← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 168

Sashe 1

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

11/05/2023, 10:59 - Les messages et les appels sont chiffrés de bout en bout. Aucun tiers, pas même WhatsApp, ne peut les lire ou les écouter. Appuyez pour en savoir plus.
14/06/2023, 07:11 - Le délai avant disparition a été mis à jour. Les nouveaux messages disparaîtront de cette discussion ‎90 jours après avoir été envoyés, sauf s'ils sont gardés. Appuyez pour modifier.
29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*RUBUTACCIYA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

_NA_

*SAMIRA HARUN*

_SADAUKARWA GA_

*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_

_Bismillahir- rahamanir-rahim._

*1*

*WANI LOKACI*

Da gudu yayi niyyar fitowa daga falon dan neman agaji, ba dan biyayya da kuma sanin *Mu'az Mika'il* mahaifin sa bane, da a wannan shekarun nashi da ya fara kama ƙasa tsabar ƙarfi, da zai dambatu ne da shi komai girman sa, amma har yau har yanzu bai wuce yayi zaune mahaifin shi na shi na masa dukan mutuwar da ya saba yi masa ba a duk lokacin da matar tasa wato *matar babanshi* ta kawo masa tsegumin yayi wani laifin ko da kuwa bai yi ba.

Duk da ya so zillewa ya bar musu gidan, amma kasancewar mahaifin nashi wato Mu'az ƙaƙƙarfan matashi ne da bai kai a kira shi da tsoho ba duk da shi ne ɗan sa na farko sannan ya haura shekara arba'in da kaɗan, bugu da ƙari soja ne da ko a cikin sojawan yake amsa sunan Sergent sannan shugaban tawagarsa.

Ƙafar matashin yaron da a ƙalla zai kai shekara 14 ya cabko, hakan ya tilastawa yaron wata irin faɗuwa ya dabsu da ƙasa tare da gwara kan shi da murfin ƙofa, cikin raɗaɗin azaba yayi waa razananniyar ƙara ya dafe kan nashi yana kiran "Wayyo Allah na, Wayyo Baba kaina, kaina ya fashe."

Bai saurari magiyar da yake masa ba, tamkar yana jan wata dabba haka ya dinga jan ƙafarshi har saida ya ja shi zuwa ɗakin baccinshi ya rufo ƙofa, wannan ɗamarar (belt) tasu ta sojawa mai ƙarfin ikon ladabtar da duk wanda tsagerancinshi bai kai matakin gawurta ba ya cire daga ƙugunshi, kafin ka ce kwabo ya shiga zabgawa *Jabir* da tunda ya ji ya rufo ɗaki ya tashi zaune yana faman haɗewa jikin gado yana bashi haƙuri kan laifin da bai san ya aikata ba, dan shi dai yna shigowa gidan ya ji mahaifin nasa da bai san ma ya dawo daga daji ba ya ce ya wuce uwar ɗaki, shi kuma da ya ji haka yasan ba sirri ko hirar arziƙi zasu yi ba, Shiyasa ma ya nemi tserewa ya bar gidan.

Dukansa yake da wannan ɗamara, ba wai mutum mai rai ba, ko gawar wannan dabbar wato jaki ce ake ma dukan nan, wanda ke nesa ma kaɗai zai iya tsayawa yana zubar mata da hawaye, bare kuma idan kana jin gunji da sautin kukan da kai ka tabbatar yaro ne matashin da ya wuce wannan dukan. Tsabar ɗorawa kai wahala shi kan shi mahaifin nashi a wahalce yake matuƙa, dukan namiji da ya kai shekaru sha huɗu zuwa sha biyar hatsari ne, Shiyasa ma yake ta gumi kuma zaka rantse dambatuwa ne suke idan kana jin su daga waje saboda irin kwaramniyar dake fitowa daga ɗakin, dan Jabir dai ba zaune yake wuri ɗaya yana duka shi ba, ƙoƙarin kare jikin shi yake da riƙe ɗamarar, hakan ya jawo idan ya riƙe ɗamarar da kyau har ya kan kasa ƙwatarta sai ya dinga harbinshi da ƙafa yana kuma marinshi ta ko ina yana faɗin "Saki, saki nace, ba zaka saki ba? Ka rainani ko?"

Cikin azaba za ka ji Jabir yana cewa "A'a Baba, a'a wallahi, zan saki to, amma kayi haƙuri karka dakeni dan Allah, ka yi haƙuri ba zan sake ba koma menene."

Suna tsaka da wannan tirƙa-tirƙa aka ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin, cikin haki da masifa ya kalli ƙofar yace "Wa ye?"

Daga waje muryar matar tashi ita ma da yanayin masifa tace "Ni ce, ka buɗe ɗakin nan ku fita waje Baban *Uzeifatu*, wallahi tallahi idan kuka min ɓarna a ɗaki sai ka biyani, kaga fa haka kwanakin baya kuke karya min gado, da ƙyar ma ka samo min mai gyara, dan haka ku fito min daga ɗaki, sannan hayaniyarku tana hana min yarinya bacci."

Tabbas hargagin da take masa ya kai yasa ya haɗa da ita ya jibgeta, to amma ba zai iya hakan ba dan ita ce Hajiar gidan, ɓacin ranta daidai yake da rugujewar tattalin arziƙin gidanshi, hakan yasa tamkar wni ɗan zakin da bashi da haƙora ya amsa mata da" Shikenan, kiyi haƙuri to, ina fata dai Uzei bata tashi ba?"

Duk yayi maganar ne yana buɗe ƙofar ɗakin daya rufe da makulli, hakan yasa Jabir ma tasowa yana shahseƙa da sosar jikin shi suka fito, zaune suka same ta tana jijjigar Uzei da take so tayi bacci, kusanta ya zauna yana ɓalle botiran rigar shi tare da share gumin da yayi.

