← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 162

Sashe 102

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga nan ban kuma tsayawa saurarensu ba na nemi hanyar tsira... Na k’ulle ‘yan kayyakina da niyan barin gari koda kuwa zan sami k’alubale... Cikin daren na nemi Umaima dan nayi mata sallama a yanda muka saba had’uwa saidai wannan had’uwar cikin dare mukayi dan bazan bari gari ya waye min cikin Masarautar ba... Dan nayi imani kafin wayewar gari mugayen mutanen nan zasu iya zartar mugun nufinsu akaina...! Ban samu damar mata bayani ba saidai nace tai k’ok’ari Ta cireni cikin zuciyarta Ta mance dani... Taci kuka sosai kaman bazata k’yaleni na tafi ba... Haka dai na bata hak’uri nace Ta mance dani zanyi nesa da Masarautar nan...! A haka mukayi sallama da Umaima na tafi na barta tana kuka...

Saidai Ina k’ok’arin guduwa daga cikin Masarautar naji an rad’eni da sanda an buga min sanda akai na fad’i sumamme... Ban kuma farkawa ba sai a cikin wani d’aki mai duhuwan gaske yanda naga D’an Sarki Yarima Jamal ashe shine ya dakeni da sanda ya kawo ya d’aure da sark’ok’i yana azabtar dani saidai kullum dare sai ya kawo min abinci a tsawon shekara guda da nayi rufe wajen har kawo ranan da kuka kub’utar dani cikin ikon Allah..!”

Ya k’arashe yana mai sauk’e ajiyan zuciya...!

Jafar yaci gaba da fad’in “Sun kashe Mai Martaba..! Kuma basu bari ya sanar dani abinda yake son sanar dani ba..! Sunyi zalunci mafi muni cikin Masarautar..!!”

Baba Nomau yana mai girgiza kai yake jinjina zalunci irin na Giwa...

Ubandoma yai shiru kaman mai nazari... Ya sani shi da hannunsa ya canza Jariri Ja’afar da d’an Bawa Sarkin Dawakan cikin Fada... Kardai Jafar d’an Sarki AbdulJabbar ne Giwa Ta damk’a masa ta umarcesa ya canza da gawan jaririn Sarkin Dawakai... Tabbas Giwa ta basa jariri a tsumma wanda baisan daga inda ta samo ba kuma ta umarcesa ya canza wannan jaririn da Jaririn Sarkin Dawakai wanda daga jaririn har uwar jaririn Ta kashesu... Ta kuma sanyashi ya kawo mata gawan jaririn amma banda na uwar yaron...! Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..! Yasan yayi mugayen ayyuka ma Giwa amma wannan yana d’aya daga cikin aikin da bazai tab’a mancewa ba sabida ya shafi jariri wanda baida hakkin kowa, hakan yasa tun tasowar Jafaru cikin Masarautar yake k’aunarsa dan yasan shi ya canzasa da d’an sarkin Dawaki bayan Giwa ta kawosa cikin Masarautar... Toh ina Giwa takai wancan gawan Jaririn da ya kai mata wanda ta saka shi ya canza da Jafar... Kenan Ta aje Jafar ya rayu da Sarkin Dawakai kan cewa uwar Jafar matar Sarkin Dawakai Ta mutu Ta bar jinjiri a raye kenan.. Bayan kuma ya sani Matsafan Giwa su suka kashe Matar Sarkin Dawakai da jaririnta, Giwa ta karb’i gawan jaririn ta canzasa ma uwar Jafaru... Toh Wai ma wacece Uwar Jafaru da Giwa tayi wannan badak’ala da d’anta... Maiyasa ta canza mata d’anta da macacce..?!”

