← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 162

Sashe 46

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin azama ya mik’e yana mai k’ok’arin k’ara wayar a kunnesa...
Zahra tabi mahaifinta da kallo har ya fice, ita dai kam ta hango wani abu tsakanin Paa d’inta da Tia Hibbah, da ace hasashenta zai tabbata da sai tafi kowa Farin ciki... Amma tunawa da tai Paa ya canza akwai abinda yake b’oye mata sai taji jikinta gaba d’aya yai sanyi... Idan har zarginta akansa ya tabbata Toh kuwa Tia Hibbah bata cancanci miji irin mahaifinta ba, domin itad’in mutumiyar arziki ce ba kaman mahaifinta da takeda tarun shakku da kokonto akansa ba... Ta lumshe idanunta a hankali tana mai silalewa saman gado...

**

A b’angaren Muhibbah tana ficewa bata zarce ko ina ba sai masauk’inta.... Tai zaune saman gado tana maida numfashi had’ida ajiyan zuciya d’aya na bin d’aya.... She shouldn’t have treated his wound... She should have let him bleed to death, it’s what he deserve after all.... Maiyasa bata k’yale shi jinin yaita kwaranya ba...?! Tai gajeren tsuka a hankali tana tina yau d’in taimako biyu taiwa Mahmood wanda duk bai cancanta ba... Na farko tsallake tuggun Raheema, sannan ga gyara masa hannunsa da tai... Tunanin abin sai yasa taji tamkar yanzu ne take rufe ciwon Mahmood, komai ya shiga zuwa mata daki daki tai saurin rintse idanunta da k’arfin gaske tana mai shafe fuskarta da duka tafukan hannayenta...

Ware idanunta da zatai tai tozali da d’igon jinin Mahmood cikin tafin hannun nata... Tai K’uri tana duban drop na jinin da tuni ya bushe cikin tafin hannunta, k’irjinta bai daina bugu ba tai saurin fad’awa bathroom ta bud’ewa tafukan hannayenta ruwa tana mai gurje tafukan hannayen nata da k’arfin gaske tamkar zata cire fatarta... Saida ta d’ibi lokaci tana wanke hannun dikda jinin ya fice kana ta d’ibi ruwa cikin tafukan hannun nata ta wanke fuskarta har kusan sau uku, lokaci guda tai K’uri tana duban fuskarta cikin mirror... Ta janyo k’aramar towel Ta goge fuskar tata dashi kana ta nufo d’aki ta d’au wayarta lokaci guda tai dialing layin Ansar...

Cikin sauri kuma ta katse kiran saidai tuni ya shiga, ta komo kan gado ta zauna tana tinanin toh ma mai zata soma ceda Ansar...? Ta kuma lumshe idanunta a hankali tana juya wayar cikin hannunta, kaman daga sama sai ganin kiran nasa tai.. Ta d’ago fuskar wayar tana duban sunan Ansar dake kira, kaman dai bazata d’aga ba sai kuma ta d’aga cikin kasaliyar murya....

Daga d’aya b’angaren Ansar ke amsa sallamarta yana mai tambayarta ko tana lafia, kaman dai Babu wani abinda ya faru haka nan yake amsa wayar...

Cikeda borin kunya Muhibbah tace “Maiyasa ka kira..? The last time I checked fushi kake dani kuma kace bazaka sake kirana ba...!”

Murmusawa yai kad’an kana yace “And last time I checked kece kika soma kirana... So tell me, what’s wrong this time...? Nasan haka kawai bazaki kirani ba, you must have a reason...Fad’a min What went wrong this time...?”

Rausayar da idanu tai a hankali kana tace “Yanzu haka ka d’aukeni bazan kiraka ba saida dalili...? Ni ba kiranka nai ba... Idan kuma na kiraka bansan nayi ba..!” Ta k’arashe cikin fad’a...

Ya kuma murmusawa a hankali kana yace “Alright fine... Naji baki kirani ba ni na kiraki sannan kuma ni na tambayeki Ki sanar dani abindake faruwa...Is there anything I can do to help..?!”

