← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 168

Sashe 135

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Akan wannan matsayar suka tsaya Mamie kuma hatta wasu daga cikin kayan da Ummu ta fara bada wa ɗinki saida ta sa aka nemo mata irin su sak ta mayar a akwati nan, washe gari da rana tsaka Larwan ya zo dan shi la kwana sukayi a gidan shi da Fauziyya suna tashin hankali da ta faɗa masa inda ta zo har take alfaharin wai ta zo tayi kashedi, bai taɓa dukan ta ba tunda suke, amma yau da safe saida ya wanwanka mata marin da shi kan shi bai san adadin shi ba, sannan ya watso ta ƙofar gida ya ce ba shi ba ita ya sake ta saki biyu, a ƙofar gidan ya barota tana haukan ba inda za ta je, ai dan ita kawai aka yo shi, dan haka ya je ya dawo zai same ta nan. Duk yadda ya so nuna musu ɓacin ran shi da son suyi haƙuri kar maganar auren nan ta lalace abun ya ci tura, haka suka bashi haƙuri da musu fatan kowa Allah ya haɗa shi da rabon sa, ya shiga tashin hankali sosai tare da ƙara tsanar Fauziyya da ita ta jawo masa, babban abun takaicin shine yadda ya ya je dan ya roƙe su suyi haƙuri, amma sai ya ce ko shine mahaifin Ummu haka zaiyi, dan alamu sun nuna matar shi ta fi ƙarfin sa sannan ba zai iya kula da gidan shi ba, abu kamar wasa sai gashi ganin Ummu ma ya zamar masa aiki, yana so ko sau ɗaya yayi magana da ita amma ya kira wayar ta kashe, kula ta kashe ne dan ya san zai kira ta ai.

*Fahad* kuma tun da safe sukayi waya da Jibril yake faɗin "Shikenan Fahad kai ma ka ƙi ni kamar yadda ƴar ka ta ƙi ni."

Fahad da baya cikin yanayin daÉ—i ya tambaya "Ban gane ba ? Me ya faru?"

A tsanake Jibril yace "Fahad na farauci Ummu ko Allah zai sa na samu, amma sai jiya muka haÉ—e da ita take ce min ma zatayi aure wai, ita bata faÉ—a min ba kai ma kuma haka."

Cikin jin haushi ma Fahad yace "Kai dan Allah wannan ma tsohuwar magana, yanzu ai ba maganar aure tsakanin Larwan da Ummu, kuma kaga ita dai ba yarinya ba, dan haka har yanzu a ksuwa take, Jibril idan ka san kana son ta tsakani da Allah kuma zaka min kara ka riƙe ta amana, to ni mai baka goyon baya ne wajen sake fitowa ka nemi auren ta, idan ta amince faƙat."

Labari ne ma fi daɗi a gurin Jibril, dan hakan a wurin shi kamar tabbaci ne na Ummu dai za ta zama mallakin shi, a yanzu ba wai so yake ya shiga rayuwar ta kafin aure ya gujeta ba, so yake ya aure ta saboda yadda Fahad ya mishi magana ɗin nan ya san an samu matsala babba, dan haka zai bari su sakankance dayawa har a ɗaura musu aure, sati kawai zai riƙe ta yana riƙe ƙugun ta yana bata wuta, satin nan na cika zai sallame ta shi kuma ya bar ƙasar saboda Fahad ya san zai iya masa ɗanyan kai, ba wai Ummu ba hatta matar shi da yaran shi suyi ta kan su ba bare kuma wata Ummu.

*Alhamdulillah.*
[30/08 à 10:44] MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*RUBUTACCIYA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

_NA_

*SAMIRA HAROUNA*

_SADAUKARWA GA_

*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_

_Bismillahir- rahamanir-rahim._

*63*

*Kwana biyu* kenan da faruwar wannan abu da ya sa Ummu lazimtar zaman É—aki da rage yawan magana, abubuwa ne sun taru sun mata yawa ta rasa yadda za ta yi, tana kwance dai ne tun da safe amma ba bacci take ba kuma ba abinda take sai tunani.

Wayar ta ce tayi vibration wanda rashin son hayaniya ya sa ta saka ta a wannan mode ɗin, a nutse ta zura hannu ta jawo wayar daga ƙasan filo, ganin sunan Yayana yasa ta jan tsaki ta mayar da wayar ta aje, saida kiran ya tsinke sannan ta ɗauki wayar za ta kashe, kafin ta kashe saida ta duba kiran da ya mata bata ɗagawa har kira kusan ɗari da shida a kwana biyun nan, tsaki ta sake ja cike da takaici ta gyara kwanciyar ta za ta kashe wayar gajeran saƙo ya shigo wayar daga lambar shi.

