← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 168

Sashe 59

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana gama faɗa ta juya a fusace ta bar falon, saida ta ɓacewa ganinta ta sauke ajiyar zuciya, Shiyasa ta fi ƙaunar Hajia Asiya, dan ita bata da hayaniya, ita idan Kaga ta shiga harkar Ummu to kawai an taɓa ta ne, bare kuma yanzu da tsufa ya zo mata mutumci kawai suke, amma shine har Hajia Atika take faɗa mata wai ta ji tsoron Allah, to ita me take yi da ya saɓa? Alhaji bai taɓa yi mata abu bai musu ba, bata taɓa yarda an tauye wata a dalilin ta ba, idan ya tashi tafiya yana ɗakin ta ne duk abu nashi muhimmi ya kan aja a ɗakin ta, idan ma ɗakin wata tafiyar ta kama shi ya kan ba wacce yake wurin ta ne, to ina kuskure a nan? Maganar yaran su kuma da take idan suna son abu, a iya sanin ta Zeinab ce kawai da ta sa kanta kasuwa tana son kuɗi masu yawa, kuma ita da Zeinab kamar ƙawaye ne, zata iya cewa ma sun zama ƙawaye kuma aminai shine ta sanar da ita ta ce ta faɗawa abban, dan tana tsoron ya hana ta, kuma da Ummun ta faɗa sai ya amince har ya bata jarin wanda yanzu take fantamawa abun ta, to ina matsala anan Shima?

Wayar da Kuwailat ta kawo mata ta ɗauka tare da gyara zaman ta dan shiga WhatsApp ta ga yau wace wainar a ke toyawa a daɗaɗɗen grp ɗin su mai tarihi da ya kwashe shekaru har yau ana damawa a cikin shi wanda dalilin shi abubuwa dayawa sun faru kuma an ƙaru da mutane dayawa sannan an buɗe wasu grp ɗin.

******************

Da sallama a baki Fa'iza ta shigo falon tare da mahaifiyar ta a bayan ta, da sauri Yaya Bilal ya kalli ƙofar saboda sanin muryar wacece, ai kuwa fuskar ta ya kafe da kallo kamar yau ya fara ganin ta, ko da yake kusan hakane, shekaru kenan da dama da suka wuce tunda ta tafi ta ƙi dawowa, su Hajia sun je bikon kan ta dawo amma ta ƙi ta ce sai ya zo da kan shi, shi kuma yana ganin ai shi ta ɓatawa rai sannan kuma iyayen shi sun je, a ƙalla ta fi shekara uku wajen Yayanta dake aiki a Moscow, ba ma wannan ba fa, labari da ya samu wai makaranta ta koma da auren na shi. Ita fa Fa'iza bata ciki da rainin hankali ne, kuma bata ciki da ƙalubalen wahalar zaman aure, idan zai yiwu kawai a yi, amma tayi yaji ya ƙi biyo ta kuma a haka yake so ta dawo? Sam ba zata iya wannan ba.

Har suka zauna bai daina kallon ta ba tana gaisawa da su Hajia da kuma Alhaji dake kwance wanda kwna biyu kenan baya da lafiya, saida t gama gaisawa da kowa kafin ta kalli inda yake, yana nan yadda yake, ko rashin yara dayawa ne yasa baya tsufa? Oho! A taƙaice tace "Y mai jikin?"

Shi ma da ya kasa daina kallon ta ganin kamar yadda ta fita daga gidan zaka rantse shekaru basu ƙaru a kan ta ba yace "Da sauƙi, yaushe kika dawo?"

Saida yayi tambayar sai kuma ya gane ba anan ya kamata ya mata tambayar ba, ba tare da ta daina kallon shi ba tace "Sati kenan da na dawo."

Jinjina kai yayi da irin yanayin nan na yayi kyau hamshaƙiya sannan yace "Da kyau, an sha karatu?"

Da fara'a a fuskar ta kamar mai son ƙular da shi tace "Umm wallahi, yanzu haka ma ina neman aiki ne a babban banki, kuma na samu hanya in sha Allah ina sa ran zan samu."

