← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 168

Sashe 134

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Ummu* kam suna zuwa gida a ɓangaren na Mamie ake faɗa mata tayi baƙuwa tana nan tana jiran ta a falo, suna shiga ma Nabila na falon tale sake sanar da ita "Aunty kinyi baƙuwa, ta jima fa zaune tana jiran ki."

Ummu mamakin baƙuwar take, wacece ? Ba ta san kowa ba a nan bayan ƴan uwa, dan haka tace la Nqbila "Wacece wai ? Ta jima ne?"

Tana gaba Ummu na baya tace "Gaskiya ta jima aunty, tafi awa zaune muna ta hira."

Taɓe baki Ummu tayi ta ƙarasa shiga sai Mamie sake baya tana tsaye masu aiki na fito da kayan da suka siyo, suna shiga Nabila ta kalli matar da ta gaji da zama, amma abinda ya kawota ya sa ta dake ta kuma haɗe har tale sakar wa Nabila fuska tace" Yawwa aunty ga aunty Ummu."

Wacce Nabila ta kira da aunty ba ta wuce tsarar Nbilan ba, ita kan ta Nabila duniya ce da kuma girmamawa yasa take kiran ya da aunty, ba wai dan ta girme ga ba. A nutse Fauziyya ta taso da fara'a sosai tana tunkaro Ummu da faÉ—in" Sannu da zuwa aunty Ummu, sai yanzu ? Ai na jima i..."

Kafi ta ƙarasa faɗa ta kawo daf da Ummu, tana zuwa kuma cikin ƙarfin hali da rashin kunya ta jefar da gyalen dake saman kafaɗar ta, ba tare da tunanin komai ba ta ɗaga hannu sai kuwa a fuskar Ummu ta ɗauke ta da mari...

Mai aikin dake biye da Umlu saida ta saki ledar da ta ɗauko, dan ita kawai tsbar tashin hankali ta hango yadda yau Abbu Mukhtar zai hargitsa gidan nan ne saboda an taɓa babynshi. Haka ma Nabila da ta juyo a haukace ta kalli matar tana ayyana _"Dama tsinanniya ce ta tarba?"_

Takaici, baƙin ciki, dana sani, al'ajab, mamaki, ruɗu da toshewar kai suka saka Ummu zaro idanu kawai ta kalli matar da bata fi tsarar ƙanwar ta ba, gata kuma bata da suffar mahaukata saboda shigar ta da jikin ta, hasalima kyakyawa da ita duk da dai bata kai Ummu kyau da haske ba. Hango kalar dukan da zata mata ne ta fara yi yasa ta saki jaka da wayar ta tare da zame gyalen ta duk ta jefar a ƙasa... Ta ɗaga hannu kenan za ta kai ga jikin Fauziyya, wace ita kuma ganin ta mari Ummu ta ci gaba a kan ta na farko kamar yadda malamin ta ya faɗa mata, sai ta fara ƙoƙarin zaro ƙaramar wuƙar data soke a siket ɗin ta da niyyar yanka wuyan Ummu idan ya so ita la a kashe ta.

Sai dai kafin Ummu da ita kanta Fauziyya su aikata abinda sukayi niyya Nabila ta shiga tsakiyar su, ba wanda ya ankara sai saukar mari suka ji a kumatun Fauziyya Nabila ta wanke fuskar ta da shi, kafin Fauziyya ta gane Nabila ce ba Ummu Nabila ta sake ɗauke ta da mari, a gigice Fauziyya ta ɗago bayan tayi ihun da ya karaɗe gidan, amma sai Nabila ta kwashi ƙafafun ta ta zubar ƙasa tare da bi ta kan ta ta fara naushi kamar dama ba ciki take da ita.

A nutse Ummu tayi wani shaƙiyin murmushi tareda duƙawa ta ɗauki jaar ta da wayar ta sannan ta kalli mai aikin nan tace "Ki ce Adama ta zo ta ɗauki kayan nan ta kai min ɗakina."

