da *Yayana*, wanda komai yana yin sa ne kai tsaye musamman ma da yake ganin zai samu kulawar da ya rasa a wajen matar sa daga Ummun, hakan yasa shi kan shi yake zaƙewa wajen nuna mata kulawa da soyayyar sa.

Tana kwance kan gado da wayar ta tana shan soyayyar ta da Yayan ta sai faman dariya take, muryar Mamie Nuriyya ce ta daki kunnuwan ta tana ƙwala mata kira da sunan da suka saba wato aunty, da sauri ta tashi zaune tana amsawa da "Na'am aunty."

Sannan ta miƙe ba tare da ta ɗauki ɗan kwali ba saboda ta ɗauka Maman ta ce kawai a wurin, tana zuwa ta samu har da Abbun ta yana mata faɗan "Shikenan haka zaku zauna ke kice aunty ita ta ce aunty? Wa ye auntyn a ciki to? Kaga sakarcin banza."

Turo baki Mamie tayi tace "To dan Allah ba Æ´ar farita bace? So kake na dinga kiran sunan ta gatsau ? Bayan manyanmu sun hana mu kuma."

Ummu na dariya ta ƙaraso tace "Aunty gani."

Kallonta Abbu yayi a tausashe yace "Haba mana babyta, faÉ—an da nake yi fa kenan."

Dariya tayi tace "Ayi haƙuri Abbu, in sha Allah zamu daina."

Kallon ta Mamie tayi tace "Kin sauke min ruwan magarya na?"

ÆŠaga gira Ummu tayi tace "Tun tuni aunty, na san la ya huce."

Kallon su Abbu yayi sai kawai ya girgiza kai yace "Allah ya shirya ku."

Da dariya kuma a tare suka amsa da "Ameen." Kallon Ummu yayi yace "Baby, Larwan ya same ni akan yana so ya turo a yi maganar auren ku, nace ya bari sai na shawarce ki tukuna, ya kika ce?"

Turo baki Ummu tayi cike da shagwaɓa ta faɗo jikin Mamie tana rufe fuskar ta tana faɗin "Ni wallahi Abbu ka daina min haka."

Dariya duk sukayi, sai Mamie da ta kalle shi tace "Ta fa amince, ai kawai ka ce ya turo, auntyna fa kullum mafarki take yi, gwara na gaggauta miƙata ɗakin mijin ta."

Sai kuwa Ummu ta fashe da kukan shagwaɓa tana kallon Abbu tace "Abbu ka gani ko? Wallahi aunty bata so muna zaman lafiya yanzu, sai ta dinga tsokanata dan kawai na koma wajen Hajia."

Zura hannun shi yayi ya kamo na Ummu ya taso da ita yana faÉ—in "Kinsan ai daina son ki tayi saboda ina tunanin laulayi ta fara, gani take zata sake samun wasu yaran, amma zo nan baby ki faÉ—a min a kunne na ji."

Zaune tayi kusan shi tana wasa da hannun shi kanta ƙasa, sunkuyo kanshi yayi yace "To ya? Kin amince ɗin?"

Shiru ta sake yi ba ta ce komai ba, hakan yasa shi shafa kwantaccen kan ta yana faɗin "Ma sha Allah baby, shirun ki ma magana ce, Allah ya miki albarka kin ji, sannan na miki alƙawarin damƙa miki wasu muhimman abubuwa da suke naki ne a ranar da aka ɗaura auren ki."

Miƙewa Ummu tayi irin da sauri tana fadin "Ni wallahi Abbu kunya kuke bani."

Da kallo suka bita inda Malie ke faÉ—in "Allah aunty ranar auren ki sai na kwaso shoki."

Da sauri Abbu ya kalle ta yace "A ina? Ba dai a gidan nan ba."

Saida ta masa fari da idanu sannan tace "A nan kuwa, za ka gani kuma."

Kallon Ummu yayi dake daf da shiga ɗaki yace "Auntyn ta Mamie (Hajia) fa na kiran ki a ɓangaren ta."

Da ladabi ta amsa da "To Abbu." Ta ƙarasa shiga ɗakin da niyyar ɗauko hijabin ta ta saka sannan ta nufi wqjen Hajiar. A can ta tarar da Nabila da aunty Fa'iza suna ta lissafin abubuwan da za'a yi na sadaka saboda Hajia na daf da fita wanka, tunda ta shigo Hajia ta harare ta tace" Sai da na neme ki ko? Ke wallahi ba dan kama da kike da ni ba da nayi hushi da ke."

Gwalo Ummu ta mata tace" Gashi kuma na zama ƙarfen ƙafa."

Zaunawa tayi kusan Nabila dake rubuta abubuwan da Fa'iza ke lissafawa tace" Me kuke yi hakane?"

Harara Hajia ta sake wanka mata tace" Aiken ki zanyi ni malama."

Numfashi Ummu ta sauke tace" Ina kuma?"

Gefen ta ta ɗauki jaka ta buɗe ta ciro abinda Ummu na gani ta tabbatar tikitin Hajd ne ko umara ta miƙo mata, tana buɗewa har da passeport na Mama ne da aunty Kubra da Mama Jamila har da Iya da malam Adam, a taƙaice dai Mama da ahalin ta da malam Adam, cikin farin ciki Hajia tace "Mun so haɗuwa da mahaifin Nabila sanda yake da rai, sai dai ubangiji bai yarda hakan ya kasance ba, shiyasa ni da iyayen ki muka tattauna muka ga idan babu shi ai akwai ahalin shi, shiyasa mukayi wannan."

