← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 162

Sashe 50

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Majidad’i ya dubesa shaye da mamaki yana nazarin maganar.. Lokaci guda yake girgiza kai yana mai furta “Ta yuwu shi yakai kansa babu wanda ya turasa tunda wannan gida namu kowa ba abin yarda bane... kuma babu irin bugun da banyi masa ba dan ya fad’i Waye ya turo shi amma ya sanar dani babu wanda ya turo shi..!”

Yazeed ya kuma sakin wata murmushi yace “And you believe him...?” Yai tambayar yana mai tsare Majidad’i da idanu.... Lokaci guda ya kuma sakin murmushi ganin ya jefa Majidad’i cikin shakku da kokonto, Yazeed yaci gaba da fad’in “Ubandoma Hadimin waye... Waye Ubangidansa...?!”

Majidad’i na tsananin sakin huci ya d’ago yana duban Yazeed... Lokaci guda cikin karaji yake furta “Yarima....Mahmood..!!!”

SameenaAleeyou 📚
[7/16, 5:34 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*

*034*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Yazeed ya kuma sakin murmushi yana mai jinjina kai “Tabbas Mahmood is behind all this, shine silan ciwon mahaifinka... Zai iya yin komai dan yaga ya mallaki sarautar nan Ta ko wacce hanya ce, gashi ya soma da mahaifinka... Wannan dama ce ta samemu muyi amfani da ita wajen kaisa k’asa...!” Ya k’arashe yana sakin huci a hankali...

Majidad’i ya d’anyi shiru tamkar mai nazari sai kuma ya nusa yace “Toh amma kan wane dalili Mahmood zai cutar da mahaifina... Da ni da kai munsan cewa tun daga fari mahaifina is being very supportive to Mahmood, Toh kan mai zai nemi rayuwar mahaifina bayan shid’in ya zabi ya goyi bayansa yayi sarauta sama dani da nake d’ansa....?!”

Yazeed ya daidaita tsayuwarsa hannayensa hard’e ta gaba ya d’an turo k’irjinsa gaba kad’an irin tsayuwar da masu mulki keyi... “Da alama har yanzu baka fahimci yanda al’amara Ke gudana cikin gidan nan ba... So tari a gida irin namu mafi kusanci dakai shine mak’iyinka, wanda ka aminta dashi can easily betray you... Correct me if I’m wrong..!”

Jinjina kai Majidad’i yai yana mai kuma karantar Yazeed lokaci guda yace “Kana tunanin Mahmood could be behind my father’s illness..?!”

Yazeed ya saki murmushin cin nasara yana mai ware hannayensa “Isn’t it obvious..? Ai a bayyane yake Mahmood shine sila, da umarninsa Ubandoma ya shiga gidan Wambai... And believe me idan bakai komai akai ba sai Sun kashe Wambai har lahira...!”

Majidad’i yace “Toh yanzu miye abunyi Ta yaya zamu kama Mahmood da laifin idan har ba Ubandoma bane ya fad’i cewa da umarninsa ya kutsa gidan Wambai kuma shine bak’on Buzu...?!”

Yazeed ya murmusa a hankali kana yace “We make him talk... We gonna make sure he rats Mahmood out... Dole mu tabbata ya fad’i cewa Mahmood shine yai masa umarni da ya shiga gidan Wambai... After all, haka zancen yake tunda Ubandoma Hadiminsa ne...!” Ya k’arashe babu alamun jin k’ai ko imani cikin k’wayan idanunsa...

Jinjina kai kurum Majidad’i yake cikeda tsanani tsanar Mahmood “Zan d’auki fansar ciwon mahaifina zan tabbata Mahmood bai zama sarki ba sannan sai ya tafi gidan Yari har tsawon lokacinda mahaifina zai kwashe a kwance....!”

Yazeed ya saki murmushi yana mai furta “Impressive..!! Yanzu abinda ya kamata muje muga Ubandoma musan ta yanda zamu b’ullo masa..!”

Babu musu Majidad’i ya jinjina kai kana yabi bayan Yazeed suka shige cikin Fursuna...
**

Dogari guda ne ya k’araso cikeda risinawa ya bud’ewa Mahmood gark’amemen k’ofar fursunan da aka rufe Ubandoma ciki wanda sai ka shige manyan k’ofofin k’arfe har kusan guda uku kafin ka cimma d’akinda Ubandoma Ke ciki.....

