← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 146 OF 168

Sashe 146

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dama dai a tsakiyar Hajia Mamie da Hajia Mammie take, dan haka Hajia Mammie da tafi zafi ta kai hannun ta daidai bakin Ummu, sai kuwa ta runbusta mata shi wanda ya bayar da sautin bupppp! Da sauri ta dafe bakin ta tana kallon ta cikin wani irin yanayi na ɓacin rai, dama ita fa ba ƙaunar tsohuwar nan take ba duk da ta haifa mata uwa, bare kuma yanzu da suke neman tado mata aljanun ta ma. A ɗan hassale ta gyara alkyabbar ta tana ja baya da niyyar komawa wajen Abbun ta da ta san zata fi jik daɗi, dan Hajia Mamie ma dai ba wani gane wa juna zasuyi ba, uwa uba kuma Mama da zata iya marin ta ita ma, ganin haka ya sa Hajia Mammie ɗin nuna mata inda ta tashi tace "Ke dawo nan? Maza zo zauna nan."

HaÉ—e fuska Ummu tayi ta girgiza kai tace "Mammie dan Allah ki É—an dakata, Abbu ne zan tambaya, na san shi ba zai min wasa ba ai."

Yunƙurawa Hajia mammie tayi zata tashi, da sauri Abbu ya musu alamar su zauna tare da kallon Ummu yace "Ummu, koma ki zauna."

Ba dan taso ba ta matsa ta zauna, Abbu ne yace "Ummu, da gaske ne abinda kika ji, jiya auren ki da Jabir aka É—aura ba da Jibril ba, ga Abban Kuwailat nan, shi ya nuna mana alfanun haÉ—a ku, bayan haka kuma muka gano matsalolin dake tattare da auren ki da Jabir, shiyasa muka yi hakan ba da izinin ki ba saboda tabbacin da muke da na zaki yi mana biyayya, ko ba zaki iya ba?"

Kallon Abbun take yi da wani irin yanayi inda hawaye suka fara yi mata zarya a fuskar ta da babu kwalliya, girgiza kai take yi a hankali kafin tace" Abbu, ya zaku min haka dan Allah? Abbu wane Jabir kuma? Abbu ni da na yarda zan auri Jibril ne saboda kawai na tausaya masa, amma ba dan ina so saboda ya min ƙanƙanta a shekaru, ta ya kuma za'a haɗani da ƙasa da shi? Haba Abbu kun min adalci kenan? Idan Jibril yana da matsala a fasa auren mana, sai na samo wani mijin ko? Amma baa haɗani da duk wanda aka gani ba kamar dai a matse kuke da nayi aure na bar muku gidan ku, Allah yana gani ni bana son wannan auren, ƙwarai ina so na mutu ɗakin mijina, amma dai yaro kamar Jabir da kuma shi kan shi Jabir ɗin, to gwara na tabbata babu aure saboda bana son harkar raini wallahi."

A ɗan zafafe Mama ta ɗaga hannu kamar za ta buge ta, hakan yasa Ummu runtse idanu amma bata gusa ba alamar ta ɗauko halin nan nata na kafuwa ba, sai kawai ta dakata dan tasan ko dukan ta zatayi yanzu zata ji mata ciwo ne amma tana nan kan bakan ta, dan haka ta sauke hannu ta a nutse tace "Ummu, magaganun ki sai suka min kama da na wacce bata taɓa zuwa makaranta ba, ya zaki bani kunya haka? Ina cike da alfaharin cexa na haɗaki da iyayen ki ban ba tare da naƙasu a tarbiyyar ki ba, amma sai ki dinga maganganu haka kara zube, me yasa? Me yasa Ummu?"

Fashewa tayi da kukan da ya sa ka Jabir ɗin muskuta ƙafar shi, shi dai ayi a ƙare dan Allah ya bar wurin nan, bai taɓa sanin Maama na da wauta ba sai yau, shine take kira yaro ɗin? To me ye aure wai? Ba ci, sha, tufatarwa, kula da addinin ta, ɗawainiya yayin tashin lafiya, sai kuma saduwa ba? Bayan wannan akwai wani abu ne da take ganin ba zai iya ɗin ba? Shiyasa har take kiran shi da yaro? Hammmmm!

Cikin kukan da ya saka Aisha jin kamar za ta fashe da kuka take faÉ—in "Abbu ku taimake ni dan Allah, wallahi ba zan iya zaman aure da Jabir ba, Jabir fa? Abbu yaron tsohon mijina ne fa, wallahi kamar É—a yake a gurin Abban Kuwailat, to ta ya za'a ce wai shi zan zauna da shi a matsayin miji, Abbu ba zan iya ba wallahi, dan Allah ku kwance wannan auren."

Hajia Mamie ce ta kalle ta tace" Hajia, ki saurare mu mana, ki dinga sanin me zaki faÉ—a gaban *mijin*, zo nan zamuyi magana?"

Ɗaga kanta tayi ta kalli Hajia jin ta ce wai gaban mijin ta, ya subhanallah! Me yasa iyaye suke hakane? Wane Jabir wai? Yaron da Eesha ma tana gaba da shi a shekaru? Ba zata iya ba gaskiya, ga shi ɗan tsohon mijin ta, ga shi ya rainata, gashi kuma ƙanin bayan ta ne, to da wane za ta ji a cikin ukun? Ita bata da matsala dan an ɗaura musu aure bata sani ba, amma dai waɗancen abubuwa a'a.

Ba zasu fahimce ta ba, dan haka ta yunƙura ta tashi tayi tako ɗaya ana biyu Hajia Mammie tace "Ke, gidan uban wa zaki je bayan magana muke da ke?"

