← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 162

Sashe 97

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Turaki ya girgiza kai yace “Your Highness zarginta kawai kake baka tabbatar ba, bakada k’wakk’waran shaida da zai tabbatar maka da hakan...!”

Idanunsa da suka kad’a sukai jazir naga kwalta yake furta “Bayan k’aryar da tayi mana, Iyayenta ma neman kai sukeda ita... Ai kai shaida ne tinda gabanka akayi komai... Wannan kawai ya isa na kuma aminta da cewa ita d’in ba mutumiyar K’warai bace..!”

Turaki ya girgiza kai yace “Mugaye sunyi yawa a duniyar nan, wasu idan har basu suka haifi yaro ba toh basu damu da duk halin k’uncin da zasu jefasa ciki ba, your Highness ya kamata kayi tunani akan hukuncin da kake k’ok’arin zartarwa... Nasan kana son yarinyar nan, kar kayi abinda daga baya zaizo ya dameka ...!”

Katsesa yai da fad’in “Bana sonta ban tab’a sonta ba kuma bazan sota ba..!!”

Turaki ya murmusa kad’an yace “Idan da baka sonta bazaka tab’a damuwa da al’amranta ba... Your Highness case d’in Muhibbah da Raheema ya banbanta, Raheema ka kamata dumu dumu ita kuwa Muhibbah zarginta kake wanda ni nayi imani can k’asan zuciyarka baka yarda zatayi duka wad’annan abubuwan ba... Nasan baka yarda ba Mahmood..!” Turaki ya k’arshe cikin sanyin murya..

Window kurum Mahmood yake duba Dan baiso ya yarda da kalaman Turaki... Shi hukuncin da ya yanke shine daidai... Idan har yana so Muhibbah Ta dawo cikin masarauta toh hanyar kenan ya aura mata wani cikin Masarautar kafin iyayenta su aurarta ga wani tinda idan tayi aure babu hali ta dawo cikin Masarautar, dole duk yanda zai ya nemama wani cikin Masarautar aurenta...! Ya k’arashe tinanin yana mai dunk’ule hannunsa sabida tsananin b’acin rai...
Muryar Turaki ya sinkayo yana fad’in “Toh idan ka aura mata d’aya cikin ‘yan uwanka ita kuma Raheemar fah... Wa zaka aura mata..?!”

Ba tareda ya dubesa ba yace “Idan Allah ya kaimu lokacin zakaji ko wanene mijin nata...!”

Turaki yai shiru yana duban abokin nasa ba tareda ya kuma cewa komai ba saima maida hankalinsa ga tuk’i da yayi....
**

MASARUTA

Giwa da mamaki take duban yanda halitta Jakadiya ya jirkid’e lokaci guda... Ko iya d’ago kanta batayi, Gata nan dai d’aure saman kujera iyaka jin jiki tayisa kam...
Ko Iya d’aga kanta Jakadiya batayi, Giwa kanta saida ta firgita da ganin yanda halittan Jakadiya ya sauya lokaci guda, bata tab’a tsammanin muguntan Jamal yakai wannan mataki ba... Jiki na rawa Giwa ta isaga Jakadiya tana k’ok’arin dungurinta take fad’in “Anya tanada rai..?!”

Jamal ya jinjina kai yace “Tanada rai Maami kawai alluran hutu tasha, nanda wasu sa’o’i zata farka...!”

Giwa tai mata K’uri tana duban yanda fuskar Jakadiya ya kumbura ga wata akwati d’aukeda tools a gefe... Dank’ari mak’ari, wannan wane irin azaba Jamal ya baiwa matar nan...

Giwa Ta dubesa tace “Jamal mai Jakadiya tai maka..?!”

“Amanata taci... Kuma kema taci amanarki don na tabbata ita ta taimakawa Ja’afar ya gudu...!” Ya k’arashe cikin huci...

Giwa Ta lumshe idanunta a hankali dan tasan tsanar Jafar ne ya shafi Jakadiya, Jamal zai iya yin komai akan yarinyar nan Umaima...
“Toh amma ya akai ka Sani....?!” Giwa ta tambaya tana mai tsaresa da idanu...

Mayafin Jakadiya dake aje gefe ya nuna mata yace “Kin gani wannan ne shaida...!” Take ya labartawa Giwa duk yanda abin yake...

