Sashe 65
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_
Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes
*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata
Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_
_Bismillahir- rahamanir-rahim._
*31*
Hajia dake zaune ce tace "Hakan na nufin Fa'iza bata da laifi kenan? Duk da muna kallon ta a mai laifi."
Da tabbaci Sa'ad ya kalle ta yace "Ƙwarai Hajia, mai laifin dai wannan ce..." Ya faɗa yana nuna Abida da tunda Yaya Bilal ya mata tsawa tayi shiru, yanzun ma shi ya kalle ta yana girgiza kai yace" Kin yi asara wallahi, da zuciya ɗaya na karɓi auren ki lokacin da mahaifin ki ya bani *sadakar ki*, amma wai ke ce zaki saka mana da haka? Lallai mutum mugun ice."
Zaune yayi kan kujera tare da ciro wayar shi yana faɗin" Na rantse da Allah idan uban ki shugaban ƙasa sai ki ɗauru a garin nan, dan ba ƙaramin tashin hankali kika jefa mu ba."
Da sauri Hajia ta rufe baki saboda zagin da yayi ta san ya hau sama ne, ba wanda yayi yunƙurin dakatar da shi dan gaskiya Abida ba irin wanda za'a tausaya ma bace, duk sun yi shiru suna sauraren Yaya Bilal na waya da abokin shi dake jami'in tsaro, ba zato ba tsammani suka ji ƙarar mari a fuskar mutum mai rai da lafiya. A gigice Abida ta dafe kuncin ta, kafin ta ankara Mamie ta sake kashe fuskar ta da mari, ba ta bata damar dawowa hayyacin ta ba ta shaƙi wuyan ta a zafafe tana faɗin "Makira azzaluma, ashe dama ke maciya amana ce? Na yarda dake ban taɓa zargin ki akan abinda ke faruwa dani ba, kina shiga sha'anina fiye da Fa'iza, hakan yasa nake ganin kamar ita ce macuciyata, ashe duk makircin ki ne, me na miki? Me yasa kika ɗauke min yarana?"
Da sauri Aisha ta shiga ƙoƙarin ɓanɓare Maman ta, Abida na jin ta saki wuyan ta da gudu ta ƙarasa kusan Alhaji ta durƙusa tana faɗin" Alhaji, Abbu, Abbu dan Allah ka min rai, wallahi sharrin sheɗan ne, ban da tunanin komai a kaina saida Abbana ya sa na shigo gidan nan matsayin mata, dan Allah ku yafe min Abba na tuba, wallahi zan gyara kuskure na."
Wani kallo Alhaji ya mata, duk da yana jin jikin shi ba daÉ—i, haka ya daure yace mata" Me yasa kikayi haka Abida? Mun yarda dake fa."
Cikin kuka sosai tana share hawaye tace" Abbu Babana ne, duk laifin shi ne wallahi, shi ya nuna min kar na yarda wata ta rigani haihuwa, hakan zai sa kima da darajata su zube sannan zan kasa samun soyayya, sai kuma na ga hakan bayan haihuwar Nuriyya, shine da fari ya É—auke Kuwailat, amma kuma hakan bai sa na samu ciki ba, kafin mu ankara ta sake samun cikin Eesha, ban yi wani tunani ba a lokacin kawai na ga mu sake É—auke yarinyar, kuma..."
Saida ta kalli Fa'iza dake tsaye tana kallon ta a wulaƙance sannan tace" Na fahimci Fa'iza bata da faran-faran da shiga al'amura kai tsaye, sai nayi anfani da hakan ta hanyar saka Rabi ta ɗauke Eesha ta goya a cikin da duk kuka ɗauka tana da ciki sannan ta bar gidan, bayan shi ban yi komai ba wallahi, dan Allah ku yafe min."
Cikin zafin nama Mame ta tintsire Abida saida ta kusa kai wa Alhaji karo t'a faɗin" Ƙarya kike munafuka, sau nawa ana tsorata ni gidan nan? Daga na ji kukan jarirai sai na ga tv da hotunan yarana, har ban ɗaki idan na shiga ina fitowa zan samu hotunan su Eesha zube a kan gado, kina so ki ce ba ke bace?"
Cikin shasheƙar kuka Abida tace "Na ji na yarda ni ce, i ce wallahi, Abba dan Allah ka ce kar ya kira jami'ai, Abba ɗaure ni zasu yi wallahi, bana son zaman maƙargama."
A kausashe matuƙa Abbu Mukhtar dke kallon ta yana son saka mata hannu amma yana tsoron abinda zai iya faruwa yace "Kenan da nufin ki ki haukata ta ko me?"
Shiru tayi ba tace komai ba dan gaskiya abinda ta so kenan, shiru aka yi ba wanda ya sake magana na wasu wasu mintuna har suka ji ƙwanƙwasa ƙofa, da sauri Yaya Bilal ya kalli Sabeer da duk abin nan da. Ak e bai ce komai ba kuma matar shi ma bata wurin yace "Ce su shigo."