Jabir take Harare da ya kama hanyar fita daga falon, ganin hareren da take ma yaron duk da É—an cikin sa ne shi ya haifi abun shi yasa shi daka masa tsawa da cewa "Kai!"

A razane ya dakata yana kallon shi da jiran jin me zai ce, cike da gargaÉ—i da nuna shi da yatsa yake cewa "Maza ka É—auki jarkokin nan ka tafi yanzun nan ka debo mana ruwa, tunda ai kasan aikin ka ne amma ka tafi yawon ka baka É—ebo ruwan ba."

Da mamaki jin haka Jabir ya kalli *Bara'atu*, ruwa kuma? A kansu aka masa wannan dukan? Bayan bai tafi makaranta ba saida ya cika mata kaf abubuwan da take cewa sai ya cika mata da ruwa tsabar son ta sa ya makara har da kansu jarkokin guda biyu saida ya cika su ya aje sannan ya tafi, duk me aka yi da ruwan? Wannan kallon da yake mata yasa ta daka masa tsawar "Lafiya wai? Ni na saka aikin ne da zaka tsaya kana harara ta? Ka ɓace min da gani malam."

Zabura yayi sannan ya juya ya fita yana jin uban na faÉ—in "Za ka gane baka da wayo idan baka É—auko ruwan nan ba."

Kallonshi tayi cike da kissa da kwarkwasa tace "Baban Uzei, gaskiya ni yaron nan wallahi ya fara bani tsoro, ina gudun wata rana ya rufeni a É—akin nan ya zaneni, tunda Kaga kai ba zama kake ba, shi kuma yanzu ya idasa lalacewa duk ya zama wani iri, ni fa ina tunani kamar Jabir ya fara shan sigari."

A razane ya kalle ta ya maimaita kalmar" Sigari?"

Da son tabbartar masa ta ɗaga kai sannan tace" Ƙwarai."

" Jabir ɗin?" Ya sake nanatawa don abun a bazata ya z mishi, ko shi da yake ubansa kuma soja sigari bata taɓa birge shi ba, ba ma shi ba har da wasu daga cikin milyoyin sojoji, amma a ce ɗansa? Lura da kamar kokonton maganar ta yake yasa ta sake cewa" Kai baka ga idanun shi kullum jajir dasu ba kamar na mai shan wiwi, ga wata rama da yake kamar ana miya dashi, ni dai gaskiya ka raba ni zama da yaron nan."

Dafa kafaɗarta yayi a tausashe yace" Ki ƙara haƙuri kinji Bebe, idan fa kika duba shekara nawa ta rage ma na kaishi makarantar horon soja shi ma ya zama kamar ni, ai shekarun da kikayi dashi a baya yanzu ko rabin rabinsu ba zaku yi a tare ba."

Turo baki tayi gaba tana cewa" To ya koma can wajen su Mama da zama mana, dan nidai n'a gaya maka tsoro yake bani yanzu, ga rashin kunya da ya ƙara koya bana saka shi aiki kai tsaye yayi sai na sha wahala."

Cikin rarrashi yana shafa wuyan ta yace" Bébé ke fa kinsan komai, Mama ba zata taɓa haƙuri ta karɓi Jabir ba, kin fi kowa sanin muhawarar da aka tafka kan Mama ta karɓeshi bayan *rasuwar mahaifiyarshi* tun yana da shekara *huɗu* a duniya, bare yanzu da ya girma ya isa ya ma ka shi komai. Kiyi haƙuri duka Bebe, ina tabbatar miki zan ja masa kunne, ba zaki sake yi masa magana sau biyu ba idan zai miki abu, kin ji?"

Taɓe baki tayi tace" Shi kenan." A ranta kuma ayyanawa take _" Ina dalili ina ɗan mafari, an haɗani da jaraba tun ina amarya ko amarcina ban ci da kyau ba, to Kakar sa ma ta ƙi shi bare ni da ban haɗa komai dashi ba? Sa'ar sa ɗaya bamu zauna da uwar ta sa ba wallahi, da Ace ta min ba-daɗi da a kanshi zan rama wallahi."_

*Jabir* kuma na fita jarkokin ruwan guda biyu ya ɗauka hannun shi dafe da kanshi dake masa mugun ciwo mai raɗaɗi, a daddafe yake tunkurarar wurin ɗiban ruwan dake ɗan nesa da gidan amma ba sosai ba, tsoron hanyar yake ji sosai saboda sabuwar unguwa ce mai kama da dajin Allah, wurin nada haɗari sosai musamman yanzu da zafi yayi yawa, haka yasa ganin kunama da maciji a wurin ba wani abu bane, shi kanshi ya kashe wa matar babansa kunama tafi a ƙirga.

Tashin hankalinshi yanzu shi ne jiya tun da rana ba wanda yaje fanfon nan É—ebo ruw saboda macijin da aka gani a wuri kuma an tabbatar mai dafi ne, shi ne yanzu ba tare da tunanin komai ba mahaifinshi ya ce ya zo ya É—iba, bayan ya san ya cika mata komai da ruwa.

Da wannan tunanin yake tafe yana lumshe idanunshi saboda kanshi har yanzu zugi yake masa, sannan kuma idanunshi da kularshi duk suna kan hanyar ne, babu hasken fitila ko É—aya a dai nan layin nasu idan ba ka shiga kwanar gidan Alhaji *Kabiru* ba, ba dan babu wuta a gidan su ba sai dan unguwar ce babu mutane sosai, hakan ke haifar da duhun dake samar da rashin amince ga ma'abocin fitar dare a wannan unguwa.
Chapter 1 · 0% Book details