Sashe 27
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta kira wayar shi amma a kashe, shi ma dai wani yanayin tashin hankali ne na daban. Tun da aka idar da sallah asuba ta sa Sabeer ya je ya dubo gidan su Ja'afar, bai mata musu ba ya tafi saboda kallon da Mukhtar ya mishi, yana zuwa can ya samu abokin yawon ba inda yaje hasalima a gida ya kwana, dan haka ya dawo ya sanar da su abinda ke faruwa, ba dan ta samu gamsuwa ba dai har suka zauna kan babban teburin cin abinci.
Lokaci ne da ya kamata Ace suna cikin farin ciki saboda duka Ahalin sun haɗu babu wanda ba ya nan, sai dai rashin Fahad da kuma damuwar da Hajiar ta nuna ƙiri-ƙiri yasa ba mai wannan farin cikin, an yi zugum ne ana kai abincin baki ba dan ana jin daɗin shi ba.
Cikin dubara Fa'iza ta kai yatsunta biyu kan bakinta ta rufe bakin d su tana kallon mijin nata Bilal dake cikin wata dakakkiyar shaddar da aka ma ƙaramin dinki, ma'ana hannayen ma iya guiwar shi suka tsaya tsayin rigar ma daga guiwanshi na ƙafa ne, ma fi aksari haka shigar sa take ta manyan kaya kuma ba mutumin saka hula bane, abinci yake ci hankalin shi na kan Hajia yana riƙe da hannun ta ɗaya yana ta mammatsa mata shi. Inda ta dubi Mukhtar kuma da hankalinshi ya fi karkata kan Kabil yana mishi wasa, sai kuma lokaci lokaci ya kan kalli Nuriyya da ita ma take duƙowa tana ma Kabil ɗin wasa suna ƴar hira duk da basu fito da farin cikin su a fili ba, Abida kuma na kusa da Sabeer ne har tana ɗn tambayar shi iya inda za'a iya samun Fahad kenan? Taɓe baki Fa'iza tayi cikin zuciyar ta take ayyana _"Me yasa wai basu kira ba har yanzu?"_
Cikin dattako Alhaji dake sanye da wani sassauƙan yadi kalar bleue ganin yadda Hajiar ke neman rikice musu tana son fara kukan da zai iya jawo mata ƙarin matsala a idanun ta dake ciwo yasa shi aje cokalin hannun shi yace" Shikenan, ki daure ki ci abincin, kuma kar ki yi kuka, ni kuma zan fita yanzu na nemo miki shi, hakan ya miki?"
Kallon shi tayi tana É—aukar tissue a tsakiyar teburin tana goge hannayen ta tace" Ba haka bane, ni ba kuka zanyi ba, kawai dai ina tunanin me yasa wayar shi bata shiga? Sannan ina yaje a wannan lokacin da ya fita daga gida, balaguro yayi cikin dare?"
Bilal da shi ma ya aje cokalin shi kallon ta yayi yace" Ammie, na tabbatar Fahad yana lafiya, kin san shiriritar sa idan ta motsa, amma ga Sabeer zai je ya nemo miki shi a duk inda yake."
Sai kuma ya kalli Sabeer É—in dake cin abinci yace" Sabeer, ka yi sauri ka idar ka je ka sake dubawa gidan sauran abokan shi."
Jinjina kai Sabeer yayi yace" To Yaya." Ya ci gaba da cin abincin, Abbu Mukhtar ma kallon Hajiar yayi cikin nutsuwa yace" Ammie, dan Allah ki kwantar da hankalin ki, zamu fita tare da Sabeer mu duba miki shi, za mu samo shi in sha Allah."
Jinjina kai tayi sai Nuriyya da tace" Nima n kira aunty Mardiyya dan naji ko yana tare da *Aslam*, amma ta ce sam basu haÉ—u ba ma saboda Aslam yana gida yana karatu dan jarabawar su ta kusa."