Jiki na rawa mai aikin ganin har wasu ma'aikatan sun fara fitowa haka ma Mama ta kwaso a guje ta shigo ta amsa da to ta nufi inda za ta ga Adama, Ummu kuma kan kujera ta ƙarasa ta zauna ƙafa ɗaya kan ɗaya saboda ganin Nabila ce ke ta casa matar da bata san ta ba. A rikice Mamie ta kalli Ummu tace "Aunty me ye haka? Kina kalo za'a yi ɓatacciya?"

Ƙala ba ta ce ba sai Mamie da take ta ƙoƙarin ɗago Nabila tana fadin ta daina mana me ye haka? Nabila kua yadda ka san mai aljannu fadi take "Aunty Ummun? Aunty Ummun ce zaki ɗaga hannu ki mara? Wa ya turo ki? Nawa suka baki? Ƙaramar ƴar iska."

Sai da Adama da ɗaya mai aikin nan suka zo ne suka kama ma Mamie raba su Nabila, lokacin har wata mai aiki ta tafi shaidawa, ƙwarai da gaske Fauziyya ita ta zo gidan nan san tayi tijara ta ɗaga hankalin kowa, saboda ta san ahalin Ahlan ai tasan masu kuɗi ne da basu san wahala ba bare ma su iya jagaliyanci, bata san akwai ƴar daba gidan ba gaskiya da ta ɗebo zuga guda sun zo.

Ana cikin kiciniyar raba su ɗin nan Fauziyya ta shammaci mutane a haukace ta sa wuƙar nan ƙarama ta yanki damtsen Nabila da lokacin hankalin ta na kan Mamie dake mata faɗan me ya aike ta wannan faɗan? Bayan ita ta ga alamun juna biyu a tare da ita, ihu Nabila tayi tare da dafe hannun ta da tuni ya fara fitar da jini. Kukan kura Ummu tayi ta ɗauke fuskar Fauziyya da marin da ya saka ta sakin wuƙar dan bata yi tsammanin zuwan wani marin ba bayan duk wannan jigatuwa da tayi a hannun Nabila.

A gigice ta duƙa zata ɗauko wuƙar Adama tayi saurin ɗaukewa a haukace tana daka wata irin tsawa da tasa mutanen ɗakin kallon ta tana faɗin "Kan ki ɗaya wai? Ƴar gidan uban wacece ke?"

Hakan yasa wata mai aiki rusunawa kusan kunnen Mamie ta faÉ—a mata "Mamie Adama bata da lafiya, idan ta rikice mun shiga uku wallahi."

Kafin ma Mamie ta maida kallon ta ga Adama har masu aikin nan biyu sun riƙe Fauziyya gam tana ta kubcewar su sake ta, kallon Ummu take hankali tashe tana faɗin "Kinga wannan jinin da ya fito a hannun wannan? Wallahi sanfuri na zo takanas dan na nuna miki kalar uƙubar da na tanadar miki, nayi alƙawari ne ko zanyi yawo tsirara sai an fito da gawar ki a ranar da aka kaiki gidan mijina, idan har ban zama ajalin ki ba Allah ya haukatani a daren ki na farko da mijina."

Daga kalaman ta suka gane me ya faru, Mamie kan ta sai lokacin ne ta ma gane ko wacece, hakan yasa da mamaki ta furta" Fauziyya? Ke ce wai dama?"

Cike da fitsara tace" Ni ce, ni ce, da matsala ne?"

Girgiza kai Mamie tayi, kafin tayi magana Hajia da Fa'iza suka shigo tare hankali tashe, sai dai suna shigowa Hajia na tambaya" Subhanallah! Lafiya? Me yake faruwa?"

Shiru ba wanda ya bata amsa, hakan yasa take ci gaba da kallon mutanen É—aya bayan É—aya har ta kalli Nabila dake zubar da jini a hannunnta, matsawa tayi kusan ta tana kamo hannun tace" Nabila, ciwo kika ji ? Wai faÉ—a kuka yi ne?"