A kasalance ta kalli Hajiar murya ƙasan maƙoshi tace "Mammi ba zaku fahimce ni bane, shiyasa zan tafi, kuyi haƙuri dan Allah."

Da sauri Hajia Mammie ɗin ta miƙe tsaye tana sake nuna mata wajen zaman ta tace "Zauna min nan malama, har wacece ke da zamu taru anan saboda ke amma ki tashi ki bar mu? Wato mu ga banzaye da basu da kima da daraja ko? To koma ki zauna min nan maza malama, idan ba haka ba ranki ne zai ɓace."

Saida ta haɗe wni irin abu da ya tokare mata maƙoshi sannan ta kalli fuskar Hajiar tace" Mammie, k..."

Abbu dake zaune ne yayi magana a kausashe da cewa" Ummu, ba magana ake miki ba? Zauna maza"

Ita ai sanyi da lumanar Abbun ta kawai ta sani, da kuma riritata da shagwaɓa ta da yake, hakan yasa ta juya ta kalle shi ba tare da tayi abinda ya ce ba tace "Abbu kai ka gwada fahimta ta mana, dan girman Allah Abbbbbbbbb...."

Ɗauke fuskar ta da yayi da mari ne ya sa ta yin ɗuffff bayan ta tangaɗa kamar za ta faɗi, tsananin mamaki yasa ta kalli mahaifin nata tana dafe da kunci da jinjina lamarin, yanzu akan Jabir ɗin ne aka mare ta? Mari fa? Da girman da ƴar ta da komai? Aka mare ta? Kuma ma a gaban yaron? A gaban shi ko kunya ba sa ji? Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Wannan wane irin abu ne haka? Ƙiriƙiri a ɗaga hannu a marze ta gaban ƙannan ta jama'a dan kawai ta zauna da ɗan ta? Sake kallon Abbun tayi da ya sake nuna mata wurin yace "Zauna na ce."

Sum sum sum ta juya ta koma ta zauna ta nutsu sosai, dan har lokacin ma kunnuwan ta basa ji da kyau, Alhaji Kabir da duk ba daɗin abun ke ta masa yawa a hankali ya kalli Abbun yace "Kayi haƙuri dan Allah, ba yarinya bace da zakuyi saurin saka mata hannu."

A zafafe Abbu ya kalle shi yace "Har ita wacece da uwata na mata magana ba zata yi abun ba? Ba yarinya bace amma zamu zauna muna maimaita mata magana sau biyu, uban wa ta haifa anan? Dan kawai mun aura mata wanda muke ganin ya dace da ita, saita raina mu?"

Ƙwafa yayi sai kuma ya kalli Ummun ta kwanta kan ƙirjin Aisha tana ta rirriga ta kamar yarinya tace" Ji nan da kyau, an ɗaura auren ki da Jabir jiya, kuma munyi hakane dan ina ganin na isa da ke, idan kina so ki ƙaryata tunanina da yaƙinin da nake da a kan ki to ki ci gaba da bore har kina faɗin duk abinda ya zo bakin ki, anjima za ki tare ɗaya daga cikin gidajen nan na Yaya Bilal dake kallon nan gidan, ki gaggauta gama shirin ki dan duk randa mijin ki ya zo tafiya ku bishi ku tafi tare."

Ko da ya faɗi haka ya miƙe a hasale ya fita ba wanda ya dakatar da shi, Hajia Mammie ma da ranta ya gama ɓacewa miƙewa tayi tana faɗin" Allah ya baku zaman lafiya."

Ficewa tayi, hakan yasa Alhaji Kabir da duk ya ji ya tsargu kuma dama dreba na jiran shi zasu koma inda suka fito yace" Kiyi haƙuri Ummu, ban bayar da shawarar wannan haɗin ba dan na cutar dake, wallahi da zuciya ɗaya nayi hakan saboda ganin dacewar hakan, amma kiyi haƙuri tunda na ɓata miki, ki yafe min dan Allah."

Miƙewa yayi zai fita Ummu ta ɗaga kan ta daga jikin Aisha ta kalle shi, cikin muryar kuka har tana rawa tace" Ban taɓa ganin mugu kamar ka ba, da fari ka sake ni babu dalili ban maka komai ba, dan kar na auri wani da baka sani ba, shine ka sa yaron ka ya aure ni, dan ya sake ni a duk lokacin da ka s haka? Ba damuwa, zan zauna da shi har sanda zaka faɗa mana ya sake ni, amma idan na fito daga gidan shi ba ni ba sake aure."

Murmushi Alhaji yayi yana girgiza kai, su Hajia ya kalla yace" Hajia ni zan wuce, in sha Allah sai munyi waya da ku."

Addu'a suka bishi da ita har ya fita bayan Jabir ya miƙe ya bi bayan shi, Hajia Mamie ce ta kalle ta tace" Ummu, kenan ba'a isa a faɗa miki ki ji ba? Yanzu tsohon mijin naki kike faɗa ma haka kuma a gaban mu?"

Kallon Hajiar tayi har da wata harara harara ta maka mata a zafafe tace" Hajia ku ba kuna kallo suka ɗaura min aure da shi ba, kun sani fa yaron shi ne da bai da kamar sa, kuma nima kun san alaƙata da shi irin ta ɗa da uwa ce, shine kawai sai a ce an aura min shi sabda ni ga wacce ta rasa masoyi, bayan gaba ɗaya Eesha ma ta girme shi a shekaru, to fisabilillah wane irin zama zamuyi? Shi ne *zai min ladabi*? Matsayina na wacce ta girme shi kuma na masa alkairi a rayuwa, ko kuma *ni zan ladabin* saboda shine mijin ni kuma matar? Ni wallahi kun cuce ni."
Chapter 146 · 0% Book details