Gudun ƙarawa kanta zargi da kawar da tunanin kowa a kanta Fa'iza ma ta ɗan taɓe baki cike da halin ko in kula tace" Gaskiya na damu sosai, dan ni fa haro saƙo na bashi da zai fita na ce idan zai dawo sai ya kawo min, gashi yanzu bamu san a halin da yake ciki ba."
Abida kam da zumuɗi da fara'a tace" In sha Allah ma ba abinda ya same shi, zai dawo cikin ƙoshin lafiya."
Kafin wani ya sake cewa wani abu wayar Bilal tayi ƙarar da ta saka Fa'iza saurin kallon shi fiye da kowa, Bilal da saida ya gama duba lambar da ke ɓoye kafin ya ɗaga da yin sallama, daga ɗaya ɓangaren ba tare da an amsa sallamar ba aka ce"I zuwa yanzu nasan kun gama tabbatar da autanku baya tare da ku, sannan ni ne wanda zai iya sanar da ku yana cikin ƙoshin lafiya ko akasin haka."
Da mamaki da kuma canza yanayin fuskar shi cikin tausa murya yace" Wa ye kai malam? Ya aka yi kasan Fahad baya tare da mu."
A tsanake aka sake cewa" Sanin wa ye ni ba shine abu mai mahimmanci ba a yanzu, halin da ƙaninku yake ciki shine ma fi a'ala, id..."
Da sauri Bilal ya katse shi da cewa" Malam ina ƙanena yake? Idan kasan inda yake k..."
Shima da gadara ya katse shi da cewa" Ya zama na ƙarshe da za ka sake katseni ina magana, Fahad na tare da ni yanzu haka kuma a ƙarƙashin kulawa ta, kuɗin fansar da zaku biya na baku shi kuma sune miliyan hamsin kacal, dan haka idan kun shirya kan kuɗin nan da minti ashirin zan kira ka dan sanar da kai inda za ku kawo kuɗi ku karɓi ɗan ƙiriniyar gidan ku, sannan kuma..."
Numfashi ya sauke sannan ya ci gaba da cewa" Sanar da jami'an tsaro halin da kuke ciki zai tunzurani na kashe yaron nan, haka ma ɓata min lokaci wajen haɗa kuɗin ko tunanin ku min wasu dubaru, to shakka babu zan kashe *ƙwayar cutar gidan ku*..." Ya ƙarashe tare da kifawa Fahad marin da ya saka shi ƙwala ƙara ya kira sunan _" Yah Bilaaaaaal."_
Da mugun sauri Bilal ya zabure ya miƙe a rikice yana dafe teburin gaban shi cikin ɗaga murya yace" Ka ga malam ka da ka sake dukar min ƙanena, zan kawo muku kuɗin yanzu, amma dan Allah ku daina dukanshi, yaro ne ƙarami bai saba da wahala ba, dan Allah n'a roƙe ku..."
Yadda ya dire maganar kamar zai fashe da kuka yasa Sabeer miƙewa a zafafe dan tuni Hajia ta miƙe tana riƙo hannun Bial da tsare shi da idanu, Sabeer na zagayawa ya so karɓan wayar dan yayi masifa, amma sai Bilal ya kauce tare da zabga mishi harara yana ci gaba da faɗin "Zan kawo kuɗin yanzu, ku gaya min inda zan je na kai, amma kada ku sake cutar da shi."
Cike da shaƙiyanci aka furta "Yaron kirki, nan da minti sha biyar zan kiraka, nasan miliyan hamsin ba komai bace dama ga ahalin Ahlan, a ƙyabtawar ido ma zaku iya yin atshawar ta, da kyau."