Tayi maganar tana kallon baƙuwar matar nan, lokacin ne kawai ta iya kallon fuskar ta, dake da gilashin ta a idanu tar ta gane ta, dan haka tace" Fauziyya? Ke ce wai dama?"

A haukace Fauziyya ta kubce daga riƙon da msu aikin suka mata tace" Nice, kula wallahi abin da kuka gani yanzu kaɗan ne idan har kukayi haukan kai wannan yarinyar gidana da sunan matar Larwan."

Tana gama faɗa ta juya a fusace za ta fita, da azama masu aikin suka so sake riƙe ta da tunanin ai ya kamata ta fuskanci hukunci, sai kawai Hajia ta masu alamar su ƙyaleta, hakan yasa Fauziyya fita a jigace tana tofar da yawun bakin ta da suka yi jini ga kukkurjewa da duk fuskar ta tayi.

Da ƙarfi Ummu ta faɗa kan kujera tana rintse idanu, ya Allah! Ya Allah ! Kawai take ta maimaitawa a zuciyar ta, Hajia kuma Fa'iza ta kalla tace "Dan Allah Fa'iza taimakawa Nabila, jini take zubar wa."

A ladabce ta amsa da to ta kama hannun Nabila suka fita, hakan yasa Hajia kallon Mamie tace "Wai me ya faru? Yaushe ma Fauziyya ta zo gidan nan?"

Cike da damuwa Mamie tace "Wallahi Hajia ban sani ba, mun dawo wannan take faɗa ma ta tayi baƙuwa, ni na tsaya a ciro kayan da muka taho da su, kawai fa sai wannan hayaniyar na ji Nabila tana faɗin wai Fa'iza ta mari aunty."

Irin É—an tsakin nan tayi tare da zama kan kujera tana faÉ—in" Gaskiya ba zan juri wannan abun ba, yaushe ma na haÉ—u da Æ´ar tawa da za'a dinga kirarin hallaka min ita? Wallahi ba zai yiwu ba."

Hajia ma cike da tabbaci tace" Ba zai yiwu ba ko kaÉ—an, bari Mukhtar É—in ya zo ayi wa tufkar hanci, wallahi sai dai duka dangi su ga laifina."

Ummu dai na jin su, amma ita abinda ta yanke a ranya shine ko su basu dakatar da wannan auren ba ita kam ba zata iya ba wallahi, dan haka ma take sauraren su kawai haka kuma ta wuni sukuku har dare, Fahad ba irin zagin da bai ma Fauziyya ba da ya ga yankan da ta ma Nabila, inda Yaya Bilal ma hankalin shi ya tashi uwa uba kuma Abbu, hakan yasa shi girgiza kai yana kallon Hajia yace "Mamie gaskiya kuyi haƙuri, amma wannan auren bana jin zai yiwu, tashin hankali irin haka? Ba wai tsoron ta ko ba za'a iya bane, sai dai ikrarin da tayi zai iya cutar mana da yarinya ko ma ta salwantar mana da rayuwar ta ta, dan haka Mamie gaskiya na dakatar da auren Baby da Larwan."

Cike da gamsuwa Hajia tace" Ka min daidai, kuma ko da baka É—auki wannan matakin ba ma ni zan É—auka, da Ummu ta iya masifa ne zan iya yarda ko dan ta koya mata hankali, amma ta je can da halin ta."

Fahad dake ta huci jinjina kai yayi yace" Wallhi da ina nan ko? Da saidai Larwan ya zo ya É—auki matar shi, amma ba abinda zai hana in kakkarya ta wallahi."

Yaya Bilal ne yace" Ku dai a yi haƙuri yanzu komai ya wuce, zan kira Alhaji (Abbas) na sanar da shi abinda ya faru, sannan a kira Larwan ɗin a mayar masa da duk abinda ya kawo, nan da gobe a bashi kayan shi, amma zama lafiya ya fi zama ɗan sarki."
Chapter 134 · 0% Book details