Sashe 154
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata
Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_
_Bismillahir- rahamanir-rahim._
*71*
Nan su Aisha suka same ta sukayi ban kwanan cike da kewar junan su, duk da Aisha na mata sharrin wai dattijo ne ashe ya hanata fita tana ta faman girki, haka dai suka rabu tana hawaye cike da kewar ƴar ta duk da kuwa a jita-jitan mutane ita ma ba da daɗewa ba za ta same su can. Ana sallah la'asar ta kammala girkin ta aje kan teburin nan sannan tayi wanka tayi sallah, ta ɗauka zaiyi irin dawowar nan ta jiya, amma haka tayi ta zama a falon har magriba tayi sallah, wasa wasa sai gashi har ƙarfe 09:00 tayi bai shigo ba.
KaÉ—aici ne ya dame ta har ta ji zuciyar ta na raya mata _"Ya zo gidan mana ko masifa ce ma muyi."_
Sai kula ta ja tsaki tana faÉ—in" Ke dallah! Dukan ki fa ya yi É—azu."
Sai kawai ta tashi ta shige ɗakin ta tare da saka makulli ta rufe ta yi kwance ba dan bacci ba, ba ta fi minti biyar ba sai ta ji an murɗa hannun ƙofar, amma dake rufe take sai ba'a shigo ba sai ma aka ƙwankwasa, zaune ta tashi tace" Wa ye?"
Duk da kuma ta san shine dai a wannan lokacin, shiru yayi tare da sake ƙwanƙwasawa, tasowa tayi a kasalance, har ta kawo bakin ƙofar da sauri kuma ta juya ta ɗauko dogon hijabin ta na sallah ta saka da tunanin ko da almatsutsan ke motso mishi ya dake ta da wayar ɗazu to hijabin zai rage mata raɗaɗi, tana buɗewa suka haɗa ido sai kuma ta kawar da nata tana jira ta ji me zai ce.
Muryar shi ba yabi ba fallasa ta ji yace "Me ya sa kike son tambaya ta wa ye?"
Ba tare da ta kalle shi ba tace "Saboda duniya ce muke ciki yanzu ba kyau, a gidan ka ma É—auke ka ake yi."
Taɓe baki yayi ya juya yana faɗin "Abinci zan ci."
Inda yake tunanin wane shaƙiyi zai zo gidan shi ya ɗauke mishi Maama ne? Wato ba'a so ƙasa ta zauna lafiya kenan? Ko da yake wai me ya sa ma ya damu ne haka?
Ummu kuma da kallo ta bi bayan shi, wallahi ƙirar shi ma a nutse take kamar fuskar shi da muryar shi, amma sai abubuwa yake yi wanda da zai dawo hayyacin shi a faɗa masa ya yi su sai yayi ta istigfari duk da ba laifin shi bane. To yanzu da ya faɗa mata me za ta mishi? Hmmmmm! Taɓe baki tayi tare da ƙoƙarin jawo ƙofar ta rufe in ya so a yi wacce za'a yi, sai kuma ɗisssssss! Ta tuna bulalar ɗazu, musamman ma ta biyun nan da ta hau bayan ta sosai, da sauri ta fita ba tare da ta rufe ƙofar ba saboda tunawa ai dama masu larurar nan ɓacin rai ne basu so, to za ta bishi *sau da ƙafa* har su rabu lafiya.
Yadda ta same shi zaune yana danna wayar shi ya nuna mata abinci yake so ta zuba mishi kenan? Duk da ta aje komai har da lemun da tayi na lemun tsami yana frigde, a ɓoye ta girgiza kai a zuciyar ta tana faɗin _"Allah ya shirya ka shirin addinin musulunci."_
Cikin nutsuwa take zuba mishi abincin har Jabir da ya ƙurawa hannayen ta da suka mishi kyau idanu yace" Ya isa haka."
Dakatawa tayi ta zuba miyar da duk wani kayan tsirfa da tayi, lemun ta É—auko cikin jug da kofi, tana zuwa ta tsiyaya msa sannan ta kama hanyar komawa É—akin ta, a dake yace" Zo ki zauna?"
Ba musu Ummu ta dawo ta zauna ko fuskar shi ba ta yarda ta kalla ba inda take ta wasa da hannayen ta dake cikin hijabin ta, wayar shi ya dake hannun shi ya miƙo yana jawo farantin sosai gaban shi yace" *Saka min lambar ki* Maama, ba zan juri ƙwanƙwasa ƙofar nan ba kullum."
Da mamaki ta tsare shi da idanu ta kasa karɓan wayar, jin shiru ba ta karɓa ba ya sa shi ɗan kallon ta, da sauri ta zura hannu ta karɓa ta saka mishi lambar sannan ta miƙo mishi, cikin wata irin nutsatsiyar muryar da saida Jabir ya kalle ta da sauri saboda rabon da ya ji amon muryar nan tun tana *gidan Abba* tace "Zan iya tafiya?"
