← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 168

Sashe 92

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin ya ƙarasa faɗa Ummu ta miƙe tsaye a zuciye, rigar ta kawai ta ɗauka ta mayar jikin ta tare da juyawa ta fita a ɗaki ba ta ce da shi komai ba, saida ta ɓace ma ganin shi ya girgiza kai cike da jin ba daɗi da kuma haushi na yadda yana magana ta katse shi ta tafi ta bar shi zaune kamar sakarai? Jinjina kai yayi ya muskuta da niyyar gyara kwanciyar shi, sai kawai ya hango kan shi a madubi, duk da zaune yake amma saida ya hango tumbin shi, ai da baya da shi girma ne ya sa shima ya zo, ba kuma iya muryar shi ta canza ba har da kan shi da yayi fari ƙal da ma gemun shi, ta duba mana ta ga Hajia Luba wacce ta ma haƙura da kwana da shi, idan ka gan shi wurin ta kawai shine ya je dan ya duba ta sannan su yi hira, me ya kawo haka? Girma ne fa, amma irin rayuwar da sukayi da Hajia Lubabatu ma idan Ummu ta gani ba sai ta suma ba dan yadda abun zai dake ta, shine za'a wani dame shi da baya iya komai? Haba mana dai.

Wannan tunanin da maganganun da duk ya faɗa mata ne ya faɗe su ne saboda dama akwai abinda yake tunani har ya fara caza mishi kai, Shiyasa bai yi tunanin komai ba ya kwanta tare da ci gaba da tunani akan Kuwailat da Jabir, da kuma Nabila da Maman ta da ya san dole tana damuwa akan rayuwar da take yi sosai, a haka bacci ya ɗauke shi bai sake waiwayar matsalar Ummu ba face ma ɓacin rai kawai game da matsalar ta ta da ta haifar masa.

*Alhamdulillah.*
15/08/2023, 20:14 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*RUBUTACCIYA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

_NA_

*SAMIRA HAROUNA*

_SADAUKARWA GA_

*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_

_Bismillahir- rahamanir-rahim._

*43*

Ba dan Nabila na gidan ba so tayi ta share shi kawai, yo me yake nufi da ita? Kenan zai kasara ta kamar yadda matan shi suka kassara? Ya zai haɗata da tsofaffin matan shi ne saboda Allah? Wacece ba ta haife ta a cikin su ba? Shi a cikin jikokin shi ba akwai wacce t girme ta ba da wacce suke tsara? Shine zai zauna yana gaya mata hakanan? To bata ƙaunar shi kuma bata ƙaunar taimakon shi, ya je ya riƙe kayan shi dama ai ba anfani suke mata ba, ita fa ba zai raina mata wayo ba kan wannan, ba fa za'a raina ta ana gaya mata magana kan abinda ita ke cutuwa, aikin banza kawai.

Sallama kaɗai ta yi ƙasan maƙoshi t shiga ɗakin, ba ta kalli inda yake ba ta aje faranti kwanukan abincin kawai tare da juyawa ta fita, shima bai ce mata komai ba ya bita da kallo har ta fita yana ayyana _"Ummu kenan! Ita ko gajiya ba ta yi da rigima."_

Sai kuma ya ƙaraso kusan farantin yana buɗawa, murmushi ya saki yana ayyanawa a ran shi _" Bayan ta saka siket shine ta tfi bata bari na yaba kyan ta ba?_"

Girgiza kai yayi yana murmushi, shi iya haka ma ai ya ishe shi rayuwa da ita, su rayu abun su mana cikin farin ciki, ga ƴar su guda ɗaya tamkar dubu mai ladabi da biyayya wacce yke jin baya son rabuwa da ita tun yanzu, amma kuma haka zai haƙura y miƙa ta hannun wanda yake da tabbacin zai so masa ƴar sa fiye da yadda shi yake yi, su gode Allah man da ni'imar sa gare su, ta dubi Hajia Luba ma ko haihuwar ba ta taɓa yi ba, haka t haƙura take zaune dashi har yanzu dake yake fatan ita ta binne shi sannan ta msa takaba, duk yaran da suke kiran ta da Mama ƴaƴan ƴan uwan shi ne da nata ƴan uwan ta raina har ta aurar da wasu daga ciki. To kenan idan Ummu ce ba zata iya wannan haƙurin ba? Wanda rashin haihuwa na iya saka komai, na iya saka mutum ya kauce hanya ma.

Kuwailat ce ta shigo ta gaishe shi sannan ta ɗora da faɗin saƙon da ak aiko ta cewa "Abba, wai in ji Mamie za su tafi gidan Mama tare da aunty Nabila."