Wani shegen kallo ya mata irin _"Ke dai kika sani É—in nan."_ Kafin ya É—auke kan shi, jim kaÉ—an suka kalli juna ita da Maman ta tace" Mu tafi ko?"

Kallon ta Hajia tayi tace" Fa'iza, kin dai ƙi dawowa gidan ki ko? Hajia..." Ta faɗa tana kallon Maman Fa'izan tace" Kun ƙi ku sa baki ta dawo gidan ta?"

Kallon ta duk sukayi sai maman Fa'iza da tayi murmushi dake irin matan nana ne ƴan boko sosai tace" Ba haka bane Hajia, ita ta ce ba zata dawo ba sai ya je da kanshi yana son ta dawo ɗin, to kuma Kinga bai je ba, kenan ba ya da buƙatar ta ne a gidan shi?"

Wallahi kunya ce sosai ta kama Yaya Bilal ya sadda kanshi, kallon shi Hajia tayi tace" To ka ji, ban an har yaushe kake so mu ci gaba da zuwa yi maka bikon mata ba, alhali kai kuma ba yaro ba."

Sabeer dake tsaye É—auke da Æ´ar shi a kafaÉ—a tana bacci wacce it ce Æ´ar shi ta uku, dariya yayi yace" In sha Allah zamu je tare da shi Hajiyoyi, yau sai ya je munyi bikon auntynmu."

Murmushi kawai Fa'iza tayi tana kallon Sabeer tace" Sabeer, zan dawo ko bai zo ba, dan akwai aikin da nake so na kammala a gidan nan, amma fa sai na cika burina na zama ma'aikaciyar da zan iya tsayawa da ƙafafuna, ta hakane ko Allah ya sake ƙaddara ana rabuwa ba za'a min gorin ban rasa komai ba anan sannan ayi tunanin na rasa wani abu a can ɗin."

Idanun shi ya ɗago ya kalle ta lokacin da ta juya dan fita daga falon, sai kuwa Abida ta shigo da sauri tana riƙe da hannun yaron ta wanda Yaya Bilal ya raɗa ma *Aslam* amma ita ta ce sunan nan bai mata ba ita *Aswan* take so, hakan yasa wannan lamari yin tsamarin da Abida ta sake fita a ran su, dan har yau ita Aswan tae kiran shi, dan kuwa tsaf tasa aka yanka mishi ƙatuwar saniya ta raɗa mishi wannan sunan, abubuwa fa sun faru a shekarun da suka gabata.

Irin murmushin muguntar nan Abida ta saki saboda ganin Fa'iza, a kullum kallon asararriya take ma Fa'iza wacce ba ta da rabo, da azama ta riƙo hannun Aslam dake gaba tana faɗin "Dakata mana, zo ka gaishe da auntynka."

Hajia da ganin Abidar ya sa ta kawar da kai haka ma Sabeer da ya bita da harara, Yaya Bilal kuma tuni ya maida hankalin shi ga Aslam yana mai matsuwa da ya ƙaraso wajen shi ya rumgume shi ko ya ji sanyi a ran shi, Abida kuma cike da izgilanci ta turo Aslam gaban Fa'iza kaɗan tana faɗin "Ga ɗan naki."

Murmushi Fa'iza ta mata irin na babba da yaro sannan ta shafa kan yaron tana kallon shi har da ɗago haɓar shi tana faɗin "Ma sha Allah, Aslam ne zan ce ko dai Aswan?"

Sai kuma tayi murmushi tace "Ko da yake dama ai kai ɗin ɗan Maman shi ne, da Abbun ka ya fahimci haka da tuni ya jefar da ƙwallon mangwaro ya huta da ƙuda."

Da ƙarfi Abida ta jawo hannun Aslam tana mai hararan Fa'iza tace "Matsalar ki kenan, ba damar a haɗu da ke sai kin yi zaurencen d za'a kasa gane ki."

Raɓata tayi za ta wuce Fa'iza ta bita da kallo tana faɗin "Hmmmm! A juri zuwa rafi dai, da sannu tulu zai fashe."

