← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 162

Sashe 55

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

D’an Aiken Waziri ya dafe k’uncinsa yana sosawa sabida zafin marin lokaci guda yake fad’in “Allah shi taimakeka wllhi nemansa nayi na rasa nadai ga kaman wani gida ya shige daga nan ko k’yallin motarsa ban kuma gani ba...”

Waziri yaci gaba da sakin fuci yana aika masa jahilin kallo... “Tashi ka b’ace min a nan kafin nai maka horonda ruhinka zai gaza d’auka...!!”

A d’ari d’an Aiken ya mik’e a guje yana mai ci gaba da sosa fuskarsa...

Waziri ya dafe kumkuminsa da duka hannayensa biyu, Ta yaya zai soma sanar da Giwa wannan batu... Inaa ko kusa bazai sanar da ita Sun sami mishkila ba gwara ya bada himma a k’ok’arin kawarda Ubandoma da suke k’ok’arin yi... Buge babbar garensa yai ya shige cikin sauri tamkar wani zai kifa k’asa...

**
Yazeed yai K’uri yana duban Majidad’i dake tsaye gabansa yanaci gaba da sakin fuci “You mean my brother was here...?!” Ya tambaya yana duban Majidad’in...

“Maimaita maka kake so na sakeyi... Wllhi idan mahaifina ya mutu alhakin mutuwansa nakan Mahmood ne... Shine ya kashe Wambai...!” Ya k’arashe cikin tsananin fuci...

Yazeed ya jinjina kai cikeda jin dad’i yace “Zuwa yai to finish what he started... To kill Wambai... Kar ka damu kaji da mahaifinka ni zanji da wancan munafukin Hadimin Mahmood d’in ya k’arashe yana mai d’an bubbuga kafad’ar Majidad’i... Suna tsaka da zancen ne kaman daga sama suka sinkayo kururuwan Innani tana fad’in ta shiga uku ta mutu ta lalace Sun kashe mata miji..!

Yazeed da Majidad’i suka dubi juna a tare... Babu shiri suka fad’a cikin d’akin Majidad’i kaman zai kifa k’asa yake ambato mahaifinsa....
Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..! Dukkanin mai rai mamaci ne, yanda akazo haka wata rana dole a tafi duk daren dad’ewa, koda anaso koda ba’aso idan wa’adi yayi dole bawa ya komaga mahaliccinsa.. Allah ka bamu k’arshe mai kyau Ameen..!

Koke koke sukaci gaba dayi cikin asibitin, yayinda Yazeed ya zame jikinsa ya fice daga cikin asibitin...

**

A can Fada kuwa tun bayan dawowan Mahmood gida ya aika ai masa kiran Fu’ad...

Yana zaune parlornsa yana duba mail d’insa da ya jima baibi takansa ba sabida abubuwa dake kan faruwa a Masarautar Fu’ad yai sallama ya shigo...

Idanunsa naga computer dake bisa teburi gabansa ya amsa sallaman Fu’ad d’in had’ida masa izinin zama ....

Fu’ad ya furta kalaman godiya kana ya isa ya zauna a d’arare dan harga Allah mugun nauyin Yayan nasa yake tamkar wani mahaifinsa...

Shiru ya d’an ratsa tsakani Mahmood naci gaba da abinda yake bisa computer... Sai bayan kaman ahud’ewar wasu dak’ik’ai Mahmood ya kashe computer d’in had’ida zame farar tabarau dake mak’ale fuskarsa wanda ko ba’ace Kai tsaye zaka iya cewa na k’ara k’arfin gani ne... Hakan ya baiwa Fu’ad daman zamowa kad’an daga cikin kujera ya gaida Mahmood d’in...

Babu yabo babu fallasa ya amsa masa kana ya soma masa tambaya gameda sabon karatunda bai jimada farawa ba “Ya karatun naka... Kanadai yi koh...?” Yai maganar yana mai daidaita zamansa cikin kujera

Fu’ad ya jinjina masa kai alamun tattabatarwa kana ya k’arada “Alhamdulillah Yaya jiya na kammala registration..”

Jinjina masa kai yai kaman bazaice komai ba sai kuma yace “Yayi kyau...!” Shiru ya d’an ratsa tsakani kafin Mahmood d’in yai gyaran murya kad’an yace “Fu’ad I want you to concentrate on your studies for now... Banda maganan mata da abokai barkatai, ba komai zasu haifar maka ba face distraction....Priorities your studies first... Ka fahimta..?” Ya k’arashe yana mai tsare Fu’ad d’in da idanu...

