Sashe 39
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai kuma ta taɓe baki ta harari inda Aisha take tace "Hmmm! Ƴar gwal kenan, Allah wadaran naka ya lalace."
Aisha sam bata gane me tambayar ta ke nufi ba, dan haka ba ta ji zafi ba hatta da karin maganar nan da ta yi, ita ta fara fita bayan ta musu sallama sannan Sa'ad ya bi bayan kafin Maman shi.
*Shirin Farko Na DG*
Suna hanyar su akan titi da dama kullum da jami'ai saboda kusa da gidan gwamna ne, anan jami'an suka tsayar da shi wai zasu bincike shi, ya so faɗa musu ba uban da ya isa, amma dake yana tare da mata biyu masu mahimmanci a rayuwar shi, sai kawai ya ƙyale su suka shiga lalubar aljihunshi da lalabe komai na jikin shi, ɗaya jami'in kuma na duba cikin mota, kallon juna jami'an sukayi suka girgiza kawunansu, dan haka ɗaya yace "Zaka iya tafiya."
Kallonshi kawai Sa'd yayi yana hardace kamanninshi a cikin ƙwaƙwalwar shi, zagayawa yayi ya shiga ya rufe ƙofar, haro zai wa motar key suka sake dakatar da shi, ɗaya daga ciki ne yace "Yallaɓai, zamu binciki matan ne, musamman ma wannan yarinyar."
Da mamaki ya kalle su yana fitowa yace "Matan?"
Da tabbaci jami'in yace "E, ai Yallaɓai mata yanzu sun zama dillalan miyagun kasuwanci, ma fi aksari kuma cikin lulluɓin su."
A tsanake Aisha ta buɗe motar ta fito tana kallon su, hakan yasa ɗaya jami'in nufa inda take yana faɗin "Yawwa ƙanwata, ɗan cire hijabin naki?"
Duk da ba hijabin bane jikin babban mayafi ne da ta rufe har kan ta, cikin tsawa da hargagi Sa'ad ya nufesu yana faɗin "Ba zata cire ba, ke, me ya fito da ke?..." Sai kuma ya kalle su yace "Kunga, ban ce zan shiga aikin ku ba, ban kuma kayan da kuke sanye da su ba, nasan ni mai laifi ne da cancanci kowane irin ƙasƙanci, amma sam ban da wannan, ban da ta hanyar Eesha."
Taruwa sukayi à kan shi suna tabbatar mishi su fa aikin su suke, dn haka ka da ya taka dokar da zata ɗaure shi, Mama kuma da takaici ya gama kamata duba da duk wannan zaƙewar yana yi ne akan yarinyar nan, kasashe ta zuro kanta tan faɗin me yasa ba zai bari su yi aikin su ba? Hannu jami'in ya kai a jikin Aisha kawai ya finciko gyalen nata, hakan yasa gyalen biyo hannun shi ɗan kwalin ta kuma ya faɗi ƙasa saboda irin ɗaurin nan ne na Zarah buhari, kuma gashi duka ta ɗora gyalen har saman kan...
*Alhamdulillah.*
29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
*RUBUTACCIYA*
👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
_NA_
*SAMIRA HAROUNA*
_SADAUKARWA GA_
*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_
_Bismillahir- rahamanir-rahim._
*18*
Shi kishi ya kan ziyarce ka ne kawai akan wanda kake tsananin so da ƙauna, haka kuma kana iya yin komai dan kare mutumcin wanda kake so. Irin hakane ya faru ga Sa'ad, shi kan shi bai san lokacin da ya ɗauke jami'in nan da mari ba duk da kuwa a cikin kayan aikin shi yake, a lokacin da idanun shi suka rufe bai hango girman hatsarin dukan jami'in dake bakin aiki ba, shi dai kawai ya ga ƙato ya yaye hijabin dake ɓoye masa *sirrin shi* yake kuma tayashi kare *mutumcin shi* a gaban shi, hakan yaa ya ji kenan ma jami'in ya raina mishi wayo? Kenan ma bai ɗauke kasancewar shi tare da ita a bakin komai ba? Bai hango cewa shi ɗin yana nan ne dan kawai ya *bata kariya* ba?
Bayan ya kashe fuskar jami'in da mari a sukwane shi ma cikin zafin nama bayan ya dafe kumci ya yi kan Sa'ad hannun shi sama da niyyar ramawa duk da yana da tabbacin idan ba'a yi gaggawar raba su ba tsaf zai sha wahala dan Sa'ad ya fi shi komai, bayan tsayi da kaurin jiki da ƙwanji, har da kazar-kazar ma na cikakken ingarman doki.
Cike da neman jaraba ido rufe Sa'ad yayi ram da duka hannayen jami'in bai yarda ya taɓa jikin shi ba ma bare ya mare shi, hakanne yasa suka kaure da kiciniya a wurin kamar wasu ƙananan yara, tuni hankalin jama'a ya fara dawowa kan su, inda masu tafiya suke tsayawa dan ganin ƙwam, da ƙyar aka raba su inda Sa'ad ke ta maimaita kalmar "Ba dan ka ɗaukeni ɗan iska ba, ta ya za ka cire mata tufafi? A gidan ku ba mace ne? Ko bishiya aka girgiza ka faɗo ne da baka san kimar mace ba? Kai ba namiji bane? Ba ka san ya mutum ke ji idan an taɓa masa mutumcin sa ba, idan binciken zaka yi ka sa ƴar uwar ta mace mana kada idan zan damu, amma haka kawai zaka saka ƙazamin hannun ka ka cire mata tufafi."
