Sashe 24
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da mamaki Mardiyya tace "Me yasa kika faÉ—i haka?"
Saida ta kalle ta tace "TV kawai na ga ta kama da kanta ina madafa, kuma hotunan Eesha aka dinga nuna min...aunty ina jin tsoro ko na fara haukacewa."
Ƙura mata idanu Mardiyya tayi tana nazarin abinda ta faɗa, tv aka kunna? Anya kuwa abu ne mai yiwuwa? Ko Dai... To! Ko dai ana bibiyar rayuwar Nuriyya ne? Duba da yadda yaran ta ke ɓata a gidan nan duk da tarin masu tsaro da masu aikin gidan nan, shekara biyu kenan da Saheeb ahlan ya sauka daga muƙamin fra minista (Premier ministre), har lokacin tarin jami'an dake gidan basu rage ba sai dai canja su da aka yi, ƙofa ɗaya ce ta shigowa da kuma fita, ba ka shigowa ba tare da an san ina ka nufa ba sannan an ji daga bakin masu gidan bayan wasu mutane da suka ware cewa su shigo kai tsaye ba sai sun jira izini ba, Mardiyya na ɗaya daga ciki kuma, hatta sabga idan ana yi gidan iya katin da aka raba wanda ya samu katin kawai ke iya shigowa, shi ma sai jami'ai sun tabbatar kana ɗaya daga cikin waɗanda aka gayyatar, musamman da aka sace Kuwailat a farko, jami'an sun tabbatar ba wanda ya shigo bare ma a ce ya fita da jariri, hakan ya sa an sake tsaurara matakai da ƙara masu kula da gidan. Amma sai gashi a haka aka ɗauke Eesha, a nan za'a iya cewa an samu makama, dan kuwa mai aikin gidan da ta zo bayan fitar ta ne aka nemi yarinyar aka rasa, a gidan babu wanda ya dasa zarginshi a kan ta, dan kuwa lokacin ma tsohon ciki gare ta sannan an tabbatar bata fita da wani abu ba da zai nuna ta ɗauki ɗan mutum.
Abu ɗaya da Mardiyya ta raya a zuciyar ta yanzun shine *na gida* ne ke aikata wannan laifin, kuma ba za ta taɓa daina zargin Fa'iza, dan ko mai aikin da t zo ranar wacce ita bata yarda bat da hannu a ciki ba ai sun fi ganewa juna ita da Fa'iza, à sanyaye ta ci gaba da shafa bayan ta tace "Ki yi haƙuri, Allah zai saka miki, alamu sun nuna wani ke bibiyar ki."
********************
Yadda ya bankaɗa labulen ya shigo ya sa Kakar saurin juyowa ta kalli mai shigowa, da mamaki ta zuba mishi idanu daga inda take riƙe da wata tasa a hannun ta dake cike da fura mai sanyi tace "Sa'ad, lafiya ka faɗo mana haka ba ko sallama?"
Da wayar shi riƙe da hannun shi ciki yanayin rashin nutsuwa yace ma Kakar "Hajia ta, ina yarinyar nan take?"
Da yatsa ta fara nuna mishi ɗakin ta sannan tace "Tana ciki, ta kasa cin abinci ne saboda cikin ta ya ƙulle, shine zan kai mata furar nan, na barta tana wanka, lafiya kake neman ta haka?"
Da azama ya nufi hanyar É—akin ba tare da ya bata amsar tambayar ta ba, da É—an sauri ita ma ta shiga bin bayan shi tana cewa" Sa'ad, ka dakata mana, wanka fa take, baka san a ya..."