Giwa Ta d’aga mayafin tana juyawa... Ko shakka babu bai kamada mayafin bayi ba, duk yanda akai wannan ba na Jakadiya bane... Akwai wata k’ulleliya, amma bazatace komai ba har sai Jakadiya ta farka.... Da k’yar ta shawo kan Jamal ya sassautawa Jakadiya da irin uk’ubar da yake mata, Kwanceta yayi ya ajeta a nan d’akin had’ida treating duk wasu wounds dake jikinta... Giwa kanta saida ta tausayawa Jakadiya Dan ko motsi bata iya yi... Haka suka fice suka barta rufe nan cikin d’akin kafin alluran su saketa ta farfad’o....

**

Sharkaf da zufa tamkar babu AC cikin d’akin haka ya farka daga baccin nasa, mafarki yayi wata Murya da baisan daga ina bane tana fad’i masa Maiyasa zai zamto mai munana zato da mummunan zargi ga mutanen kirki... Da yawa daga cikin zato zunubi ne, kuma sashenta ba gaskiya bane..!

Ya shafe fuskarsa da tafukan hannayensa mafarkin na dawo masa daki daki... Wasu mutanen kirki ne ya munana masu zato..? Tambayar da zuciyarsa tai masa... Toh kodai Yazeed ne..? Ko Raheema ce..! Toh amma ya kamasu red handed ba zato yake masu ba.... Take yaji zuciyarsa Ta ambato masa MUHIBBAH...

Ya lumshe idanunsa a hankali yana mai kuma shafe fuskarsa, Toh idan sashen zaton nasa ya zamto gaskiya fah...?
Wata b’angare na zuciyarsa ta basa amsa da fad’in Kai da kanka ka kasa aminta cewa zatai abinda kake zaton ta aikata...!

Ya fuzar da fuci mai tsananin d’umi tunanin na kuma damunsa, duk yanda yaso ya yakishe tinaninta cikin zuciyarsa ya kasa... Dik yanda yaso ya amince cewa ita d’in mutuniyar kirkice ji yake bazai iya hakan ba musamman da Zahra ta sanar dashi duk wasu shawarwari da Muhibbah taita bata tin daga fari, har cewa da tai ta tambayesa a cikin mutanen da yake jin nauyinsu... Kenan Muhibbah itace Ta tunzuro Zahra tai masa abinda tai... Gaba d’aya sai yana jin bazai iya aminta da ita ba bayan all that he learned about her... Da k’yar ya iya mik’ewa ya nufi bayi Don d’auro alwala....

**

Giwa sai faman safa da Marwa take a k’uryar d’aki Jamal na gefe yana juya mayafin, kenan Zahra itace Ta baiwa Jakadiya...!

Jamal ya dubi Giwa yace “Maami amma Zahra bazata iya lek’en asiri cikin d’akina ba... Maiyasa ma zatayi haka...? What could be her reason..?!”

Giwa tai shiru tana nazari sai kuma tace “K’warai Zahra bazatayi duk abinda ka zayyano mai wannan mayafin tayi ba, duk yanda akai akwaita a k’asa... Kodai akwai wata ‘yar lek’en asiri cikin Masarautar nan ko kuma bata cikin Masarautar amma tana amfani da Zahra...!”

Jamal yai shiru kaman mai nazari sai kuma yace “Maami karki damu, I’ll talk to my niece a nitse nasan zata sanar dani komai... Kinsan na k’ware a iya shan cikin mutane Dan naji labari...!”

Giwa ta murmusa tace “Hakan yayi Gwarzo na... K’warai na yarda dakai.... Idan muka sami wacece wannan ‘yar lek’en asirin...”

Jamal ya katseta da fad’in “Horon da nayima Jakadiya sai ya zamto horo mafi rahama a gareta... Sai ta zab’i mutuwa da rayuwa...! Sai ta tsuguna kan gwiwoyinta tana rok’on na kasheta don hakan sai Yafi mata sauk’i kan irin azaban dana tanadar mata..!!”
Ya k’arashe yana tsananin huci jijiyoyin jikinsa na kuma fitowa...

Giwa tai masa K’uri tana sakin wane irin murmushi na jin dad’i...