_"Dan girman Allah ki ɗaga waya ƙanwata."_ Shine abinda ya rubutu a saƙon, to ita wacece da za'a haɗa da girman Allah ta ƙi abun? Yana kira ta ɗaga sai dai tayi shiru kawai, ajiyar zuciya ya sauke cikin wata gigitacciyar murya yace" Haba ƙanwata, saboda Allah ko da ace abinda ya faru bai faru ba tsakanin mu, shin babu girmamawar da zata saka ki ɗaga kirana ko babu dalili?"

Rashin son magana yasa a taƙaice kuma a daƙile tace" Kayi haƙuri."

A taƙaice shima yace" Na yi. " Sai kuma ya marairaice yace" Ƙanwata, ke ma kin goyi bayan hukuncin da iyayenmu suka yanke? Ummu ba laifina bane abinda Fauziyya ta zo tayi, ban sani ba wallahi, ban sani ba, dan girman Allah Ummu kiyi haƙuri kar ki ce kin fasa auren nan, wall..."

Katse shi tayi a saiɓance da fadin" Dan Allah Yaya Larwan, mu bar maganar kawai, mu yi haƙuri da hukuncin da suka yanke, bayan haka ni ba zan iya da wannan tashin hankalin ba, gidan da na baro mu huɗu ni ce ta huɗun, amma wallahi har yau ba zan iya gaya maka wata magana da cikin ukun nan wata ta faɗa min da ta min zafin da ta hana ni sukuni kamar yadda matar ka ta min ba, kawai ina fuskantar wariya ne da shariya a gurin su, idan kaga magana marar daɗi ta haɗa mu to suna ganin na shiga hurumin su ne, amma sai gashi har gidan iyayena, matar da ban auri mijin ta ba ta zo yi min kashedi har da marina a fuska? Yarinyar da bata wuce tsarar Nabila ba, sannan ga ikrarin ganin bayana da tayi wanda ya isa mu tsaya gaban alƙali ni da ita akan wannan furucin.... Ba zan iya ba Yaya Larwan, dan Allah ka manta da alaƙar soyayya da mukayi da kai a baya ya zama tarihi, mu ci gaba da kallon junanmu a matsayin ƴan uwa, bana so wani abu ya shiga tsakanin mu marar daɗi, sai anjima."

Tana ji yana kran sunan ta da kar ta kashe wayar ta kashe ta gaba ɗaya ta aje wayar gefe, gyara zama tayi kan gadon ta ɗauki filo ta rumgume tana kallon ƙofar ban ɗaki, ta yi nisa a tunani kamar daga sama ta ji ana bubbuga ƙofar, da sauri ta dawo da nutsuwar ta ga ƙofar a tunanin ta Mamie ce dan haka ta ce "A shigo."

A hankali Abbu ya buɗo ƙofar ya shigo yana faɗin "Baby."

Ƙara gyara zama tayi da rigar baccin ta mai siraren hannaye tace "Abbu, ba ka fita ba dama?"

Bai ce komai ba saida ya zo kusa da ita ya zauna yana kallonta yace "Ban fita ba, Mamin ki ta faÉ—a min yanzu É—aki kawai kike zama, kina lafiya? Wani abun yana damun ki ne?"

Numfashi ta sauke tana kallon hannayen ta tace "Abbu ba komai."

Girgiza kai yayi yace "Um um! FaÉ—a min ke dai?"

A hankali ta sauke numfashi ta kalle shi cikin sanyin murya tace "Abbu, dama haka zawarci yake tattare da ƙalubale? Abbu na fara sarewa da lamarin nan, na fara jin tsoron ko shikenan na rasa adalin namiji a cikin dubannin mazaje."

Da sauri Abbu ya girgiza mata kai a sanyaye shima yace "A'a, ba haka bane *magajiya*, ta ki jarabawar ce ta zo a haka, kuma in sha Allah na san ba da jimawa ba zaki samu wanda ya dace, ai har yanzu kina samun masu son ki, kuma zaki samu wanda ya dace da ke da izinin Allah."

A ladabce ta girgiza kan ta kamar za ta yi kuka tace" Abbu bana jin hakan zai faru, ni na ma fara tunanin ko butulci na ma Abban Kuwailat, shiyasa ubangiji zai jarabe ni da ra..."

Da sauri ya mata alamar tayi shiru yana girgiza mata kai yace" A'a, kar na sake jin kin faÉ—i haka, ba kiyi butulci ba, shi ma kuma ya san da haka, sannan adalci ya miki, dan haka bana so ki sa damuwar nan a ran ki, dan Alhaji Haris da Larwan sun kubce, zaki samu wani nagartaccen da ya fi su dacewa dake, ina tabbatar miki da haka."

ÆŠan murmushi tayi ta jinjina kan ta tace" To Abbu, nagode."

Hannu ya kai ya shafo kan ta yana murmushi yace" Ki tashi kiyi wanka ki fito, gaba É—aya auntyn ki ta damu saboda rashin ganin walwalar ki."
Chapter 135 · 0% Book details