A hankali Fu’ad Ke jinjina masa kai “Na fahimta Yaya... And in sha Allah this time around I’d not disappoint you, zanyi iyaka k’ok’arina naga nayi graduating da yardar Allah... But Yaya wani hanzari ba gudu ba...!”

Mahmood ya d’ago yana dubansa.. Kafin Fu’ad ya sami zarafin magana Sarkin Gida ya shigo a firgice had’ida zubewa k’Asa yana furta “Tuba nake Allah shi taimaki ‘ya’yan Sarki.. A gafarceni na shigo babu izini Babban Al’amari Ke tafe dani...!”

Yarima Mahmood yace “Fad’i damuwarka Sarkin gida meke tafe dakai...?”

Sarkin gida ya kuma risinawa yana mai yarfe gumin goshinsa yake fad’in “Allah shi taimakeka Wambai ne...!”

Baikai aya ba Mahmood ya mik’e tsaye zunbur yana furta “Ya jikin Wambai...?”

“Allah shi taimakeka Wambai dai Allah yayi masa cikawa....!!” Ya k’arashe yana mai karanto addu’o’i ga Wambai d’in...

Hannayensa hard’e Ta baya ya lumshe gajiyayyun idanunsa yana mai furta Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un cikin zuciyarsa...
Fu’ad ma ambaton Allah ya somayi yana mai jinjina lamarin...

Take Yarima Mahmood ya d’au wayar salulansa saman center table ya nufi k’ofa babu shiri lokaci guda yake ceda Fu’ad “Call your brothers Yazeed and Jamal, and please ka shiga ka sanar da Maami calmly...” Fu’ad ya jinjina kai yana mai furta “Okay Yaya... Right away...!” Mahmood ya kuma duban Sarkin Fada yace maza a sanar da ahalin Fada shi ya wuce gidan Baba Wambai.... Sarkin Fada ya amsa yana mai masa addu’an sauk’a lafiya had’ida karanto addu’o’in neman rahama ya Wambai...

Yana tafe ya kirawo Turaki ya sanar dashi, babu b’ata lokaci Turakin yace su had’u can gidan Wambai d’in....

Daga can Sarkin Mota ya hangoshi ya taso a guje ya nufosa yana masa fadanci yake fad’in “Allah shi baka yawan rai Ka baiwa Sarkin mota izini ya tuk’a ka rik’e sitayari(Steering) ba naka bane... Kokuma d’aya daga cikin drebobin gidan ya tuk’a Allah shi taimakeka... Balle ma kaid’in Sarkin Mota shi yafi cancanta ya jaka... Godiya nake Allah shi taimakeka...!” Ya k’arashe yana mai bud’ewa Mahmood d’in owners corner...
Shidai kawai shigewa motar yai ba tareda ya tsaya sauraren Sarkin Mota ba... Bafaje guda d’aya ya shige gaban mota...Kankace mai Sarkin mota ya jata sun fice cikin Fada....

A can k’ofar gidan Wambai suka tadda su Waziri Hakimi Galadima Jarmai da dai sauransu.... Sanda Mahmood ya iso suka soma gaisawa suna masa ta’aziya had’ida sanar dashi Wambai na cikin ana masa sutura...

Fitowar Majidad’i tareda Yazeed kenan sukai tozali da Mahmood.. Ganinsu su biyu a tare sosai ya baiwa Mahmood mamaki, ya akai har Yazeed ya sani ya rigasa k’arasowa kuma Sarkin Fada mashi ya soma sanarwa... Toh Wai ma ya akai yaga Yazeed da Majidad’i a tare... Wata zuciya tace rasuwa akai so ba komai bane dan ka gansu tare... Mutuwa na sa a aje duk wani gaba da k’iyayya a gefe... Majidad’i sai aika masa muguwar kallo yake yayinda Yazeed ya k’arasoga su Galadima yana sanar dadu an gama shirya Wambai...
Mahmood kaw k’arasawa wajen Majidad’i yai ya masa gaisuwa dukda cewa ba wani amsa sa yai ba...