Da sauri Sabeer ya ƙarasa ya buɗe musu ƙofa, jami'i biyu ne sai mace ta ukun su, suna shigowa ya nuna mishi Abida fuskar shi a haɗe yace "Gata nan Mansur."
Jinjina kai Mansur ɗin yayi tare da ɗan waigawa ya kalli jami'a macen nan, gane yaren shi yasa ta tunkarar Abida da tuni ta sake ruɗewa ta rarrafo ƙafafun Yaya Bilal tana faɗin "Dan girman Allah Bilal kar ka bari su tafi da ni, na tuba, na tuba Bilal, Haba Bilal ya zaka min haka? Ka min dan girman Allah, wallahi ba zan ƙara ba, ka tausaya min Bilal ko dan Aswan dake tsakanin mu."
Ba wanda ya saurare ta har jami'ar nan ta ji haushin yadda Abida take riƙe carfet har tana neman gaggaɓoshi daga inda yake ta finciketa da ƙarfin bala'i, jan ta take yi a ƙasa dan ta ƙi tashi ko zaune bare tsaye, ba sunan wanda bata kira ba a wurin har da Sa'ad kan shi, amma kowa da idanu yake bin ta yana tsaki da taɓe baki, wahala ta kai mata karo, yanayi ya ɗimautar da ita, gashi har yanzu janta ake kamar wata dabba ana gaf da fita da ita, cikin tsananin ƙunar zuci da ɓacin rai da rufewar ido haɗe da lokaci idan ya zo na abu to ba makawa sai ya faru, ta mance da me ke fitowa daga bakin ta, ita dai kawai tasan ranta ya ɓace na ganin dukansu suna kallo ana mata wannan wulaƙancin, ai ko me ta yi za su iya taimaka mata a tona mata asirin asirrance, hakan ya tunzura ta take faɗin "Tirrr daku wallahi, dukanku sai naga bayan ku, kun ji haushin duniya wallahi, kuna kallo ana min wannan wulaƙancin, har kai Alhaji dake Tsoho, Tirrr da halin ku marasa imani kawai, dukiyar ku ta banza? Nima zan yi kuɗin kuma sai na wulaƙantaku a duniyar nan, banzaye azalumai, kai kuma Bilal..."
Ta Kira sunan shi har da juyowa tana kallon inda yake zaune tare da ƙoƙarin tashi da tayi tsaye tana ci gaba da faɗin" Ka ji haushi wallahi, banza lusarin namiji, ka je ka tuntuɓi likita su gaya maka gaskiyar magana ita ce baka haihuwa, kar ka saki ka ɗauka *ɗana* ɗanka ne, wallahi baka haihuwa kuma ba a banza Allah ya hana ka haihuwa ba, dan baka tausayin mace ne a rayuwa..."
Tunda ta ambaci ba ya haihuwa ya tashi a zafafe yayi kan ta, rufewar da idanun ta sukayi yasa ba ta ma ga yana tunkarar ta ba saida ta ji shaƙar da ta ruɓanya wacce Mama Nuriyya ta mata, dan kuwa wannan tsaf ta ji numfashin ta ya ɗauke ta inda ta tabbatar idanun ta sun fito waje, ba ta ji tambayar da shi yake mata ba sai ƙoƙarin ɓanɓareta da jami'an ke yi daga hannun shi suna bashi haƙuri, sai lokacin ta ji yana faɗin "Ku sake ni na kashe ta na kashe banza, ɗan waye Aslam? Na ce ɗan uban waye?"
Kallon shi tayi duk da tana ganin shi hazo-hazo haka ta dage da ƙarfin guiwa dan ta ga Shima hankalin shi ya tashi, to Gwara a yi mutuwar kasko kawai kowa ya ji ba daɗi, cike da dariyar mugunta tace" Ba banza za ka kashe ka ba Bilal, Abida za ka kashe wacce ta kafa maka tarihi, Aslam ba ɗan ka bane, kuma ka sani na raina ka ne tun ranar da Hashim ya min cikin da kai ka kasa yi min."
*Hashim*! *Hashim*? Hashim ! Tangal tangal yayi baya zai faɗi da sauri Mansur ya riƙe shi, da sauri Sa'ad da Sabeer suka nufe su tare da riƙo Yaya Bilal da idanun shi biyu amma dai baya da maraba da wanda ya shiga duniyar suma. Zaunar da shi sukayi inda aka ƙarasa fita da Abida kowa na wurin jikin shi ya mutu tare da sake tsanar Abida, an ɗauki lokaci kafin Yaya Bilal ya ji abinda ya tokare mishi zuciya da maƙoshi ya ɗan sake shi, duk da girman shi haka ya fashe da wani irin kuka na takaici da dana sani haɗe da nadama, cikin kuka yake faɗin "Rashin haihuwata na Allah, Ubangiji ne ya nufe ni a zama haka, kula ko da gaske ne wannan matsalar daga ni ne, ban jin zan damu kaina dan ba ni na ma kaina ba, amma a ce kamar ni mata ta ta haɗani neman ta da wani sakaran ƙaramin yaro."