Sashe 120
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sannan ne Alhaji Abbas yace "Sai kuma magana ta biyu da ta kawo mu, wacce ita Hajia Radiya ta yi alƙawarin ba zata koma ƙasar ta ba har sai kin amince da buƙatar ta."
Murmushi Mama tayi tana sadda kai tace "In sha Allah ma babu abinda zai gagara muyi musu."
Yana kallon fuskar ta ya furta "Auren Nabila take so ki ba Fahad, dan Allah ? In dai da gaske komai ya wuce."
Ɗan kallon shi Mama tayi, amma haiba da kwarjini sai ta sadda kai tace "Alhaji, wallahi ban hana Nabila amincewa buƙatar su ba, amma indai ni na haifi Nabila, kuma da gaske tayi tuna na gaskiya, in sha Allah Nabila ta amince da Fahad kenan, idan na koma gida umarni kawai zan bata, Hajia sai ki saka musu lokacin da ya dace."
Ba wanda bai yi farin ciki da wannan magana ta mama ba, wacce ta ce ita idan a so samun ta ne bayan kammala istibra'in Nabila da sati É—aya a É—aura musu aure abun su, take Mama ta amsa ta yarda da hakan, hakan yasa aka yi ta murna sai Ummu da suka kira wacce tunda Mama tace tare da Alhaji suke ta shige ciki basu haÉ—u ba.
*A GURGUJE*
Mama ta cika musu maganar ta, dan suna komawa gida tare da Ummu suka saka Nabila tsakiya, dole ta amince da buƙatar su har da raha da cewa "Wallahi aunty Ummu dan dai yana ɗan uwanku ne, ba dan haka ba bani ba shi."
Ummu dariya tayi ta amsa mata da "To mun gode a haka ma." Amma kuma sai ta ce ba fa za'a ɗaura mata aure a kai ta wani gari ba tare da Ummu ba, dan haka ma Ummu ta sake jadadda "Gaskiya fa ba zan saɓa umarni ubangiji ba, an ce mace mai idda ta killace kanta, ba zan ta yawo sakaka ba alhalin ina idda, ke dai Allah baku zaman lafiya."
Ita ma cike da tabbaci tace "Wallahi tallahi Mama na yarda zan auri Fahad, amma fa sai bayan auntyna ta gama idda, idan bata raka ni ba waye zai raka ni? Dan haka in ya musu to, in bai musu ba su ƙara gaba."
Dole dai suka bar ta a haka, da suka sanar da Hajia ta ce ba damuwa, da yau da gobe da bayan wata uku ai duk kamar gobe ne wajen Allaj ba wuya, dan haka su Hajia suka tattara tare da Kuwailat da saida ta je ta É—auko kayan ta tama su Hajia sallama sannan suka tafi dukan su a mota.
*Bayan sati ɗaya* da haka kuma aunty Mardiyya ta zo, ita kawai suna waya da Ummu ne da sunan zata sauka gidan su, na farko ita ma taga Ummu sannan ta isar da saƙon Jabir wajen Alhaji, ba ta san cexa Alhaji Kabir shine mijin Ummu ba, ita dai sun zo ita da Anna Ummu da Mama suka tarbe su yadda ya dace.
*Washe gari* da sassafe suna tsaka da shiri Ummu ta kawo musu abun kari, gaisawa sukayi sosai kafin tace "Mamma, ga abincin ku."
Aunty Mardiyya dake shafa mai ta amsa da "Ok ina zuwa, bari na saka kaya."
Kallon su tayi daga yadda suke shiri tace "Mamma ko fita zaku yi?"
Amsa mata tayi da "E wallahi, ba na faÉ—a miki abu biyu zai kawo ni ba? To na ganki yanzu zamu fita gabatar da É—ayan."
Da kulawa Ummu tana kallon Anna dake shafa kwalli a idanu tace "Kuma Mamma sai da sassafe haka? Har ina zaku je?"
Nuna mata Anna tayi tace "Akwai babban jikan ta dake nan, to akwai wani ubangidan sa da ya msa komai a rayuwa, kusan ma kamar shi ya haife shi, to shine da ya je yace yana so mu zo mu ƙara yi msa godiya saboda dai yasan duk alkairan da yake masa muna sane kuma muna jin daɗi."
Cikin gamsuwa Ummu tace" Gaskiya ne, hakan yana da kyau ai."
Anna jin su kawai take, amma idan akwai abinda ta fahimta a ciki bai wuce mahaifi da ta ji an ambata ba, sam sam bata jin hausa ko kaÉ—an bayan gaisuwa, dan haka take shiru shiru saboda bata san da yaren da zasu gane juna ba.
Suna cikin cin abinci Ummu tace "Duk da bana son na cika yawan fita, amma zan raka ku sai na kaiku, bai kamata mu bar ku ku hau adaidaita ko taxi ba."
Murmushi aunty Mardiyya tayi tace "Kar ma ki damu kan ki, akwai wani É—an gidan da yayi magana da shi zai zo ya É—auke mu."
Murmushi ita ma tayi tace "Yawwa, gaskiya hakan ya fi."
