← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 168

Sashe 28

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jinjina kai Bilal yayi ya kalli Mukhtar da ba abinda yace face yanzu da yake bin Fa'iza da kallon tsana da kuma aza équation a kan ta, daga alamar tarawa da ɗebewa har da ruɓanyawa da ninkawa yake duk a take, cikin taushin murya Bilal yace" Ɗan uwa, k kula da Ammie, ni zan je na kai musu kuɗin, sun ce za su kira da minti sha biyar kacal."

A tausashe Mukhtar É—in ya kalle shi sai kawai yace" A'a, zamu tafi tare da kai ne."

Girgiza kai Bilal yayi zai yi magana kawai Mukhtar da bai cika magana ba ya kama hanyar fita daga falon, hakan yasa Bilal bin bayan shi da tunanin zai rarrashe shi a can har ya samu y zauna kar ya bi shi.

Kafin ya fit daga ƙofar Ammie ta ɗago ta kalle shi tace "Bilal..." Juyowa yayi ya amsa da "Na'am Ammie."

Cike da bada umarni tace "Idan ka samo Fahad, ina so mu san labarin yaran ɗan uwanka guda biyu da suka ɓace, a jikina da na mahaifiyarsu muke ji suna raye, kuma da kashe su ake son yi da an kashe su lokacin da aka samu damar keɓanta da su, amma sai ba'a yi haka ba aka ɗauke su daga nan, dan haka duk wani gidan radiyo da telebijin da yake na kuɗi ina so mu siyi babbar shiya a ciki dan a mana talla, ko Allah zai sa mu dace."

Kaf kowa kallo ta yake a wurin, Bilal kuma da mamakin ta yadda zasu fara yace" Amma Ammie, ta ina zamu fara? Sannan bamu da wata makama d zamu iya bayar da wata shaida akan yaran..."

Da sauri Nuriyya ta kalle shi tace" Akwai Yaya Bilal, a duk inda na ga yarana zan iya gane su, Kuwailat tun tana jinjira na saka mata wasu duwatsu a ƙugunta, ba lallai ta girma da su a jikin ta ba, amma kuma robar da aka ɗaura duwatsun tana ja ne sosai ta yadda in har ba ta cire ba to suna nan har yanzu a ƙugun nata, sannan tana snye da ƙananun ƴan kunnen zinariya masu ƙaramin jan dutsi, ba kowa zai gane anfanin su ba bare a rabata da su, sannan a wuyan ta, akwai wani tabo mai ɗan duhu wanda lokacin da aka haife ta mutane suna cewa wai mahaifa ce ta taɓa wuyan nata, Shiyasa ya fita daban da hasken fatar ta..."

Sai kuma ta raunana murya tace" Iya wannan ma hujja ce da zan iya gane Æ´ata Yaya Bilal, dan Allah ka taimaka min."

Jinjina kai yayi ba dan ya wani gamsu ba yace" Shikenan, zan ƙoƙarta."

Sabeer dake tsaye kuma cewa yayi" To Eesha fa?"

Kallon shi Nuriyya tayi sai kuma ta kalli Bilal tace" Eesha kuma tana da a..."

Tsaf! Da sauri Fa'iza dake tsaye har lokacin ta katse ta da cewa" Zamu iya neman Eesha da cikakken sunan ta ai, ma'ana *Nana Aisha Mukhtar Ahlan*."

Da sauri kowa ya zuba mata idanu har da Abbu dake zaune ya tangale haɓa yana sauraren su da kallon su, da mamakin abinda ta faɗa Abida ta miƙe tsye tace"...

*Alhamdulillah.*
29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*RUBUTACCIYA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

_NA_

*SAMIRA HAROUNA*

_SADAUKARWA GA_

*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_

_Bismillahir- rahamanir-rahim._

*13*

Da mamakin abinda ta faɗa Abida ta miƙe tsaye tace "Amma ta ya zamu saka sunan t cikakken bayan na tabbata wanda ya sace ta zai canza mata komai nata?"

Da i-ina da kuma rashin tabbas Fa'iza tace "Eeew...hakane,ina nufin muyi anfani da sunan, wataƙila muyi sa'ar samun ɗaya daga cikin su."

Sabeer dake kallon ta ne yace "Ba abu mai yiwu bane, idan muka ce muyi abinda kike tunani, to ina tabbatar miki a kwana ɗaya zamu tara Eesha cike da gidan nan, dan kowa zai yi ƙoƙarin alaƙanta kan shi da mu ne."

Sai kuma ya kalli Bilal yace "Yaya Bilal, ka je, idan ka dawo zamu tattauna a tsanake."

Da sauri Yaya Bilal ɗin ya juya ya fice daga falon, hakan ya sa Mukhtar bai ma san akan me suka tattauna ba, cikin alhini da tanzanko suka kasance musamman da ya zama babu mai labarin abinda ke faruwa, gashi kuma su biyu suka tafi amma babu wanda ke ɗaga waya idan aka kira dan a ji me ke faruwa, sun fi awa biyu kafin su dawo gidan tare da Fahad da yunwa da ƙishin-ruwa duk suka jigata shi, ga tafin da ya sha wanda har lokacin kumcinshi bai yi nasarar lashe shatin hannun ƙaton mutumin ba.

Ta wata fuska sun samu daidaituwar Fahad, dan kuwa gaba ɗaya ya daina fita a gidan, ba inda yake zuwa daga cikin gida sai masallaci. Haka kuma gidajen labarai na kuɗi sun ɗauki harama ana ta bayar da sanarwa akan yaran da suka ɓata tare da zayyana lambar da za'a kira idan an same su, sannan ga duk wanda ya san inda suke ko ya bada wani bayani a kan su, to yana da kyautar miliyan biyar cif.

