Sashe 79
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murmushi Abban yayi ya dafa kafaÉ—ar shi yace "Karka damu Jabir, burina yanzu shine naga ku manyan Æ´aÆ´an nawa kun hau kan turbar da ta dace, Alhamdulillah kun samu ilimin addinin da nasan ko iya shi kawai ya isheku rayuwa mai nagarta, amma bayan haka ina so na ji abinda kuke son faÉ—a min da wuri wuri, dan naga ko da taimakon da zan iya muku?"
Kallon juna sukayi shi da Aliyu, da idanu suka gama yanke shawarar kawai su sanar da shi É—in tunda ya matsa, Aliyu ne ya kalli Abban a ladabce yace" Abba, ba wani abu bane dama, kamar yadda kuka sani ina son yin koyarwa, to shine nake so ku tsaya min dan ina son buÉ—a islamiyya, zan tafiyar da ita ne akan wani tsari da na gani a Madina, sai shi kuma Jabir, kun san dama shi dai É—an kasuwa ne, kuma har tafiyar can ma bai daina aikin wahala ba dan ya samu kuÉ—i, to Alhamdulillah ya tara kuÉ—in kam..."
Aliyu yayi maganar yana dariya saboda hararan da Jabir ya watso mishi, dariya Alhaji ma yayi yana ci gaba da sauraren Aliyu da ya ci gaba da faɗin" Ya nemi kuɗi sosai Abba, yayi aikin wahala ya wa larabawa bauta duk dan ya tsaya da ƙafafun shi, da taimakon Allah kuma ya fara siyan kaya a can yana turowa wani abokin mu anan, to Alhamdulillah zan iya cewa ya zama babban gwaska ta nan wajen, dan yanzu haka a Saudia da Madina da Lebanon akwai wasu da yayi sabo da su kuma yake siyan kayan nan namu na gida yana raba musu suna bashi kuɗin, Abba, a taƙaice dai Jabir ya tsayu sosai."
Gyara zama Aliyu yayi yace" Abinda yasa na faɗa muku haka Abba, yana son buɗa babban shagon da zai zama a cikin yake ɗaukan kayan da yake rabawa, to shine yake son ka saka masa hannu, dan yana son shagon ya kasance a idanun jama'a ne, sai taimako na gaba kuma da yake buƙata Abba... Conteneur ɗin ka dake yawan tasowa daga Dubai da Chine, yana so idan ana muku lodi ya dinga bada nashi saƙon, idan abubuwa suka yi kyau wata rana shima sai mu rasa wurin zama tsabar yawan conteneur ɗin da ya kawo a garin nan."
Dariya Alhaji yayi yana kallon Jabir dake girgiza kai ya rasa me ke damun Aliyu, cike da ƙarfafa guiwa Alhaji yace" Ma sha Allah Jabir, ni dama nasan babban ɗan kasuwa ne za'a yi tun da ka faɗa min har ga-ruwa kayi da wanke wanke a gurin mai siyar da abinci, Allah ya sa albarka Jabir, Allah ya tallafe ka har kai ma ka tallafi dubbunnai."
A tare shi d Aliyu suka amsa da" Ameen Abba." Sai kuma ya ɗora da" Duka ba damuwa, na ji buƙatun ku kuma ba zasu gagara ba, da izinin Allah za'a muku yadda kuke so, Allah ya dafa mana."
Amsawa suka ƙara yi inda suke ta murmushi da mishi Addu'ar ƙarin lafiya mai anfani, shi kuma shiru yayi na wani lokacin kafin ya kalli Jabir yace" Jabir, akwai wani babban wurin aje kayan gonana dake nan bayan ofishin ƴan sanda kan titin dake zuwa babban likita, me zai hana ka je ka duba? Idan ya maka Kagaai shikenan ko, sai a fara abinda ya kamata, dan gaskiya wurin titi ne sosai kuma fuskar jama'a."
Kallon shi Jabir yayi, a nutse ya kamo hannun shi yana tattausawa idanun shi taf da hawaye yace" Abba, ba damar mu zo da abu muna so sai ka mana shi? Abba yaushe ne zaka ce ba zaka mana ba saboda bai dace ba? Abba da wuri haka?"
Murmushi ya mishi yace" To ai ku ɗin ne ba kwa zuwa da abinda bai dace ba, shawara kuke yi da kuma hangen nesa kafin ku zo da buƙatar, shiyasa kullum nake jinjinawa tunanin ku."
Jinjina kai Jabir yayi yace" Mun gode Abban mu, ba mu san ya zamu yi ba idan ba kai? Abba Allah ƙara maka lafiya da nisan kwana mai albarka."
"Ameen Ya Allah." Ya faɗa da fara'a sosai a fuskar shi, Aliyu ya ƙalla dake kallon tsantsar ƙaunar da suke ma juna yace "Aliyu, tunda na siyi wannan gidan na su Hajia Mairo, da gida na so yi muku kai da Jabir da Khamis ku zauna nan dan aure zan muku, to tunda ka zo da maganar nan ina ga zaka iya shiga kai ma Kaga idan girman sa zai maka yadda kake so, Kaga daga nan sai a fara ginin makarantar ko?"
Da jin daÉ—i Aliyu ma ya sumbaci hannun Alhaji yana mishi godiya da addu'a sosai, ba su tashi daga nan ba haka suka ci gaba da tattaunawa har rana ta fito.
