← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 168

Sashe 131

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta ji zafin maganganun nan ƙwarai da gaske, hakan ya sa ta jima tana kuka na takaici, jin motsin Mamie na tahowa tana faɗin "Aunty, wai ba Haj..."

Da gudu ta tashi ta shige ban É—aki dan bata so ta ga tana kukan nan sai ta tambaye ta dalili, ita kuma abun kunya ne ta maimaita kalaman da yarinyar nan ta mata, yo shi kan shi Yaya Larwan É—in shekarun sa nawa da zai auri wacce ta kai shekarun ta? Ai ya faÉ—a mata yana son auren ta ne ma saboda shekarun ta zasu killace ta daga aikata masa aikin da kan iya saka shi firgita. Wanko idanun ta tayi sannan ta fito, tsaye ta samu Mamie tana kallon ban É—akin da taji motsi, da sauri Mamie É—in tace "Aunty Hajia fa jiran ku take, me kike yi ne wai?"

A hankali ta sauke towel ɗin dake fuskar ta ɗan ƙarami ta kalle ta, cikin dakusashiyar murya tace "Ba komai Aunty, ina shiryawa ne kawai ture ya shigar min idanu, kinji masifar zafin."

Da mamaki Mamie ta matsa kusan ta tana faÉ—in "Kuka kikayi aunty saboda turaren ?"

Turo baki Ummu tayi ta Æ™ magana, hakan yasa Mamie girgiza kai tace "Aunty, ni kal da gaske ke kika haifi Kuwailat? Ko farka ki akayi aka cirota?"

Da irin son abar maganar Ummu ta buga ƙafa tace "Auntyyyyyyyy."

Da sauri Mamie tayi tace "To shikenan, ama dai gaskiya taɓarar ki tayi yawa, dama Maman ki ta gaya min kina wa dattijon Hajia kuka (Jabir), ai da na so ma nace Abbun ki ya au..."

A ƙagauce Ummu ta kalle ta tace "Aunty, zan ƙarasa shiryawa."

Dariya mamie tayi tace "To na fita, me ye ba kya so na gani? Nonuwan? Ko uwawun?"

Sai kuma ta dakata tana duban ta tace "Ke bari ma kiji, kije ki dawo ki zo ki nuna min nonuwan nan naki, aure fa zakiyi, dole muyi gyara wallahi."

Irin kallon nan Ummu ta mata na _"Tofa."_ Hakan yasa Mamie yin murmushi tace" Oh ! Na manta, ashe gyaran da nake tunanin yi miki a gare ku na koye shi... Wayyo Allahna."

Ta faɗa tana ƙyalƙyala dariya ta fita daga ɗakin, Ummu ma dariya tayi saida ta ga ficewar ya sannan ta kalli kan ta a madubi, kawai sai ta samu kan ta da latsa nonuwan nata, sai kuma tayi murmushi na jin daɗi, ba ta da matsala da su gaskiya ta nan fannin, to tunda ta yaye Kuwailat wa ye ya kuma jan su? Tayi gyara kamar ba gobe saboda tunanin za ta sake haihuwa, sai gashi haihuwar shiru nonuwan kuma suna nan gidir gidir dasu a tsaye kuma a cike, ƙwarai hilba ta mata anfani sosai ta wannan fanni, haka ma albasa da madara peak da zuma sun taka muhimmiyar rawa, kazalika alkama, dan haka ba abinda za ta ce musu sai godiya.

*Idan kuna so zaku iya magana sai mu koyi wannan gyaran na nono in sha Allah.*

Da gaggawa ta ƙarasa shiryawa ta fita ta samu Nabila, nan Hajia ta basu kuɗi mai yawa sannan ne ma Ummu ta san me za'a je siya, kayan da za'a yi wainar sadaka ne da kuma cincincin, sai gyaɗa mai suga da kuma wani ɓangare na naman zabi da zasu biya su bawa mai kawo naman shi zai biyo su da shi har gida gobe in ji Hajia.

Hak suka je sukayo siyayyar nan suka kamo hanyar dawowa gida kusan bayan la'asar, suna shigowa farfajiyar gidan ta hangi motar Yaya Larwan tasan me ya kawo shi, dan haka ta haɗe fuskar ta har suka tsaya ƙofar ɓangaren na Hajia inda shima anan yake har ma ya gaisa da Haji sannan ya ɗan dakata ya jira su.

A mutumce suka gaisa da Nabila sannan t shiga ciki É—auke da wasu ledojin, inda dreba ya bi bayan ta da sauran kayan, Ummu kuma fuska tamke ta É—an juya msa baya tace "Barka."

Murmushi yayi yace "Ƙanwata, a haƙura ko na rera waƙar da aka yi dan ni da ke?"

Sake turo baki tayi ba ta ce komai ba, a hankali ya taka ya fuskance ta yana murmushi, cikin tattausan murya yace "Na sani ni mai laifi ne, amma ayi haƙuri a saurari uzirina."

Da mamaki ta kalke shi tace "Uzuri? Yayana wane irin uzuri da ya sa zaka ba w a matar ka waya ta zage ni son ran ta? Ka kuwa san irin maganganun da ta faɗa min? Kaji zagi da cin mutumcin da ta min wanda ba'a taɓa kwatanta yi min shi ba tun da nake a rayuwata? Sannan har wautar matar ka tasa tayi ikrarin ganin bayana."