Ubandoma na hango Yarima Mahmood ya shiga sanne kansa ya zube gwiwoyinsa ya had’e hannayensa waje guda yana fad’in “Rankaidad’e dan Allah ka ceceni kamin rai ka fitar dani daga wajen nan... Wllhi banida laifi sahun b’arawo na ta...!” Hango tsagwaron b’acin rai saman fuskar Mahmood wanda bai tab’a ganin irinsa ba tattaredashi tsawon zamansu tare ya sanyashi saurin had’iye zancensa gumi naci gaba da tsartsafo masa...

Yazeed da Majidad’i da k’arasowarsu wajen kenan tin daga k’ofa Yazeed ya umarci dakarun dake tsare da fursunan da su bud’e masu suga Ubandoma...

Dogarin ya risina yace “Allah shi taimakeka Mai Girma Yarima Mahmood yana ciki bazamu iya barinku ku shiga ba...!”

Wani jahilin duba Yazeed ya watsa masu “Kun kuwa San ko ni wanene...? Kun kuwa San da waye kuke magana..?!”

Dogaran suka kuma risinawa d’ayan na fad’in “Umarnin Yarima Mahmood ne kuma zab’ebb’en sarki na gaba Allah shi taimakeka... Wannan ba umarninmu bane...!”

Yazeed da Majidad’i suka dubi juna... Yazeed dake tsananin huci yana k’ok’arin damk’o wuyan Dogarin Majidad’i yai saurin taresa kana ya d’aga bakin rigarsa kad’an zarkwad’ed’iyar wuk’a mai tsananin shek’i sabida kaifi Ta bayyan...
Dodagarin ya had’iyi miyau da k’yar dan tsoro yana mai k’ifta idanu... Lokaci guda ya matsada baya yana mai basu hanya...

Yazeed ya dubi Majidad’i yace “Zaifi kyau idan ka jirani a nan... Shiganmu a haka mu biyu zaisa Mahmood ya zargi wani abu....!”

Majidad’i ya jinjina kai kana ya koma da baya ya bar Yazeed ya soma shigewa...

**
Mahmood ya girgiza kai yana duban Ubandoma lokaci guda ya d’an gyara tsayuwarsa yana mai fad’in “Kai nake saurare, ka sanar dani gaskiyar Al’amari idan har kanaso na taimakeka..!!”

Ubandoma ya kuma goge gumin dake ci gaba da karyo masa, Ta ya zai soma sanar da Mahmood ga abinda ya kaisa gidan Wambai, Ta yaya zai soma sanar dashi zancen Giwa da Waziri yaji har ya jefasa a ukun da ya tsinci kansa... Sanar da Mahmood gaskiya na nufin tono komai na Masarautar kenan... Idan har ya sanar dashi ga shirin Giwa da Waziri komai ya riga ya lalace kuma yayi imani hakan na iyayin sanadiyan rayuwarsa tinda yasan wacece Giwa ballantana Waziri...

“Kai nake saurare Ubandoma..!!! Wai ma tsaya tukuna, who are you..? Wanene Kai..? Ka sanar dani idan akwai wanda kake munafunta dashi cikin Masarautar nan..!!” Ya k’arashe cikin tsananin zafin rai...

Ubandoma ya shiga girgiza kai yana furta “Allah shi taimakeka BillahilAzim bani ha’intarka da kowa... Ka yarda dani Rankaidad’e, ka min rai ka cireni daga wajen nan..!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya yana mai k’ank’an da kai...

Girgiza kai kurum Mahmood yai kana yace “Had’in kanka shi kad’ai zai bani damar taimakonka Ubandoma... Amma a halin yanzu ni kaina ban yarda dakai ba, inada kokonto da tarin shakku akanka... Zan baka nan da kwanaki Uku Ubandoma, ka gama dik tinanin da zakai... Idan ka zab’i ka fad’i gaskiya watak’ila ka tsira da mutuncinka amma idan ka zab’i akasin haka... Kafi kowa sanin zaka dawwama cikin k’ask’anci a gidan Yari har lokacinda Allah zai baiwa Wambai lafiya ya bud’e bakinsa ya fad’i komai...!”