*MUHIBBAH*

*63*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

A hankali take jin idanunta da suka matuk’ar mata nauyi suna bud’ewa... Ta saka hannayenta tana murtsuka idanun nata... Tin daga kan gadon da take kwance bisa ta soma bi da kallo har izuwa d’akin da take ciki... Ta d’aga kanta sama sosai tana duban d’akin wanda yafi mata yanayi royal bedroom, komai na cikin d’akin gwanin ban sha’awa ne da burgewa... Ta kuma mik’ewa zaune sosai tana mai kuma k’are ma tangamemen d’akin kallo, ga kayan ado na alfarma da aka k’awata d’akin dasu... Toh inane nan...? Yama aka tazo nan, ita abinda zata iya tunawa shine tana zaune rik’eda Taswiran da mahaukaciyar nan ta damk’a mata tana kallo tana hawaye tana ayyanawa cikin zuciyarta shikenan Allah ya nufa bazata San dalilin da yasa matar nan ta bata taswiran ba kwatsam Aunty Gudidi ta shigo da wani had’i cikin cup tace da ita maza ta kafa kai ta shanye yanada kyau wa amare..! Koda taji shigowar Aunty Gudidi sai tayi saurin dunk’ule takardan cikin hannunta.. Ta amshi cup d’in da d’aya hannun Ta kafa kai ta shanye abinda Aunty Gudidi Ta umarceta da Ta shanye, tin daga nan bata kuma sanin ina take ba tasan dai kaman bacci ne yayi awon gaba da ita...! Toh mai ya faru tinda tayi baccin..?! Kenan ta jefar da zanen garin bacci ba tareda ta sani ba..! Toh Wai ma ina sauran mutanen suke, ina k’awayenta ina Ansar.. Ina Mommy..? An d’aura auren ko ba’a d’aura ba..? Waima a wace duniyar take ne..??! Tambayoyin da Ta dinga jerowa kanta kenan...

Ta mik’e k’afafunta a hankali ta sauk’o saga saman gadon tana mai taka cikin d’akin kaman mai tsoron tafiya... Allah ya gani kanta ya d’aure Ta rasa meke wakana a rayuwarta... Ta isa jikin window a hankali tasa hannunta kaman mai tsoron kada a ganta ta d’an janye labulen... Nan ne gabanta yayi wane irin yankewa ya fad’i, ta sake shafe idanunta domin tabbatarwa.. Cikin masarauta Ta dawo..? Waye ya dawo da ita..? Shin kodai Giwa tabi sawunta ne ta dawo da ita bayan ta fahimci itace Saudatu..? Kodai Fu’ad ne ya sanar dasu itace Saudatu kuma tana raye shine suka bita har gida suka saceta ranan aurenta suka dawo da ita cikin Masarautar..! Tinani barkatai taketa faman yi tana sak’awa tana warwarewa... Da alama daga ita sai suturan dake jikinta tazo... Gashi babu wayarta a tareda ita balle tayi k’ok’arin kiran Ansar taji meke faruwa.. Ita kam gaba d’aya kanta ya k’ulle....

Tana nan tsaye wasu bayi ‘yanmata guda uku suka turo k’ofa suka shigo... Gaba d’aya suka zube har k’asa suna kwasan gaisuwa wajenta...

Muhibbah tabisu da kallo cikeda mamaki tana ganin abin banbarak’wai... Bayin cikin Masarautar sun saba duk’awa suna gaisheta amma yanda wad’annan suka zube gaba d’aya gabanta lokaci guda sai taga abin yayi mata wane iri...

Ta kasa furta komai sai binsu da kallo da take... ‘Yar babbar matar daga cikin Kuyangin ta bud’e Murya tace “Sunana Kande sunan wancan Julde, ita kuma wannnan sunanta Hasiya.. Mune masu kula da al’amaranki da duk abinda kike so Ya Shugabata..! Ga ruwan zafi mai k’amshin furanni an shirya miki a ban d’aki Ki shiga kiyi wanka..! Idan kika fito sai ki sanar damu kalan abincin da kike so a kawo miki..!”

Izuwa lokaci Muhibbah ta soma k’osawa da wannan karatun da Baiwar ke karanto mata wanda bama fahimta take ba, hakan yasa ta katseta da fad’in “Wa ya baku umarnin kuyimin wannan hidima..? Kuma Maiyasa aka kawoni nan aka ajeni..?”

“Ki gafarceni ya Shugabata.! Umarni muke bi muma, idan kinyi mana izini zamu baki waje domin Ki kimtsa..!” Ta k’arashe kanta a k’asa...