**

BAUCHI

Iatakam tasha mamakin ganin Mommy Ta sauk’o daga dokin fushinda ta d’ale, har idan ta shiga gaisheta bata korinta, ganin yanzun ma bata koreta ba ya sanyata zama daga can gefe wajen k’afafun Mommyn... Dak’ik’ai suka d’an shud’a kana Muhibbah ta soma fad’in “Mommy zuwa nai na miki bayanin komai dalla dalla ba tareda na b’oye miki wane abu ba...!”

Mommy ta katseta da fad’in “A’a Hibbah ni bana son naji komai balle ma bak’in labari, kedai kije kuci gaba da shirin biki Keda k’awayenki kinga babu wani sauran time kwanaki ne kawai suka rage, duk abinda kuke buk’ata ku sameni, idan bazaki iya samuna ba Meenatu Ta sameni... Bana son na kuma jin kin tono zancen nan... Allah ya baku zaman lafiya a gidajen aurenku...!”

Jiki a sanyaye Muhibbah Ta amsa da “Ameen Mommy..!” Allah ya gani tana son Mommy ta bata chance ta sanar da ita labarinta daga farko har had’uwarsu har kawo yau, tayi imani Mommy zata fahimceta amma tak’i bata wannan daman ko menene dalilinta... Wata zuciya tace k’ila bataso taji yanda akaci zarafinki ne... That’s how much she loves you.... Bata ida tunanin ba Aunty Gudidi tai sallama tana rangad’a gud’a tafe da wasu ‘yan Office d’in su Mommy guda biyu wanda duka k’awayensu ne...

Muhibbah ta gaishesu Aunty Gudidi harda rungumarta tana nunawa K’awayen nasu ga d’aya amaryar dashike Mommy Ta sanar da ita yanda sukai da Yawale akan Muhibbar... Itadai Muhibbah sai mamaki take yanda Mommy da k’awayenta suka canza lokaci guda... A b’angaren Ansar ma yaji dad’in hakan don tuni sukaci gaba da shirye shiryen biki, har can gidan Baffah Yawalen ma yaje da yaga sun saduda sun amince ya auri zab’insa hakan yasa yai alk’awarin bazai watsa masu k’asa a idanu ba suma zaibi umarninsu a matsayinsa na iyayensa koda hakan bazai faranta masa ba...

**

A can masarauta ma shirye shirye ta kankama, Mahmood ya sanar da Giwa harda auren Jamal da Umaima duk za’a had’a a d’aura, Giwa bata damu ba tinda tasan sunada shirinsu na musamman akan Umaimar, hasalima tuni tasa aka killace Umaima Kuyangi na kula da ita na musamman, wannan dalili yasa sam itada Jamal basu sami damar yin magana da Zahra ba Dan tsananin Farin ciki da Jamal Ke ciki ma yasa ya mance da batun tambayar Zahra, Giwa kaw Ta bada Himma ne sosai wajen ganin Jakadiya ta warke dan tunk’aran Tal’udu dole saida Jakadiya batasan wannan zuwan wane sassan jikinta ne zaici wuta ba musamman sanin yanda sukai baram baram da Tal’udun a had’uwarsu ta k’arshe....

**

Yau d’in Ta kama Alhamis kwanaki biyu tak suka rage a d’aura aurarrakin... Turaki na gefensa yana ci gaba da karantarsa, koda ganinsa kasan babban al’amari ke damunsa...

D’an gyaran murya Turaki yai yace “Your Highness, da an k’ara duba lamarin nan daga gobe ne fah ake saka ran d’aurin auren nan.....!”

Ba tareda ya dubesa ba ya jinjina masa kai a hankali “Na riga na gama magana Turaki, my decision is final... Dani dakai zamu tafi mu karb’o auren yarinyar Dan ina buk’atarta a cikin Masarautar nan... Sannan zan wakilta Galadima da Sardauna harma da Hakimai kaman guda uku su tafi Masarautar su Raheema su karb’o aurenta itama...Waziri dasu Matawalle da Liman zasu tsaya a nan su d’aura auren Jamal.... Haka na tsara tafiyar....!” Ya k’arashe yana murza zobban hannunsa a hankali...

Turaki ya had’iyi miyau da k’yar yana mai jinjina kai Dan yasan wannan hukunci da abokin nasa ya yanke dole nadama ya biyo baya....
Fatansa bai wuce Allah ya shiga lamarin ba ya tabbatar da ikonsa akan komai....

**

RANAR ASABAR 29 GA WATAN AFIRILU...
Chapter 97 · 0% Book details