Cikin tafasar zuciya da baƙin ciki jami'in nan yace" Ni dai ka mara ko? Wallahi za ka gani, za ka gani nake faɗa maka, kuma na gane fuskar ka."
Cike da shaƙiyanci Sa'ad yace" Ka gane fuskata? Wai da baka shaidani ba ma? Bari ka gani..." Ya faɗa yana saka hannu aljihu ya ciro katin shi tare da cilla mishi yace" Katina ne wannan, cikakken sunana da sunan ubana da inda nake zaune duka yana nan, idan kuma baka iya karantawa ba to ka ji da kyau, *Sa'ad Ibrahim tela* nake."
A fusace ya zagaya ya samu Aisha tsaye duk tayi sanyin da ta kasa motsawa ko kaɗan, to ita bata ma san me za ta ce ba, Sa'ad yayi abun da ya saka ta tunanin to ko dai da gaske *son ta* yake kamar yadda kwanan baya Leila ke faɗa mata saboda kwanakin da ya dinga bata kulawa, sannan da bakin shi ya ce zama tare da ita shine abinda ya fi mishi komai a yanzu, ga kuma irin wannan dambatuwa da ya yi duk saboda ita, Gaskiya ko da tana da ƙaracin shekaru ai za ta fahimci akwai soyayya a nan. Dake ran shi a ɓace yake yana zuwa kusa da ita dama ƙofar motar a buɗe take, dan haka ya ɗan ɗora hannun shi a damtsen ta ta hanyar tura ta cikin motar sannan ya mayar ya rufe kawai ya shiga ya tayar suka bar wannan taron ana ta maganganu a kai, sai dai dayawa mutane da suka fahimci jami'in ne bai da gaskiya sai kawai Sa'ad ya birge su matuƙa, inda jarumta da ƙarfin halin shi suka sake ɗaɗasu a ƙasa duba da saida ya bar ma jami'in masaniyar da zai gano shi a sauƙaƙe tunda ya san yana da gaskiyar shi.
*Muje* da sauri, kun san dole Mama za ta yi magana, tayi faɗa, tayi bala'i, tayi kumfar baki kamar za ta ci Sa'ad, amma lokacin idanun shi a rufe suke, bai tanka mata ba yana dire su gida ya sake tuƙa mota ya yi wani wurin, bai kuma dawo gidan nan ba saida ya tabbatar da ya salwantar da wannan kayan mayen da aka ciro daga cikin Aisha, rame yayi mai zurfi sannan ya banka musu wuta sannan ya tafi. Da sassafe sammaci ya ziyarce shi na marin jami'in nan, sai dai da jami'in yasan abinda zai faru da bai shigar da ƙarar ba, dan daga abinda Sa'ad ya faɗa ya haɗasu kuma da bakin shi ya tabbatar aka bashi rashin gaskiya, amma dan sulhunta babban jami'in ya ma Sa'ad kashedi da kiyaye saurin dukan, sannan ba za'a ci shi tara ba dan an so tozarta *iyalinsa* ce kamar yada ya faɗa musu yanzun da aka zo ana bibbika zancen, sai dai dole ya bashi haƙuri, tsaf ya murje ido ya kalle shi yace "Zan bayar da haƙuri, amma sai shi ma ya fara bata haƙuri."
Lallaɓa shi jami'in yayi dake sulhu yae so suyi ya fara bashi haƙuri sannan shi ma aka kira Aisha ya ce tayi haƙuri, daga haka aka kashe wannan matsala ta zo ƙarshe. Sai dai DG bai haƙura ba dan baiyi nasara a karan farko ba, wani shirin ya shiga tsarawa wanda ya san da wuya Sa'ad ya tsallake shi.
*Bayan Kwana Biyu*
Yamma lis ya dawo gidan a matuƙar gajiye da kuma yunwa, dake nan yake cin abinci da gaggawa Aisha ta gabato mishi da abinci tare da abun sha mai sanyi ta aje mishi, har ta juya da niyyar ta bashi wuri dan tun da yayi faɗan nan da take dangantawa da a kn ta yayi shi ta ƙara jin kunyar shi na rufe ta, ɗaga idanun shi yayi yace "Karɓi?"
Juyowa ta fara yi sannan ta dawo baya kaɗan ta rusuna, wata dalleliyar waya dake kan tebur ɗin ya ɗauko ya miƙo mata yana faɗin "Duba ki ga ta miki kyau?"
Hannu biyu tasa ta karɓa tana duba wayar da son gane me yake nufi? Jin bai ce komai ba yasa ta cewa "Tana da kyau."
Sai kuma ta miƙa mishi dan bata tunanin ita ya ba, hakan yasa ya kalle ta yace "Ta ki ce, idan kuma bata miki ba ki faɗa a canza."
Da mamaki tace "Ta wa?" Jinjina mata kai yayi alamar e, ƙara kallon wayar tayi sai tayi murmushi ta sunkuya tace "Nagode, nagode sosai, Allah ya saka da alkairi."
Bai ce mata uffan ba har ta juya za ta koma ciki, da sauri kuma ta dakata saboda jin jiniyar mota kamar irin motar gwamna haka na shigo cikin gidan, shi kan shi Sa'ad mamaki ya sa ya kalle ta yace "Su waye?"
Ɗaga kafaɗa tayi da taɓe baki kaɗan tace "Ban sani ba nima."