Muhibbah tai shiru yana dubansu ba tareda Ta kuma cewa komai ba... Can kaman bazatayi magana ba sai kuma tace “Ina son sanin umarnin wanda kuke bi...!”

Kuyangar Ta murmusa kad’an tace “Zan sake neman gafara a gareki.. Ki gafarceni Rankaidad’e amma sanar dake umarnin wanda muke bi ba huruminmu bane... Aikinmu kad’ai shine kula dake... Allah shi taimakeki..!!”

Takaicin Kuyangar ya kama Muhibbah sanin cewa ita Amarya ce ta tabbata mijinta da Mommy suna can suna neman duniyar take wannan matar ta zauna tana mata wani fadanci maras dalili...

Ta dubi sauran bayin ‘yanmata guda biyun tace “Ku kuna iya tafiya amma Ke ki tsaya..!” Ta k’arashe tana nuni da Babbar wacce ta gama mata magana...

Suka dubi shugabar kuyangar tasu ta jinjina masu kai alamun suje.. Take suka kuma duk’awa alamun girmamawa ga Muhibbah kana suka fice...

Suna ficewa Muhibbah ta k’araso gaban Matar tana dubanta, lokaci guda kuma Ta zauna dirshan a gabanta itama, cikin yanayi kaman Ta mai son yin kuka Ta soma fad’in “Dan Allah Ki taimakeni..! Kada Ki bari azzaluman Masarautar nan su cimma burinsu akaina.. Wllhi nasan kasheni sukeda niyya... Kinga ni Amarya ce yau ake d’aura aurena suka sato ni.. Kin gani kinga k’unshi na kin gani dan Allah Ki taimakeni kema mace ce ki tai..!” Gaba d’aya tamkar wacce bata a hayyacinta haka yake maganganun tana nunawa Kuyangar lallen hannuwanta tana kwaye zaninta tana nuna mata na k’afafunta alamun tana tabbatar mata da cewa ita d’in Amarya ce..

Saurin rik’o hannunta Kuyangar tai ta dakatar da ita da fad’in “Kiyi hak’uri Rankidad’e, ni kaina banida bayanin da zan miki a halin yanzu.. Abu guda da na sani shine zaki rayu a nan na d’an wani tsawon lokaci... Watak’ila Ki samu amsoshin da kike nema..!!” Ta k’arashe tana mai mik’ewa tsaye, Ta risina alamun girmamawa tace “Zan jiraki daga waje har ki gama kimtsawa..!” Ta k’arashe kanta a k’asa...

Muhibbah tana gani Kuyangar nan ta fice ta barta nan zaune dirshan a k’asa wani irin kuka had’ida tausayin kanta na zuwa mata... Meke faruwa da ita..? Shin kodai nan ba Masarautar data sani bane.. Ko wasu mutane ne daban..! Innalillahi wa Innalillahi raji’un..! Shi take nanatawa cikin zuciyarta... Ta mik’e da sauri ta isa jikin window ko zata hango wasu mutane tayi ihun taimako... Toh amma idan tayi ihun taimako tasan babu mai taimakon nata tinda mutanen da suka ajeta a nan dole sun bata tsoron da bazata iya guduwa ba... Allah ne kad’ai zai ceceta daga wannan uku d’in data tsinci kanta ciki... Ta koma kan gadon ta zauna ta tak’ure waje guda tana kuka sosai...

Daga nan cikin d’akinsa yana zaune saman sofa k’afarsa d’aya bisa d’aya yake kallon duk wani movement nata a makeken na’uran nasara dake gabansa wanda k’ank’anuwar camera dake cikin d’akin nata yana nad’o masa komai ya nuna masa...

Yai mata K’uri yana duban yanda take cazgan kuka... Ta kuma mik’ewa ta nufi window harda ‘yar k’ok’arin tsallanta alamun tana son ta bud’e tagar tai escape... Yanda take tsallen yaso basa dariya amma bai dariyar ba sai ma saita remote da yayi ya kashe na’uran...
Chapter 102 · 0% Book details