Daga haka juyawa yai da niyya ficewa Yazeed dake mak’ale daga gefen gini ya gama sauraren duk abinda suka fad’i, shiru yai yana nazari... Kenan Ta tabbata ba Mahmood bane ya tura Ubandoma..? Kenan akwai wani wanda Ubandoma yafi aminta dashi a Masarautar sama da Mahmood... Idan ya fahimci wani abu tabbas akwai wanda yake son ganin bayan Mahmood cikin Masarautar fiyedashi... Toh wanene wannan wanda Ubandoma kema aiki... Waye mak’iyin Mahmood har haka..? Lallai ya zama dole yasan ko wanene wannan...?! Ya k’arashe tinanin yana mai juyawa da baya shiga wajen Ubandoma da baiyi ba kenan... Dole yai shiri ya kuma San takunsa da alama Kuraye sunyi yawa a Masarautar tasu... Mahaifiyarsu tana cen tana fatan Mahmood ya d’ale Karaga ashe akwai wani wanda Ke cin dunduniyarsu basu sani ba.. Yayi imani Giwa batasan Ubandoma na munafuntar d’anta da tafi so da sarauta ba...!
Shafa hab’arsa yake a hankali yana nazarin waye ke son ganin bayan Mahmood sama dashi irin haka a cikin Masarautar..!?

**
Mahmood yana fitowa yaceda Dakaru masu tsaron Fursunan kar su bari wani ya gana da Ubandoma har nan da tsawon kwanaki uku, dan yasan idan aka bari kowa yana shiga munafukin da Ubandoma ke masa aiki zai iya tsoratasa har ya canza niyyansa na fad’in gaskiya tinda ya kula kaman Ubandoman ya soma karaya da alama zai fad’I gaskiya bayan kwanakin da ya d’ibar masa cewa yai shawari da zuciyarsa....

**

Wayar mak’ale kunnenta na b’angaren hagu ta kuma sauk’e huci a karo na biyu, saida ta canza wajen zama kana taci gaba da fad’in “Ansar I’m quite certain matar nan sunana Ta kira... She knows me Ansar... Duk yanda akai ta sanni... Tambayar a nan shine wacece ita..?!”

Daga d’aya b’angaren Ansar ya fuzar da fuci a hankali kana yaci gaba da fad’in “Hiba kiyi tinani maybe kin tab’a saninta a shekarun baya, watak’ila tun tana cikin hankalinta kafin lalurar hauka ya sameta... Kiyi tinanin mutanen da kikai rayuwa dasu a shekarun baya...!”

Shiru tai tamkar mai nazari sai kuma tace “Ansar bazan iya tunawa ba, bazan iya tuna sanin wata mace mai yanayinta ba... The only thing da na sani shine inajin wani babban al’amari gameda matar sannan inaso na taimaketa bayan haka inason sanin asalin labarinta da kuma yanda akai Ta k’are rufe a cikin wannan masarauta..!” Ta k’arashe maganar cikin rawar murya..

Shiru na d’an dak’ik’ai suka gifta kana Ansar yace “I have faith in you Hibbah... Nasan duk wad’annan abubuwan da kika saka gabanki da izinin Allah zaki Kai k’arshensu... Addu’ata da soyayyata na taredake ko yaushe kinji koh, dan haka Koda wasa kada Ki karaya...

Jinjina masa kai tai a hankali tamkar yana ganinta kana sukai sallama cikeda kewar juna... Takardan zanen da mahaukaciyar ta damk’a mata Ta d’auko Ta ware tana kuma k’are masa kallo.. Ya kamata taje sashen Giwa ta had’e zanen waje guda don ta tabbatar ko iri guda ne...
Mik’ewa tai ta soma shirin nufa sashen Giwa...
**

Cikeda ladabi Jamal ya k’araso gaban Giwa yana sauraren kiran gaggawa da tai masa...

“Ina zanen yake..?!” Ta tambaya cikeda kulawa...

“Maami wane zane kenan...?!”

Fuzar da fuci tai a hankali kana tace “Jamal sanin kanka ne Masarautar nan babu lafiya akwai wanda Ke mana zagon k’asa.. Na tabbata yana nan yana neman zanen nan... A ina ka ijiye...?!”

D’an jim yai kana yace “Maami na kyautar...!”

“Ka me...?!” Giwa Ta tambaya tana dubansa

“Na kyautar Maami...!”
Chapter 50 · 0% Book details