Kallon fuskar Kuwailat yayi, ba wai fa tana neman izini ba, a'a zasu tfi ka ce masa? Zai iya cewa a'a saboda ya isa kuma ba'a tambaye shi da girmamawa ba, ko da dai ran ta ɓace yke ai zata iy bashi wannan martabar, to amma mecece macen ma gaba ɗaya? Wata karkatacciyar halitta ce da ke tunani da zuciyar ta, sai kawai yayi murmushi matsayin sa na dattijo yce ma Kuwailat "Har sun shirya kenan? To ki ce ta zo na sallame ta."

Da sauri ta amsa tare da juyawa ta fita, sanda ta isar mata da saƙon saida ta yi jim kamar ba za ta tafi ba, sai kawai ta miƙe tana faɗawa Nabila ta yi sauri ta gama cin abincin za su wuce. Tana shigowa ta tsaya gaban shi tace" Ka ce na zo?"

Kallon ta yayi sosai ya dakatar da cin abincin yace" A ganin ki ya dace ki turo min Kuwailat wai zaku fita? Yaushe muka yi dake zaki fitar?"

Ƙofa ta ƙurawa idanu ranta ɓace tace" Ina so naje ne saboda muhimmin abu, kuma zan raka Nabila ba wa mama haƙuri."

Jinjina kai yayi da yaji abinda zai kai ta ɗin, hannu yasa aljihu ya ciro kuɗi ya miƙo mata yace" Ki sha mai da wannan?"

Girgiza kai tayi tace" Ka bar shi nagode, akwai mai kuma ina da kuɗi ko da yake ƙarewa."

Ƙwarai ran shi ya sosu kuma so take ta hassala shi ta ga ɓacin ran da bata san shi da shi ba, amma sai ya sake dakewa yace" To karɓi, tukuicin kwalliyar nan ne?"

Da wata irin zuciya dake hawr mata sama tana sauka ta sake yatsina fuska tace" A'a, ka bar shi wallahi, nagode Allah saka."

Juyawa kawai tayi za ta fita tana faÉ—in" Sai mun dawo?"

Yadda ran shi ya sosu sosai ya sa ko abincin bia ci ba shima ya miƙe ya fita. Lokacin su Ummu har sun fice ita da Nabila tare da Kuwailat suka aje ta makaranta duk da kusa ne sosai.

A gidan suka samu Yaya Luƙman ya zo gaishe da Mama kafin ya wuce aiki, bayan gaisawa Yaya Luƙman ya kalli Nabila yace "Gimbiya, an ga damar zuwa yau duba mutane?"

Sai kawai ya girgiza kai dan haushi zai iya saka shi make ta, da kunya Nabila ta sadda kan ta tare da share ƙwalla na tausayin yadda ta ga Mma ta rame sosai kamar ba ta jin daɗi, ta san sauyin ba zai rasa nasaba da tunanin matsalar ta ba, har zai fita yana faɗin "Nasan dai ba jimawa zaki yi ba zaki tafi, to ki gaida mutanen can, ba zamu sake riƙe ki ba Nabila, kije duk inda kike so."

Ummu ce ta kalle shi tace "Yaya."

Kallonta yayi yace "Na'am."

A nutse tace "Dan Allah ka zauna, magana ce ta kawo mu mai mahimmanci."

Bai mata gardama ba ya zauna yana kallon su, cikin nutsuwa Ummu ta dube su tace "Mama, Yaya Luƙman, ga dai Nabila ta dawo gida, jiya ta zo daga Agadez, ta zo min cikin wani irin yanayi tana kuka, Mama..."

Ta faɗa a tausashe sannan ta ɗora da "Mama ki yafe wa Nabila duk abinda ta miki wanda ya ɓ...." Da sauri Mama da tuni ta fara hawaye ta rufe bakin Ummu tare da fashewa da kuka tace "Kar ku fara Ummu, ban taɓa riƙe Nabila a zuciyata ba, nasan illar yin haka, shi ya sa ban taɓa kwatantawa ba, kullum tsakanina da ita addu'a shiriya ce da kuma fatan alkairi a duk inda take, ban taɓa riƙe ta, ban taɓa kwana da ɓacin ranta a zuciyata ba, saboda ban san ko zan iya farkawa daga baccin ba ko kuma tazarce zan yi, dan haka ta je na yafe mata, kuma Allah ya shirya ta."

Nabila dake kuka kamar ranta zai fita ne ta faɗa jikin Mama cikin matsanancin kuka take cewa" Mama ki yafe min, nayi kuskure a rayuwata mama, wanda na bijire muku saboda shi ya ci amanata, iyayen sa sun zaɓa masa mata a gidan, sun ce ni ba zai aure ni ba saboda ban dace da shi ba, Mama ki yafe min dan Allah, ki taya ni roƙon Allah ya yafe min."
Chapter 92 · 0% Book details