Isowar Turaki dasu Fu’ad su Jamal dadai wasu tsiraru daga cikin tawagar Fada suka d’unguma zuwa cikin gidan gaba d’aya sukaima iyalan Wambai gaisuwa...
**

Kasancewar hankulan mutanen gidan ya karkata zuwa rashin da akai ga d’aukacin Masarautar hakan sai ya baiwa Muhibbah dama domin ta binciko zanen da takeda tabbacin Jamal ya d’aika daga wajen Umaima..

Sashen Jamal a kulle yake gashi wannan shine damarta na k’arshe dan batasan sanda zata sake samun dama irin wannan ba... Mayafin kanta Ta cire Ta had’a da d’ankwalinta tai majajjawa ta jefa sama nan ta samu kuwa ya kama... Tuni Ta soma k’ok’arin haurawa sama da igiyar data k’ulla dikda cewa k’iris ya rage bata zulo k’asa ba... Cikin sa’a da ikon Allah ta samu ta dafe jikin gini ta k’arasa haurawa da k’yar tana mai tsananin haki... Ta koma gefe tana maida numfashi tana duba hannayenta yanda Ta kukkuje... Cikin sauri Tai azaman tashi had’ida kakkab’e jikinta Ta bud’e sliding door da zai sadaka da cikin d’akin Jamal daga nan sararin shak’atawa dake a saman nasa... Cikin sand’a take gudanar da al’amran nata...

D’akin Ta soma k’arewa kallo kafin ta soma binciken drawers tana duba ta yanda zata sami wannan zanen...

Drawers da dama ta bincika bata samu ba saidai tana janyo wani drawer dake a k’Asa gabanta ya yanke ya fad’i, hannunta na tsananin rawa take janyo abinda Ta gani cikin drawer d’in... Farin k’yalle Ta gani da shatin jini jiki... Jikinta bai ida mutuwa ba saida taga Fararen k’yallayen har guda goma sha biyar ne ko wanne da shatin jini a jiki.... Sosai jikinta Ke tsananin rawa tana mai ci gaba da k’arema k’yallayen kallo.. Gabanta ya kuma tsinkewa ya fad’i sanda taga ko wani k’yalle d’auke yake da suna daga k’asansa... SAUDATU shine sunan data hanga jikin k’yalle na k’arshe wanda shima d’auke yake da shatin busasshen jini....
Take ta rintse idanunta had’ida toshe bakinta da duka hannayenta biyu jin wane irin kuka mai k’arfin gaske na zuwa mata.... Ta koma gefe guda ta tak’ure sosai tana kuka mai tsuma zuciya.... Abubuwan da suka faru da ita shekarun baya sukaita dawo mata... Da k’yar ta iya saita kanta tai saurin tattare k’yallayen ta maidasu yanda ta samu... Har ta saduda bazata sami hoton zanen ba dan gara tai ta fice kafin a taddata cikin d’akin komai ya rushe mata... Kaman ance ta d’aga bakin katifa nan taji ta kamo alamun abu... Tana janyowa kuwa taga frame d’in ne... Sauk’e deep breath tai kana tai saurin ciro wayarta ta soma d’aukan hoton zanen... Sauri sauri take k’ok’arin maidawa...

Tana shirin ficewa ne taji alamun ana haurowa saman babu shiri Ta koma da baya k’irjinta naci gaba da bugu... Ta rintse idanunta tana karanto addu’a cikin zuciyarta...

Muryar Giwa ta sinkayo cikin fad’a fad’a tanaima Jamal d’in magana shi kuma yak’i tsayawa ya saurareta sai haurowa sama yake...

D’aki ya shigo rai a matuk’ar b’ace kafin ya maida k’ofan Giwa ma ta bangaji k’ofan ta shigo tana furta “Ka saurareni nace Jamal.... Kana jina koma wacece budurwar taka ka aje maganar soyayya ba yanzu ba na fad’a maka sai babu adadi akwai shiri na musamman da nake maka...!”

Cikin tsananin k’unan rai yake dubanta kana ya girgiza cikeda rashin yarda da kalaman dake fitowa daga bakinta “Har yaushe kenan Maami... Har yaushe zanyita zama a haka... Maami girma nake ba k’ank’ancewa nake ba... I want to start my own family, na rok’i arzikinki Ki k’yaleni haka nan... Ya isa haka please..!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya yana mai had’e hannayensa biyu waje guda alamun rok’o...
Chapter 55 · 0% Book details