Yana faɗin haka ya yanke kiran ya bar Bilal baki sake yana nanata kalmar yaron kirki da ya kira shi, ba dan iskanci na mutane ba da ubangiji ya albarkace shi da haihuwa da yanzu an fara tara masa jikoki fa shima, wataƙila rashin haihuwar ne yasa har yanzu yake ɗanye sharaf abin shi kamar bai wani zarta arba'in da tsiraru a kai ba. Muskutawa yayi da nufin jaye kujerar d yke zaune baya dan ya wuce zuwa sashen shi, hannun shi da Ammie ta riƙe a rikice tana faɗin "Bilal, Bilal ɗina, ya aka yi? Me ya faru da Fahad ɗin? Su waye suka kira ka? Me suka mishi? Yana ina yanzu?"
Fuskar ta ya kalla cike da tausayawa musamman da take neman fashewa da kuka, dafa kafaɗar ta yayi cikin nutsuwa yace "Ammie, ki kwantar da hankalin ki, zan fita ne yanzu zan dawo miki da shi, nayi alƙawari."
Girgiza kai ta fara yi tana faÉ—in "A'a Bilal, mu tafi tare, na ji kana magana kamar wani abu ya samu Fahad ko? Ka faÉ—a min gaskiya mana."
Abbu dake zaune ya zuba musu idanu kawai yana kallo ne ya tsare Bilal É—in da idanu yace "Masu garkuwa da mutane ko? Sun kama shi ne?"
A hankali Bilal ya kalle shi, bai gyaɗa mishi kai ba kuma bai bashi amsa ko da idanu ba bare baki, shirun kuma ya tabbatar ma da kowa halin da ake ciki, hakan yas Abbu sunkuyar da kanshi yace "Nawa suk ce suke da buƙata?"
Saida ya ja numfashi ya sauke sannan furta "Miliyan hamsin." Ammie da ta gama rikicewa a gigice ta sake riƙo duk hannayen shi ta shiga jijjigawa tana magana "A basu mana Bilal, a basu kuɗin mana su sakar min yarona, ni...ni zan basu kuɗi, ina da kadarorin da na gada wajen mahaifina, Bilal a siyar a biya mana."
Tallabo kumatunta yayi cikin nutsuwa yace "To Ammie, abinda nake ƙoƙarin yi kenan, ba sai kin siyar da kadararki, ni zan biya Ammie, ina da kuɗin zan biya na karɓo miki shi in sha Allah."
Nuriyya dake kusan ta riƙota tayi cikin muryar kuka dan har ta fi Ammie shig tashin hankali ta rumgume Ammie a jikin ta tana faɗin" Ammie kiyi haƙuri, Yaya Bilal zai dawo miki da shi ki ganshi, na fahimci abinda kike ji, kum da rashin sanin inda abinda ka haifa yake, Gwara a ce gawar sa ce a gaban ka ka samu tabbacin yana cikin ƙasa ya fi kwanciyar hankali."
Duk zubawa Nuriyya idanu sukayi, hakan yasa tana maƙale da jikin Ammie ta kalle su ita ma hawaye na bin kumatunta tace" Ƙwarai, akwai raɗaɗi sosai, raɗaɗi ne mai zafin gaske da baya warkewa a zuciya, samun namiji tamkar dubu ya kasa sakawa mu manta da ƴan matanmu, ina ma an nemi n biya kuɗin fnsarsu ne, ni kam da na yi komai dan na biya fansar su daga ciki har da *sata* ma."
Kalaman ta suka saka Ammie ƙara rumgume t ƙwarai suna fashewa da kuka, hakan yasa Ammie cikin kuka take faɗin" Kamar muna da laifi ko? Ya kamata mu fara cigiyar su ta kowane irin hali."
Ganin kamar za'a daina maganar Fahad yasa Fa'iza miƙewa tana kyaɓe fuska kamar za ta yi kuka tace" Abun tausayi, gaskiya ya kamata ayi maganar Fahad, dan bamu san halin da yake ciki ba, na damu akan shi sosai saboda ina tsoron kar wajen karɓo saƙona ne abun ya faru da shi."
Kallonta duk sukayi, hakan yasa ta É—an wayance da sake cewa" Ina fata ba abinda suka mishi."