Duk da Alhaji Kabir ya kai Mama aikin hadj haka ma Yaya Luƙman yasa tayi umra, amma bai hana Nabila da Ummu rumgume juna ba suna murna da farin ciki, suna cikin wannan farin ciki Hajia tace" To kune zaku mata abishir ɗin sabon gidan ta? Ko kuma ita ce zata muku?"

Nan ma sake ruɗewa sukayi sai Nabila data sunkuya ƙasa tana ma Hajia godiya, tallaba ta Hajia tayi tana faɗin ba komai, ita ta musu alkairi ai kuma har yanzu basu biya ta ba. Ummu nata sharar ƙwallan farin ciki da hasaso yadda Mama zatayi Hajia tace" Ke, daina kukan nan je ki shirya zaku tafi kasuwa ke da Nabila."

Da mamaki Ummu tace" Amaryar ce zaki fara aika kasuwa?"

Kallon ta Hajia tayi tace" To amarya ba'a aiken ta? Kuma ni ba aikena za ta je ba, sautu dai zan baku idan kuka tafi tare, ama Nabila yanzu ai Æ´ar garin ce, sati kusan biyar yanzu."

Turo baki Ummu tayi tace" Ke dai tsohuwar nan, to bari na je, kuma kisa dreba ya kaimu, dan ba zan yi tuƙi ba."

Uffan Hajia ba ta ce mata ba har ta fita ta koma na su ɓangaren, tana shiga ta samu kira a wayar ta kiran Yayan ta har bakwai, murmushi tayi tunanin ta shine tunda yau week-end ne baya aiki yana gida kawai neman ta ne yake da fitina dan tana gaya msa bata son shiga lokacin auntyn ta, kenan ɗan dakatawar da tayi bata bashi amsa bane har ya kira ta sau bakwai haka?

Dake ba wanka za ta yi ba kaya ta fara canzawa, tana cikin canza kayan ta ji an sake kira, tana zuwa ta ga shine ba ta ɓata lokaci ba ta ɗaga tana murmushi tare da danne wayar da kafaɗar ta dan ta samu ta saka zif ɗin siket ɗin ta tana faɗin "Yayana, rigima ko? Ba nace bana son shiga lokacin auntyna ba?"

Wata irin gigitacciyar murya ce aka daka mata tsawa cikin hargagi da ita wnda alamu suka nuna mai muryar ko hausa bata da mai kyau a baki ana faɗin "Auntyn ubanki ne ni, ƴar iska karuwa mai bin mazan mutane, wacece ke? Me kike nema gurin mijina? Ko kinsan da zan iya hallakaki har lahira akan mijina? Kinsan da na ɗauki ranki ni ba komai bane a gurina indai akan shi ne? To bari kiji karamar ƴar iska, mijina ya fi ƙarfin ki, kula shiga gonata tamkar ki tari zakin da yayi shekaru bai ci nama bane, sannan shigowa gidana daidai da yake da kin wa ƙarbarin ki sallama, dan haka kada ki sake kira min miji, ki fita a harkar shi tun kafin nasa a gano min ke sannan na saka rayuwar ki a gararin da kafatanin danginku sai sunyi tofin Allah tsine da kika fito ɗaya daga cikin su, banza ballagaza shashasha."

Ƙit ! Ta yanke kiran, hakan kuma ya sa Ummu lumshe idanun ta ta saki wayar ta faɗi, kwaram ta faɗa kan gado tana ambaton sunan Allah a zuciyar ta. Ta san yana da mata, kuma dake ita ƴar uwar sa ce ta ɗan ji labarin wai bata da kirki, bata da halaye na ƙwarai sannan ga rashin girmam shi shi kan shi, amma...amma ai bata ɗauka abun ya kai haka ba, yau ita? Ita da kan ta ce aka faɗawa wannan maganganun? Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un ! Wani irin kuka ta fashe da shi tare da faɗawa kan gado saboda tuno wasu abubuwa dayawa, dama haka zawarcin yake cike da ƙasƙanci da tozarci? Ashe shiyasa duk munin gidan miji iyaye ke cewa ayi haƙuri dai a zauna? Ban da Alhaji Kabir ma da ya ja mata wannan buru'ubar, har wata mace ta isa ta kira ta a waya sannan ta gaya mata wannan maganganu masu zafi haka? Har ita ce ake kira da banza ballagaza shashasha? Ita ba yarinya ba ba komai ba, wacece wannan matar tashi? Wacece ita? Fatan ta ɗaya ace babbar mace ce da shekarun ta suka fi nata, dan ta hakane zata iya yin daidai da ita su gurji junan su, amma idan bata kai ga shekarun ta ko kuma tsarar ta ce, ai ta cuce ta ba kaɗan ba wallahi, kuma ba abinda zai hana ta saka Nabila ta zane lata yarinya ko Abbun ta Fahad, ai ya gaya mata ba abinda ba zai iya yi akan ta ba.
Chapter 130 · 0% Book details