Murmushi ya sakar mata saboda wallahi sai ta kashe mishi jiki tare da bashi tausayi, wannan ita ce maaman shi, wannan ita ce maaman shi da ya sani mai nutsuwa da hankali, dan haka ya kai lomar farko bakin shi bayan bismillah yana girgiza mata kai alamar a'a, saida ya gama taune na bakin shi sannan ya kalle ta yace "Maama, abincin nan ya yi daɗi sosai, kin iya girki maama, da wannan naje ƙara godewa Allah da ya *bani ke*."
Ba ta da ta cewa a lamarin na Jabir, sai dai a haka ta bishi da irin kallon hangen nesan nan cikin tattausar murya tace "Jabir, me ya sa kake min duk abubuwan nan? Bayan nasan dole akwai wata manufa a aurena da kai."
Kallonta shima yayi yana cin abincin shi a nutse yace "Me ya sa kikayi wannan tunanin maama?"
Cikin yanayin jin haushi tace "Da fari dai ka daina kirana da sunan nan na Maama, tunda kaga ai babu wani abu da kake yi da ya nuna kana girmamani yanzu."
Murmushi yayi da har saida haƙoran shi suka bayyana har ta ɗan shagala da kallon shi sannan ya jinjina kai yace "Ok, idan na ce *ƴar ma'aiki* ya yi? Ko kuma nace *Kulsum*?"
Da mamaki ta kalle shi tace "Kuma zaka iya cewa Kulsum É—in ba tare da ka ji kunya ba?"
Cike da tabbaci ya É—aga mata kai sannan yace "Sosai ma, to ba matata bace."
Jinjina kai tayi tace "Shikenan."
Kallon ta ya sake yi yace "Me ya sa kike tunanin akwai wata manufa a auren mu?"
Ba tare da ɗar ba tace "Saboda yadda muke da kai, da kuma yadda kuke da Alhaji, wataƙila ya sa ka aure ni ne saboda bai so na aure wani daban, amma kai idan ka aure ni zai zama ikon sarrafani yana hannun shi, sannan..."
Sai kuma ta ɗan lashe leɓen ta tare da sunkuyar da kai saboda kunya, zuba mata idanu yayi alamar yana sauraren ta, saida ta ɗauki sakan din da ya fi sha biyar sannan ta ɗan ɗago tana kallon teburin dake gaban shi tace" Ka faɗa ya faɗa maka abinda ya rabamu, kenan kaga..."
Da sauri tasa yatsa biyu ta share ƙwallar da ta fara gangaro mata sannan ta haɗe wani abu mai ɗaci da ya tokare mata wuya sannan tace" Ka aure ni dan ka min abinda ya kasa yi min shi, Jabir shiyasa bana son auren nan, dan ni ta wannan fuskar nake kallon shi, saɓanin iyayena da Alhaji Kabir ya nuna musu kawai hallatar auren, Jabir, ni fa ba jahila bace, na san ba'a kaina aka fara ba, aurena da kai ta ko ina hallata yake yi, ƙwarai da gaske ina son ka dinga bani girmana na wacce ta baka shekara uku a duniya, amma son girmana bai kai ƙadamin da zan kasa yi maka biyayya ba matsayin ka na *mijina*, Nana Khadija (R.A) ta girmi Annabi da shekarun da suka ninninka nawa, amma ta mishi biyayya kuma sun mutumta junan su har ta koma ga Allah, ta zama macen da Annabi ke alfahari da ita, yake kuma jin ba daɗin rasata a lokacin da addini ya tsayu kan ƙafafun shi bayan gudummuwar da ta bayar, har Nana Aisha ta ce ban taɓa ganin hushin Annabi (S.A.W) ba kamar yadda ta ga fushin shi ranar da take faɗin ya daina damuwa da rashin Khadija tunda Allah ya musanya masa da wacce ta fi ta, amma Annabi ya ce ina! Hakan ba zata taɓa faruwa ba. Jabir da zan samu tabbacin kyakyawar niyyar ka ta aure na, me zai sa ba zan so zama wacce zata kafa maka kyakyawan tarihi ba? Bayan ni na fi kowa sanin ka sannan nasan irin wahalhalun da ka sha a rayuwar ka, da zan zamar maka baiwa ne wacce ka sa kuɗi ka siya, ta ɗaya ɓangaren kuma ai anyi auren Zeinab da Zeid, shima dan ubangiji ya mana togaciya da ƙin aikata kyakyawan aikin da zuciyar mu ke muradi ne, na sani ne ba ta yadda za'ayi ka aure ni alhalin Alhaji Kabir na raye, saboda kana girmama shi kamar shi ya haife ka, to ta ya zaka aure ni kuma?"
Ko da ta gama faɗin haka ta miƙe tsaye ta nufi wajen fridge ta ɗauko ruwa, ba ta kalli inda yake ba ta wuce ɗakin ta ta rufe sai dai ba da makulli ba ta sha ruwan nan sannan ta kwanya tana sauke ajiyar zuciya, ba ta yaarda da auren nan ba, ba kuma za ta yarda ba kawai ya sawaƙe mata, amma ba za ta ci gaba da zama da shi yana mata rainin wayo kala kala bayan ta san ba tsakani da Allah ya aure ta ba.