Cike da rashin jin daɗi da takaicin halin *Fauziyya* ya jinjina kai yace" Duka na ji abinda ta faɗa ƙanwata, muna magana dake na ga nayi magana amma baki ban amsa ba, sai nayi tunanin kin ɗan aje wayar ne, hakan yasa nima na tashi na shiga wanka dan ina so na fita kafin l'asar, ina wanka ne naji bala'in ta tana faɗin wai dama amanar ta nake ci? Kenan gaske ne da aka ce zan ƙara aure? Shine fa kafin na suturta jiki na fito ta rufe ni a ban ɗaki, ban ina ƙoƙarin ta buɗe ni naji tana kiran ki, na mata kashedi da gargadin kar ta kuskura amma bata saurare ni, haka ina ji tana faɗa miki mugayen kalaman nan, amma wallahi ƙanwata na ɗauki mataki a kan ta wanda bana jin gobe zata sake maimata min ɗanyen kan nan."

Kallon fuskar shi tayi kamar mai son gasgata abinda ya faÉ—a, sai ta ji ya bata tausayi ma, kuma ai ya ce ya É—auki mataki akan ta, dan haka ba komai, zata shiga gidan nashi idan ta je ta sace zuciyar mijin ta ita kuma ta bar ta a gantale.

Cikin wata mahaukaciyar shagwaɓa da ita kan ta tasan ta wuce misali, amma da dagangan tayi saboda ta fara nuna ma matar shi iyakar ta kawai ta shiga bubbuga ƙafa tana kukan shagwaɓa tace "Uhhmm uhhhm! To shikenan naji na haƙura, amma sai an bani chocolat ɗina."

Zuba mata idanu yayi yana jin kamar zai suma dan wani irin abu da yake ji tare da yin murmushi yace "Ƙanwata rigimar ki ko? To in dai chocolat ne ai zan bayar, amma kafin nan albishirinki?"

Kallon shi tayi tana murmushi tace" Zuma."

Dariya yayi yace" Goro ake cewa." Ita ma kai tsaye tace" To ai bana cin goro."

Murmushi yayi yana cije leɓen shi yace" Ashe da wayon ki."

ÆŠan zaro idanu tayi tace" Yayana, shekaruna fa talatin a duniya, kaga kuwa ai ba abinda ban sani."

Dariya yayi yace" Ƙanwata alamu nuna min suke kina da son girma, ke dai baki ƙi ace ni ma kin girme ni ba ko ?"

Ajiyar zuciya ta sauke tace" Ba wai son girman nake ba, sai dai ina so idan ka san na girme ka to ka girmamani kawai, raini ne bana son Yayana."

ÆŠan sunkuyo kan shi yayi kusan fuskar ta cikin raÉ—a yace" Ina fata dai baki yi kuka ba da Fauziyya ta miki rashin hankali?"

ÆŠan gimtse fuska tayi ta kalle shi da kyau ba alamar wasa tace" Maganar gaskiya nayi kuka, musamman da na shiga tunanin ya adadin shekarun ta."

Numfashi ya sauke yace" Kiyi haƙuri dan Allah, amma na miki alƙawarin share miki hawayen nan ranar da kika tare ɗakina."

Rufe fuska tayi da tafukan hannun ta tace" Ni dai Yayana kunya nake ji."

Dariya yayi yace" Na sani mana, na sani ai ke ba ruwan ki."

Jinjina kai tayi sannan tace" To ina albishir É—in nawa?"

Cikin raɗa ya sake faɗa mata" Abbu ya ce min na turo magabatana, kuma yau zasu zo nema min auren wannan ƴar ƙriniyar, sannan na roƙe su Allah Annabi da su suka mana sati ɗaya a ɗaura mna aure."

Zaro idanu tayi tace" Lahhh ! Sati É—aya ? Wallahi babu mai É—aura min aure a sati É—ayan nan."

"Me yasa? Wani abu zakiyi ne da baki yi shi ba?" Ya tambaya yana tsare ta da idanu, jinjina kai tayi tace "Sosai ma."

Da wani mayateccen kallo ya bita yace "Menene shi abun?"

Saida ta É—an matsa daga gefen shi sannan tace "Bacci a gadon auntyna."

Tana gama gaɗa ta kwasa da gudu gudu ta shige falon Hajia, dan ta san halin Yaya Larwan zai iya sako mata zancen da zai sa kanta yayi nauyi, da kallo ya bita yana dariya, saida ya ga shigewar ya sannan yace "Ƙanwata kenan, to ai nima da gadajen a gidan nawa ko? Ba sai ki kwanta a can ba."

Girgiza kai kawai yayi ya shiga benz ɗin shi ya bar harabar gidan cike da farin cikin haduwar shi da Ummu da zumuɗin Allah ya nuna mishi ranar da zai kwashe yarinyar nan, dan shi ya kasa yarda ma shekarun ya sun kai yadda take faɗa. Haka kuma cike da baƙin cikin halayen Fauziyya da fara dana sanin auren ta a rayuwar shi.

*Da dare* kam su Alhaji Abbas da wasu dattawan suka zo nema wa Larwan auren Ummu, cikin farin ciki da shauƙin haɗa dangantaka suka saka musu sati uku mai zuwa a ɗaura aure, dan haka aka tsayar da magana kan washe gari mata zasu kawo kayan tsarabe tsaraben da suka saba, bayan su sun damƙa sadakin su da duk wani abu da ya kamata.

An kawo kayan Ummu tamkar na wata budurwa, inda labari ya game duk wani wanda ya san ta ko ya san wanda ya san ta, kai har ma wanda bai san ta ba yana da hoton kayan saboda yawan su, dan harka ce sukayi ta girma da son nuna bajintar su.

*BAYAN KWANA HUÆŠU*
Chapter 131 · 0% Book details