← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 168

Sashe 100

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da kallo ta bishi, sai ta sake Taɓe baki, ita ta rasa me suke nufi da ita? Kamar wata mai hassadar su, sai wani abu suke yi haka dai... Ko ba komai dai ta ji daɗi, sabon babur fa aka siya mata madadin tsohon da take fama da shi, ita kam me ya fi ran ta? Da alama ma ladabi za ta fara yi ma Jabir ɗin, in dai zai dinga mata irin kyautar nan, to me ye a ciki? Duniya ce fa da bata da tabbas.

*Alhamdulillah.*
15/08/2023, 20:14 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*RUBUTACCIYA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

_NA_

*SAMIRA HAROUNA*

_SADAUKARWA GA_

*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_

_Bismillahir- rahamanir-rahim._

*47*

Ƙara ƙyalƙyalewa Nabila tayi da dariya tana ci gaba da kitsewa Mama kan ta tana faɗin "Allah Mam ba zan iya sana'ar kitso ba, duba fa mama ke kaɗai amma na huta ya kai sau uku, to ina ga idan mutum biyu ne ko sama da haka? Ai kwana zamuyi ana abu ɗaya."

Mama ma dariyar tayi tana taɓe baki tace "Shirmen banza, son jiki ne ba komai ba, ama sana'ar kitso ai sana'a ce mai kyau da idan kina yin ta ba ke ba talauci."

Murmushi Nabila tayi tace "Hakane Mama, gaskiya ni dai ban iya zaman nan, amma idan kika ce na dinga yi sai na fara yi wa Æ´an unguwa."

Jim Mama tayi, a ranta take ƙara godewa Allah da ya shirya mata Nabila, yanzu fa ko ƙofar gida ta daina leƙawa, ta ce istibra'i take jira ta gama duk wanda Mama ta zaɓa mata za ta aura, daga nan kuma ta koma islamiyya ta ci gaba da karatu. Kafin Mama ta ce wani abu Mujittafa ya shigo da sallama suka amsa, gaisawa suka fara yi kafin ya miƙowa Nabila ledar hannun shi ƙarama yace "In ji Yaya Luƙman , ko layin ki ne ya canza miki ko ya ya ne ma ni ban gane ba."

Karɓa tayi tana faɗin "Ayya, Allah sarki Yaya Luƙman, shi da nace ya siya min sabo, ni bana son tsohon nan gaskiya."

Kallon ta Mama tayi tace "To me ya sa wai? Tsohon da shi aka san ki ai."

A ladabce tace "To ai shine matsalar Mama, da na saka yanzu duk mai lambata ai zai neme ni, ni kuma bana son sake mu'amala da mutanen da nayi a baya."

A tausashe Mama tace "Ki saka layin ke dai, ai ba'a taru a lalace ba, dole akwai na ƙwarai a ciki wanda nasan kina jin daɗin tarayya da su, ko ba haka ba?"

Mujittafa ma murmushi yayi yace "Gaskiya kam, kuma a cikin su ma zaki iya samun wanda shi da gaske auren ki yake so yayi, ke ce kawai kika kawo shashanci."

Shiru ta É—an yi, gaskiyar Mujittafa akwai masu son auren ta sosai, musamman ma wani Alhaji Babangida, jinjina kai tayi tace "Shikenan, duk yadda kuka ce haka za'a yi."

Buɗe wayar tayi ƙarama ce kamar yadda ta buƙata, saka layin tayi sannan ta kunna wayar, Mujittafa ta kalla da Mama ke tambayar sa iyali tace "Yaya idan ka je ka ce wa Yaya Luƙman nagode sosai, zan kira shi ma na masa godiya da kaina."

Bai ce ƙala ba shi dai ya juya yana cewa Mama "Zan tafi, dama hanya ce za ta ɗauko ni ya tsare ni da saƙon ƴar nan."

Tafiya ya yi inda Nabila ta ci gaba da yi wa Mama kitso. *Amma* ba'a kai ko ina ba kiran *Fahad* ya shigo wayar... Tunda aka amince da maganar auren su yake kira hankali tashe amma waya kashe, ya ɗauka shine bata son Magana da shi, ya karɓi wata wayar ya kira amma dai ba'a samu, haka ya tisa Ja'afar gaba ya bashi lambar ƙawar ta ya tambaye ta Nabila, ita dai amsar ita ce ta jima rabon ta da ita, kuma tana kiran ta ba ta samu, dan haka yake ci gaba da kira dan Hajia ta ce su Alhaji da Yaya Bilal da u aunty Fa'iza za su je dan yin magana da Maman ta akan auren su.

Ta san lambar shi dama, dan haka tana ganin kiran ta ja tsaki ta yanke tare da cewa Mama "Wai Mama kin san wa yake kirana? Fahad ne fa."