Tunda Khamis ya faɗa mishi shi fa a kwatancen da ya mishi gashi ya zo kuma kwatancen gidan su aunty Ummu ya nuna Jabir ya shiga tunani da mamaki, gudun kar ya mishi kwatance ba daidai ba ya sa kai tsaye ya ba Khamis lambar aunty Mardiyya ta gaya mishi inda suke, to ya haka kuma? Aunty Mardiyya ta ce gidan ƴar ƙanwar ta da aka samu kwanan nan ne suka sauka. Amma dan ya samu tabbaci sai ya kira yace "Aunty, wai a ina kuka sauka ne?"
Da mamakin tambayar ta amsa da "Jabir ina inda nace maka zamu sauka."
Shi ma dai da yanayin rashin fahimta yace "To ai aunty kwatancen ne ya nuna *gidan su Maamana*, shiyasa na sake tambaya."
Kamar suna gaban juna ta jinjina kai tace "Ummm! To mu dai anan kaga mai gidan sunan ta Aminatu, sai ita Æ´ar Nuriyyar da bata jima da dawowa nan ba saboda rabuwa da sukayi da mijin ta, sai kuma autar gidan Nabila wacce ita ce Fahad autan *Hajiarka* zai aura in sha Allah nan da wani lokaci."
A duk cikin maganganun ta ba abinda ya fi fahimta da kyau ya kuma fi riƙe shi sosai a cikin kan shi sai *saboda rabuwa da sukayi da mijin ta*... Sai ya ji gaban shi ya faɗi daga jin wannan magana da bai gama tantace da wa ake nufi ba, yanayin tashin hankali da zufa suka nemi rufe shi lokaci ɗaya , da sauri ya tambayi aunty Mardiyya "Wacece ? Wacece ta rabu da mijin nata aunty?"
Ba tare da tunanin komai ba tace "Ummm! Ummu Kulsum, ƴar ƙanwar tawa."
Saida Jabir ya dafe kan shi saboda bugawar da yayi mishi yace "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Maama, me ya faru? Ya aka yi ban sani ba?"
A nutse aunty Mardiyya tace "Jabir, ka san wani abu a kan su ne?"
A dake ya amsa da "Ba komai aunty, shikenan kawai."
Kafin ta ce wani abu kuma ya yanke kiran ya bar ta da tunanin to ko lafiya? Ummu ma saida ta fita rakiyar su ta ga Khamis ne ya zo É—aukar su, anan ta fahimci Jabir ne kenan jikan Anna? Sannan sun zo yi masa godiya ne wajen Alhaji? Haa dai suka rabu ba wanda ya nuna wani muhimmin abu.
*Washe gari* suka dawo daga Niamey shi da Abban shi, zai iya ce wa ya fi jin daɗin zama Agadez akan Niamey, saboda ko ba komai kakanin shi sun nuna alamar damuw a fuskokin su da kunyar haɗa idanu da shi, to amma kakar shi da ta haifi mahaifin shi ita da ƴan uwan mahaifin nashi babu wnda ya nuna masa wannan alamar, hasalima zalamar su ce ta fito fili akan ganin irin arziƙin da Allah ya mishi wanda shi a wurin shi ba komai bane face kaɗan da ya ɗebo saboda su, hakan yasa bai ji daɗin zama da su ba, babban abinda ya bashi haushi sosai game da su shine yadda Kakar shi ta masa maganar wai ga ƴan mata nan cikin dangi ya zaɓi ɗaya sai ya aura, bai iya ce mata komai ba sai mahaifin shi da ya bata amsa kawai.
Shi ba la wannan ne gaban shi ba, abinda ya ji jiya ne tashin hankalin shi, Abba ya rabu da Maama? Me ya faru? Me ya shiga tsakanin su? Damuwar da suke ciki har ta kai ƙadamin da dole sai rabuwa ce kaɗai maslaha? Ya Allah! Ya Allah! Me ya shiga kan Abba ne? Me Maama tayi da zafi da har mata uku da ya zauna da su basu taɓa kwatanta yi masa ba? Da wannan tunanin suka shigo kuma har ya haɗu da Aliyu, ya jima yana kallon fuskar shi da mamaki, wannan maganar ce dama ya ƙi faɗa masa a waya? Tun Aliyu na kawar da kai har dai shima ya kalle shi yace "Jabir? Me ye a ran ka? Faɗi ina ji?"
Girgiza kai Jabir yayi sannan ya gyara zama ya sae kallon Aliyu da kyau yace "Maama bata gida, me ya yi zafi tsakanin su da Abba?"
Ajiyar zuciya Aliyu ya sauke yana duban shi cikin nutsuwa yace "Na so faɗa maka tun a waya, amma mahimmancin maganar ya sa ban yi haka ba, ƙwarai aunty da Abba sun rabu, kuma rabuwar tasu ta taɓani sosai ta yadda na so ƙalubalantar Abba, amma da naji yana sanar da su Hajia babba dalilin sa na sakin nata, sai na gamsu na kuma yarda da hukuncin da ya yanke ɗari bisa ɗari, shine daidai."
Zubawa Aliyu idanu yayi cikin tashin hankali yace" Alfasha Maama ta zo da ita?"
Girgiza kai Aliyu yayi yace" Ba alfasha ko É—aya."
A É—an kausashe Jabir yace" Kuma a hakane kake ganin hukuncin da Abba ya yanke yayi daidai? Saboda me? Dan ba...."