Ganin ya tura ƙofar ɗakin ya buɗe kuma ya shiga yasa tayi shiru kawai ta ci gaba da bin shi, zaune suka samu Aisha da ɗaurin ƙrji sai dai ta rufe daga wuyan ta har zuwa kafaɗun ta da kallabin ta. Kallon masu shigowar tayi, ganin sune da suka taimake ta sai ta tashi tsaye tana kallon fuskar Sa'ad da ta ya kalli bangon wayar shi sannan ya sake zuba mata idanu, tun daga kan gashin kanta dake baƙi ƙirin mai ɗankaran tsayi ga kuma waya, a ido zaka gane bai sa sulɓi dan bai yi yar yar ɗin nan ba, sai dai daga yadda kowane sili na gashin yake da mummurɗewa zaka gane yana da taushi sosai, fuskar ta ta ya sake ƙurawa idanu har saida bakin shi ya furta "Ke ce?"
Da mamakin tambayar da ya mata ta ƙanƙance idanun ta tare da kama kallabin ta ta ƙara rufe jiki tace "Ni ce wa?"
Da sauri ya saita nutsuwar shi tare da É—an kawar da duban shi daga kanta yace "Amm...ina nufin, idan kin gama ki fito zamuyi magana."
Bai kuma cewa komai ba ya juya a sukwane ya fita, da kallo ta bi bayanshi har ya ɓace ma ganinta duk da ya bar mata ƙamshin Turaren shi a ɗakin, Kaka dake tsaye tana kallon su a hankali ta tako ta aje mata furar gaban madubi ta dube ta tace" Ki shafa mai gashi nan, bari na samo miki ko da kayan Leila ne kafin zuwa safe mu san abun yi."
Da murmushi tace" Tom, nagode sosai."
Juyawa Hajia tayi tana da ce mata" Kuma ki tabbatar kin shanye furar nan kafin na dawo."
Yadda tayi maganar cike da gargaÉ—i yasa Aisha yin murmushi, sai kuma ta kalli tasar ta zaro idanu kaÉ—an tana ayyana ta ina za ta iya shanye furar nan, ai ita cikin ta baya É—auka dayawa.
*Bayan 30mnt* ba tayi tsammanin samun shi a falon ba, kallon ta Kaka tayi ta mata alama da hannu ta zo da cewa "Zo nan Æ´ar rikona."
Da sauri ta ƙara tana zuwa ta zauna ƙasa kusan ƙafafun ta, dafa kanta kaka tayi cikin fara'a tace "Sa'ad ne yake so ya ji, wai ina iyayen ki suke da har aka satoki aka kawo ki nan?"
Ƙara sadda kanta tayi ƙasa tayi shiru na daƙiƙu, sai kuma ta ɗaga kanta ta kalli Kakar hawaye na tararo mata a kumatu tace "Mamie, ban san su ba nima, a gidan marayu na girma, Mother kuma ita ce Maman mu, ita take kula damu take mana komai, amma ni ban san su waye iyayena ba."
Cike da tausayawa Hajia Kaka ta tallabota ta zaunar da ita kan ƙafafun ta ta rumgume, Aisha dake kuka ya ci ƙarfin ta bata ma san a ƙafafun Kakar take zaune ba, cikin rarrashi Hajia Kaka ke faɗin" Yi shiru haka ya isa kin ji Nana Aisha, kiyi haƙuri, ai bai san da haka ba da bamu tambaye ki ba ma."
Kuka take yi Hajia Kaka tana rarrashin ta, cikin daƙilewa Sa'ad ya miƙe tsaye tare da cewa" Zamu san abun yi zuwa gobe."
Da sauri Kaka ta kalle shi tace" A'a Sa'ad, mu barta kwana biyu ta samu nutsuwa, ka ji fa ta ce a gidan marayu take, idan babu tsaro a can wanda suka sato ta ai zasu sake komawa dan ita."
Kallon Kakar yayi da tunanin ko wa ya ce ma Hajia za'a mayar da ita nan kusa? Sai dai kuma tayi gaskiya a maganar ta, tunda *makashin su yana tare su*, mai basu agaji da sunan gidan marayu shi ke musu ɗauki ɗai-ɗai, bai ce ma Kaka ƙala ba ya nufi hanyar fita, sai da ya yi ɗan nesa da su ya tsaya tare da juyowa, zamn Aisha a ƙafafun Kakar tashi ya kalla, cikin taushin murya yace "Ki zauna kan kujera, ba'a ƙafafun Kakata ba."