A shirye auta ta fito sanye da zunbulelen hijab É—in ta na islamiyyar da ya saka Jabir sake mutuwa akan yarinyar har saida ya furta "Ya Arrahaman."
Ba kwalli ko ɗigo ɗaya à fuskar ta, yarinya ce ƙarama, amma shigar nan da tayi ba ƙaramar kamala da fuskar manya ta yafa mata ba, a zahiri kake gane ƴar dattijo da dattijuwa ce, ma'ana ƴar manyan mutane da ta samu tarbiyya, zai so hakan, zai so a bashi ita tun yanzu, ya ji ya gani zai iya rainon ta har sanda za ta gama cikar kamalar ta, amma ba zai juri nesa nesa da ita ba, maza yanzu mace ta gari suke so, dan haka ƙaracin shekarun ta ba zai hana namiji na ƙwarai wawar ta ba.
Yadda yake kallon fuskar ta dake ɗauke da murmushi irin na maman ta yasa har ya ɗan shagala da kallon nata, ba tare da sanin shi ba kuma yake taya ta murmushin sakamakon tsokanar da Aliyu ke mata cewa ta kusa daina zuwa islamiyyar kowa sai tashi, amma hakan ba yana nufin za ta makara ya ƙyaleta ba, zane ta zai yi. Da fara'a Abba ya ɗan rumgumata jikin shi yana shafa kan ta yace "Aliyu autata ce fa, ko ni ban taɓa dukan ta ba."
Dariya duk suka yi sai Kuwailat dake rufe fuska dan kunya, jin Jabir bai sa baki a maganar ba duk da dama zai yi wuya ya furta wani abun, amma sai Abba ya juya ɓangaren da yake yana faɗin "Kai Jabir ka yarda ya dak..."
Ba wai kallon da ya kama Jabir É—in na ma Kuwailat bane ya bashi mamaki, sai yadda yayi saurin sadda kan shi cike da basarwa da kuma kunyar yadda Alhaji ya kama shi yana kallon Æ´ar tashi, wani murmushi Alhaji yayi irin shikenan É—in nan na gano ka tare da dafa Kuwailat yace "Autar Mamien ta, maza kama hanya tafiyar ki, Aliyu bai da tausayi zai iya zane min ke anan."
Da fara'a ta kma hanya tana musu bye bye da cewa "Sai na dawo."
ÆŠaga mata hannu Aliyu yayi yace "A dawo lafiya."
Saida ta tafi Alhaji ya sake duban su yace "To yanzu ya maganar aure? Na ji gaba ɗaya tunanin ku kan yadda zaku kyautata rayuwar ku ne kawai, ban ji wani cikin ku yace na je gidan dattijo wani na karɓo masa ragamar kulawa da wata kyakyawar matashiya ba?"
Dariya Aliyu yayi inda Jabir ya kalli Alhaji cike da tsarguwa sai kuma yayi murmushi yasx girgiza kai, Aliyu ne ya shafa kan shi cike da kunya yace" In sha Allah Abba, muna nan muna nema shima, da zaran mun samu waÉ—anda suka dace, zamu izaku gaba ku nemo mana É—in."
Girgiza kai Alhaji yayi da rashin jin daÉ—i yace" Gaskiya ban ji daÉ—i ba, ace kamar ku babu ma mai niyya a cikin ku, yadda na so fa shine kuna zuwa da kamar sati É—aya bikin ku za'a yi."
A tausashe sosai cikin ladabi Jabir yace" In sha Allah Abba zamu gabatar muku da su nan da É—an lokaci."
Jinjina kai yayi ba fara'a tare da shi yace" Shikenan, Allah ya yarda, amma ku sani idan naga kun share sati É—ayan nan kuna neman cinye na biyu, to fa zaku gane Abban ku bai da tausayi, dan kuwa tsaf zan nema muku mata ku aura."
Murmushi duk sukayi inda Aliyu ya ƙara shafa kanshi yace" A'a Abba, in sha Allah ma ba zata kaimu ga haka ba."
Sai Jabir da ya kalli Alhajin da kyau cikin nutsuwa yace" Abba, ko auren je ka ga ɗakin ka kuka mana zamu karɓa da kulawa muyi godiya, kun isa damu ne kuma zamu karɓa muyi biyayya da yardar Allah."
Kallon shi Alhaji yayi cike da jin daÉ—in yadda ya nuna zai masa biyayya, inda Aliyu ya kalli Jabir da mamaki yace" Ka tabbata Alaramma, sami'ina ne wa aÉ—a'ana?"
Da idanu ya amsa mishi da tabbas ta hanyar lumshe su sosai, jinjina kai Aliyu yayi da tsokana yace" Ko da yake ai kana da wurdin da zaka yi ne ku zauna da soyayya, ni kuma ka ga ba ruwana ko?"
Murmushi dai Alhaji yayi yana jin farin ciki yadda suke fahimtar junan su a kamar ƴan uwa abun na birge shi. Daga nan ya miƙe ya bar su ya tunkari ɓangaren Ummu da suka fi kusa da shi dan gaishe da matan kamar yadda ya saba kamar ya shirya ɗakin Hajia Atika dan yau ita ce da shi.
*In sha Allah mun kusa fara darasi na kayan marmari.*
*Alhamdulillah.*
15/08/2023, 20:13 - MOM LATEEF: 👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
*RUBUTACCIYA*
👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
_NA_
*SAMIRA HAROUNA*
_SADAUKARWA GA_
*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_
*Tallah, tallah, tallah*
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_