*Cikin* tashin hankali da ɓari har kamar za ta yi kuka take cewa "Yanzu Hajia ya zanyi idan garin neman yaran nan aka gane da hannu na a ciki? Hajia tsoro nake ji wallahi, dan Allah kiyi wani abu a kai."

Cike da rashin damuwa Fa'iza tace "Kinga *Rabi* kar ki ɗaga min hankali, na ɗauka burinmu kenan akan ɓatan yaran nan, dan haka kar ki wani ɗaga hankalin ki."

Cikin É—ar-É—ar Rabi ta sake cewa "Na sani Hajia Fa'iza, ni tsorona shine kar a gane ni na É—auke yarinyar daga gidan."

Cike da tabbaci Fa'iza tace "Hakan ma ba zata faru ba, ki kwantar da hankalin ki."

Daga inda take amsawa ta jinjina kai tace "Shikenan Hajia, Allah ya sa mu dace."

Ba tare da ta amsa mata ba ta yanke kiran tare da kiran lambar DG kai tsaye, ba ɓata lokaci DG ya ɗaga dan kiran nata yake ta jira kena tsawon lokaci, yana ɗagawa yace "Kiran ki nake ta jira dama Hajajju."

A daƙile tace "Ina fata an samu ci gaba game da abinda na saka ka?"

Da ƙwarin guiwa ya shiga labarta mata "Hajia, kamar yadda kika sani ina yin bincike kuma akwai masu tayani binciken, yau mun yi nasarar gano wani gidan marayu ta dalilin wani Dr. E manuel, shine ya bani masaniya akan gidan marayun ya kuma tabbatar min zamu iya dacewa idan muka duba can, dan haka nake ta jiran kiran ki dan na sanar da ke yau zan bar ƙasar nan, kuma da yardar Allah ba zan dawo ba sai da wannan yarinyar."

Ajiyar zuciya ta sauke mai sanyin gaske tare da yin murmushi tace" Shikenan DG, naji daÉ—in wannan labarin, daga yanzu har ka dawo zaka iya kirana a duk sanda ka so dan ka sanar dani ci gaban da ake samu."

"Shikenan Hajia, sai kin ji ni ɗin." Ya faɗa tare da yanke wayoyin na su, zaune tayi tana sakin murmushi na farin ciki da jin daɗi, ta kashe milyoyin kuɗaɗe duk dan a gano mata yarinyar da har da kuskuren ta a ɓatan ta, wanda da bata bayar da goyon baya ba da yanzu tana tare da iyayen ta, amma in sha Allah za ta gyara wannan kuskuren da ta aikata ta hanyar dawo da yarinyar wa iyayen ta.

********************

Sallamar sa tasa Hajia Kaka gyara zamanta tare da dakatawa daga cin abincin ta amsa tana kallon shi, shi ma kallon ta yake yana kuma ƙarewa ɗakin kallo saboda hayaƙin turaren da yake tashi mai ƙamshin daɗi, ƙarasawa yyi ya zauna kujerar dake gefen ta yana faɗin "Hajia, wa ya cika miki ɗaki da gobarar nan?"

Kallon É—akin Hajia ta fara yi sannan ta kalle shi tace "Gobara kuma? A ina?"

Cike da wofantarwa yace "Na ga ɗakin sai hayaƙi yake."

Murmushi tayi cike da jinjina hali irin na Sa'ad tana sake kai lomar biskin ta dake matuƙar yi mata daɗi a baki musamman ma kifin da take taunawa a kai a kai, tana taunar abincin tace "Yanzu Sa'ad ba ka ji ɗakin nan na ƙamshi ba, yaushe rabon da ka samu ɗakina a kimtse haka? Sai da ka kawo min ƴar rainon nan tawa da bata da ƙiwar aiki."

Taɓe baki Sa'ad yayi tare da ƙara lafewa jikin kujera ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yana danna wayar shi, jin bai ce mata komai ba yasa ta sake dubanshi tace" A zubo maka abincin?"

Fuskar ta ya fara kallo, sai kuma ya kalli farantin abincin dake gaban ta, rasa fahimtar me ye ma take ci É—in yasa shi yatsina fuska yace" Me wai?"

Murmushi ta sake saki tace" Biski ne, wallahi yarinyar nan ba dai iya girki ba, wai ka ji daÉ—in biskin nan kuwa? Ni ban ma san a ina ta koyi haÉ—a shi ba, bari ka ji..."

Ta faɗa tana miƙewa da ƙyar ta nufi inda yake da loma a hannun ta da kuma farantin tana cewa" Ɗanɗana ka ji."

Ƙara yatsina fuska yayi kamar ta nufo shi da wani mugun abu, tana zuwa ta tunkari bakin shi yana girgiza kai tare da cewa" Um um! Bar shi kawai Haj..."

Kafin ya rufe baki ta ɗura masa lomar da ta saka shi ƙura mata ido, shi ba kallon takaici ba bana jin haushi ba, ba yadda ya iya da ya wuce ya shiga tauna lomar à tsanake haro yana wani waina idanu da son tantance ɗanɗanon, Hajia da ta zuba mishi idanu tana murmushi da fara'a tace "A zubo maka ko?"

Jujjuya idanu ya dinga yi alamar yana tunani, dan yunwa kam yana jin ta fa Shiyasa ma ya shigo ɓangaren nata dan ya ci abinci, uwa uba kuma abun ya birge shi a baki, saida ya kawar da kai yace "Kaɗan."
Chapter 28 · 0% Book details