Sabeer dake ƙufule da Abida kallon ta yayi yace "Me ye abun da ba'a ganen ba a maganar ba? Hausa ga ta yi."

Kallon shi tayi fuskar ta a haÉ—e, magana ta gaskiya ta jima da fahimtar akwai canji da zaman ta da mutanen gidan nan, yadda suke da yanzu ba haka suke ba, ba ta san me yasa ba, kuma bata so ta sani tunda mijin ta dai suna zaune lafiya, sannan yana bala'in son É—an ta, dan haka bata da matsala da wannan, ba tare da ta saki fuska ba tace "Hausa ta yi, amma ai da lauje cikin naÉ—i a hausar ta ta."

Wani malalacin murmushi Sabeer yayi yace "Hmmmm ! Dama ai idan da laujen cikin naÉ—i sai mutum ya ji ya tsargi kan shi."

Da mamaki yanzu ta dube shi jin kamar akwai abinda yake nufi da ita tace "Tsarguwa? Tsarguwa fa ka ce Sabeer, wace irin tsarguwa kuma kamar wata wacce ta aikata laifi?"

Saida ya bita da shashashan kallo sannan yace "Kusan haka." Yana faÉ—a ya É—auke kan shi, da wani mamaki ta sake kallon shi tace "Ban gane me kake nufi ba Sabeer? Ya kake magana kamar kana son faÉ—in wani abu."

Kallon ta ya sake yi yace "Ina nu..." Da sauri Hajia ta katse shi da "Sabeer kana lafiya wai?"

A ldabce ya kalli Hajia yace "Kiyi haƙuri Hajia."

*ME CE CE DAMUWAKI*?

Rashin ni'ima?
Rashin gamsar da mai gida?
Warin gaba?
Bushewar gaba?
Zubewar nono?
Cikowar nono ?

*Kina buƙatar...*

Fatarki tayi laushi?
Tayi santsi?
Ta kwanta luf?
Kina walkiya da annuri tamkar amarya?
Sabulu kike so ko haÉ—in shafawa ki wanke ko mai na shafawa?
Ki wadatu da sahihin ƙamshin haukata mai gida?
Humra da zaki saka mijinki bacci bai shirya ba?
Humra da zata tayar da sha'awarsa?
Kulaccha da zata saka mijinki ya kasa yi miki tsara a fannin ƙamshi?
Kulaccha da zata gagari manyan mata suffanta kalar sunan turarenki?
Turaren wuta irin na asali barebari?
Turaren da zaki fesa à zanin gadonki har ya rike mai gida ya kasa tashi?
Turaren da zaki zuba ga ruwan wankan mai gidan ki?
Turare don yaranki?

_Idan duka kina buƙatar ɗaya daga cikin kayan nan, to ki tuntuɓi wannan lambar ta WhatsApp *+227-82-21-91-74* wanda suk gwada sun san ingncin kayanmu, ba buƙatar ɓata lokacin cika muku baki._

Wani abun farin ciki kuma, duba da yanzu ba kowace mace ke son shan garin magani ko matsi ba, akwai haÉ—i irin su *tsumi*, *ruwan tsumi*, *tukunya*: dayawa sun san tukunya, don da itace muke tutiya, kuma tukunyar nan akwai na ruwa dana dafawa a nama, sannan akwai kankat wato haÉ—in *kayan marmari*.

*Garaɓasa*

Ga waÉ—anda sukayi nisa kuma haÉ—in kayan marmari ba zai kamacesu ba, duba da kafin sakon yaje garesu zai fara lalacewa, don haka ga sauki ya samu, madadin kuÉ—in mota da zaki yi, zaki biya 1000k kacal don a sanar dake yadda zaki had, ba iya guda kawai ba, dama sauran haÉ—i irin na kayan daya shafi na marmari da É—anye, musamman ma *sirrin kankana* da kuma *cucumber*.

*JANNAT HOUSE.*🧕
Chapter 59 · 0% Book details