Saida gaban Mama ya faÉ—i da jin sunan, amma ai ta dake tace "Fahad kuma? Dole ya kiraki mana tunda kin jefar da waccen wayar."

Taɓe baki tayi tace "Ba zan ɗaga kiran shi ba Mama."

Cikin nutsuwa ba tare da ta kalli fuskar ta ba Mama tace "Saboda me Nabila ? Ina ce duk kin bani labarin abubuwan da suka faru tsakanin ku, har da abinda aka miki a gidan su ma, ni sai nake ganin da gaske yana son ki, ki É—aga ki ji me zai ce miki?"

Katsewar da kiran yayi yasa Nabila kallon wayar sannan ta kalli Mama a tausashe ita ma tace" Mama, bana musun son da Fahad yake min, kuma na yarda da aurena da yake son yi, sai dai na ksa yarda ba hannun shi a cikin abinda aka min gidan su, Mama..."

Ta Kira sunan Mama da wani irin yanayin da saida Mama ta ɗan janye kanta ta juya ta kalle ta da kulawa, ɗorawa tayi da" Ban sani ba Fahad alkairi ne haɗuwata da shi ko kuma sharri, sai dai ya min alkairin da ba zan manta da shi ba a rayuwata, domin kuwa shine ya nuna min abinda muke yi ba kyau, sannan ya ce mu tuba ga Allah sannan muyi aure, hatta jiran ganin tsarki ɗayan nan da nake shine ya koya min, sannan..." Sai kuma tayi murmushi kafin ta ɗora da" Shine ya sa na sake dawowa gare ki, Mama a dalilin shi ne yanzu nake jin zan iya saka ƙafar wando ɗaya da duk wani abu da zai ɓata miki rai ko da kuwa bana da iko akan hakan."

Narai-narai tayi da idanu tare da sako da wasu hawaye masu zafi tace" Na fahimci mutanen gidan su ba sa ƙaunata, kuma ni na jawo wa kaina hakan, sai dai sun zurfafa ƙiyayar su gare ni, yayin da ni kuma da na kalli tsohuwar nan matar nan... Mama, mahaifiyar Fahad."

Sai kuma ta sake yin shiru, dan ita sai yanzu ne abun ya zo mata a rai, tunda jimawa tana tunanin da wanene? Ko wacece? Saboda bata tunanin a kusa da ita duba da ba wata alaƙa, amma yanzu da ta tuna aunty nata sai tayi saurin kallon Mama tace" Mama, wallahi mahaifiyar Fahad duk da tsohuwa ce, amma idan kika ganta yanayin ta sak irin na aunty Ummu, sai dai gaskiya ita bata da kirki ko kaɗan, hasalima ko murmushi ni ban ga tana yi ba."

Shiru Mama tayi na sakanni, kamar ba za t yi magana ba kafin ta numfasa tace" Allah sarki, kinsan akwai kamanni a duniya."

Kiran da ya sake shigowa ya sa Nabila kallon wayar sannan ta ja tsaki, hakan yasa Mama cewa "Nabila, ina ce yanzu kika gama faÉ—a min Fahad ya miki alkairi a rayuwa?"

Cikin kumburo baki tace "E Mama."

A nutse tace "To me yasa zaki saka masa da haka? A ƙalla ki ɗaga mana ya san halin da kike ciki, idan ya so sai ki faɗa masa ya fita a harkar ki."

Jinjina kai tayi tana É—aukar wayar tace "Shikenan Mama."

Sakin kan na Mama tayi tare da miƙewa ta nufi ɗaki, dan dole ta san za su buƙaci suyi sirri, da kallo mama ta bita duba da shigar dake jikin ta, riga da zane ne da kuma ƙaramin hijabin ta, wanda waje ma Nabila ta fita kusan tsirara bare cikin gida? Amma yanzu dake ubangiji yayi ikon sa gashi tana gyarawa.

Tun bata shige É—aki ba ta É—aga wayar tare da faÉ—in "Hello salama alaikum?"

*Fahad* dake ɗakin shi yayi baka-baja da shi saboda damuwa da ɓacin ran rashin sanin me yasa Nabila ke masa haka? A gigice jin an ɗauka ya miƙe tsaye yana ƙarasawa gaban madubi yace "Hello! Beela, wai ya kike min hakane? Ya zan ta kiran ki ki kashe min waya? Me yasa Nabila? Me na miki dan Allah?" kin kashe wayar ki kowa ya kiraki ya ce ba ya samu, na kira ki sau ba adadi da layina da na mutane ke har Mamie ma ta bani wayar ta na kira ki, amma amsa ɗaya ce wayar ki kashe."

Duj wannan dogon bayanin da jawabin, daga ƙarshe cike da basarwa da taɓe baki Nabila ta furta" Dan Allah wa ke magana? Ban gane murya ba."
Chapter 100 · 0% Book details