Da sauri Aisha ta miƙe tsaye tare da zaunawa ƙasa, Hajia kuma murmushi tayi ta bi shi da kallo, Sa'ad kenan, yanzu nan kafin Aisha ta fito da ta zaunar da shi tana mishi magana a kan sana'ar da yake yi, kallon ta kawai yayi yace _" Karki damu Hajia, ai laifin Ibu ne."_
Da ta sake kallon shi ta masa magana akan sunan mahaifin shi da yake faɗa gatsau, sai ya yatsina fuska tare da taɓe baki yace _" Na saba ne ai."_
Shine yanzu zai wani nuna mata kulawa, bayan yana gwasale mata É—an ta, girgiza kai tayi tana dariya tace" Allah ya shirya min kai."
Sai kuma ta kalli Aisha tace" Kin ga taso na sake rumgume ki, rabu da shi kin ji, kishi yake saboda ya ga za ki ƙwace masa ni."
Dariya Aisha tayi tana satar hanyar da ya bi da kallo, sosai take girmama taimakon da suka mata, a ƙalla dai ko mutamin banza ne ya taimake ta kuma ta ji daɗi, iya kwana ɗaya ma idan suka bata ta gode, bare kuma bata ga alamar tafiyar ta gobe ko jibi ba.
********************
Cikin kwanaki kaɗan aka gama ma Jabir shirin tafiyar shi, kafin lokacin tafiyar tashi kuma ya zauna ne a ɓangaren Ummu, daga wajen ta da Alhaji Kabir ba wata matsala da yake fuskanta ko ta ƙwayar zarra, amma a wajen mutanen gidan, Hajia Atika da Hajia Asiya da wasu daga cikin yaran su, yana ganin tsangwama da ta sa Ummu ta gargaɗe shi da nufa ma inda suke, dan ita kanta sosai take ganin raini a wajen wasu yaran gidan saboda kawai ta auri uban su, dan haka yake kiyayewa ba ya nufa inda suke, har daren da ya shiga ya musu ba kwana dan zai tafi.
Sosai Hajia Lubabatu ta bishi da addu'a da yi masa nasiha ya maida hankali ga abinda ya kai shi, ya ji daɗi ƙwarai kuma ya ɗauketa a matsayin uwa ko ma Kaka, wajen Hajia Asiya kuma kallon wulaƙanci ta bishi da shi cike da zaƙuwar ya bar mata falo tace _"Allah ya kiyaye, sai anjima."_
Suna fitowa shi da Ummu dake rakiyar sa suka nufi ɗakin Hajia Atika, daga ƙofa tana hangosu ta miƙe da waya a hannu tana faɗin" Zeinab idan sun fita ki rufe min ƙofata zan kwanta ne, bana son hayaniya."
Hayat da Zeinab ne suka nuna rashin jin daɗin su har Hayat ɗin ya rakosu har ɓangaren Ummu yana basu haƙuri, shirye shirye ya ci gaba da yi har zuwa ƙarfe 03:00 na dare Alhaji Kabir da Khamis ɗan riƙon Hajia Luba suka kai shi gidan mota bayan yayi sallama da Ummu.
Bai taɓa sanin ya yi sabo da su haka ba sai da ya ga zasu juya su bar shi gidan mota, cike da so da ƙauna ya faɗa jikin Alhaji Kabir din yana riƙe shi gam, cike da dattako Alhaji Kabir ya shafa kanshi yace "Jabir, ba dai kuka kake ba ko? Ka ga maza shiga layi an fara kiran suna."
A hankali ya ɗaga daga jikin shi, kallon fuskar shi yayi ya furta "Nagode ABBA, *ina ƙaunar ka*, ba zan taɓa mantawa da kai ba."