Fuzar da huci tai a hankali kana tace “They wanted to do a background check on me...Ansar they were planning to have me investigated...!” A tak’aice Ta labarta masa tattaunawar Mahmood da Raheema dataji...Ta k’arashe tana mai dafe goshinta da hannu guda...

Kaman wanda yake ganinta yace da ita “Just calm down and take a deep breath..! As long as ina taredake bazan bari susan ko ke wacece ba... Karki damu kinji, just leave that to me, I would take care of that...abinda kawai nakeso dake shine kici gaba da kula, karki basu wata k’ofa da zasu fahimci ko ke wacece kinji koh...”

Ta jinjina masa kai a hankali “In sha Allah... Bazan basu ba... Thank you Dr, thank you for always having my back..!”

Suna gama waya da Ansar tura file d’in gabansa yai yana d’an dukan kansa da pen, baida lokacin tsayuwa yin fad’a ko fushi da Muhibbah... Yafi kowa Allah Allah ta gama wannan mission d’in nata ta dawo ai maganar aurensu once and for all... Dole yai hak’uri da dik wani fushi da fad’a ya aje komai a gefe ya taimaka mata ta ida wannan so called mission d’in nata dan idan ba haka ba the more yana biyeta sunayin fad’a the more yawan lokacinda zatai zaune cikin Masarautar yana k’aruwa... Ya kuma fuzar da fuci a hankali yana mai bada izini ma patient na gaba da ya shigo...

***

A b’angaren Muhibbah kaw zuciyarta ne yai wasai dan tasan Ansar zai toshe dik wani k’ofardasu Raheema zasubi a makaranta su gano asalinta, yanzu abinda ya rage mata shine tai monitoring duk wani move nasu Raheema idanma son samu ne ta shige jikinsu ta samu yardarsu dukda tasan hakan abu ne mai matuk’ar wuya tinda tin farkon had’uwarsu babu jituwa sam tsakaninsu musamman dashike Raheema gani take tamkar Ta shigo Masarautar ne dan Ta k’wace mata masoyinta Yarima Mahmood.. Dan haka shiga jikin Raheema zai matuk’ar mata wahala... Ta fuzar da fuci a hankali tana mai kuma sak’e sak’e cikin zuciyarta had’ida neman mafita...

**

A cen parlorn Mahmood kuwa tsaye yai yana duban Turaki hannayensa hard’e ta baya... Saida ya kuma takowa kad’an kana yaja ya tsaya “Turaki bana shakkan su fahimci cewa ni ne bak’on Buzu... Abu guda da zaisa bazan bayyana masu kaina a matsayin bak’on Buzu ba shine nima akwai abinda nake bincike cikin gidan sannan Ina akwai abinda nake son fahimta gameda ciwon Baba Wambai... Idan har da gaske akwai wani abinda Baba Wambai ya sani gameda abubuwan da suka jima suna faruwa a gidan nan Kaga babu makawa za’a nemi a b’addashi Ta ko wacce hanya ko kuma a hansa yin magana.. Everything is possible a gidan nan, zasu iyayin komai to silent him dan asirinsu ya rufu...So kaga dole na k’ara taka tsantsan hardai inaso na sami amsoshin da na jima Ina nema...!”

Jinjina kai Turai yai a hankali yace “Wannan gaskiya ne Your Highness... Toh yanzu mai kake shiryawa...?”

D’an dubansa da wutsiyar idanu Mahmood yai kana ya kauda fuskarsa kad’an “Lokaci zai sanar damu...!” Ya fad’i yana mai zama cikin kujera...

Turaki yai ma abokin nasa k’uri kana yace “Toh shi Majidad’i fah... Ya zakai dashi... I’m sure he won’t stop tunda ya soma kutso Kai cikin Fada d’aukeda makami... Sannan na tabbata a shirye yake sosai...!”

Ba tareda ya dubesa ba yake furta “Zan k’yalesa yaci gaba da bincikensa... In the process na bincikensa zai iya samomin wani abu da zai min amfani a binciken da nake, wannan na d’aya daga cikin dalilin da yasa nace a k’yalesa... Is possible someone has been monitoring my every move all this time... Ta yuwu akwai wanda yasan cewa nine bak’on Buzu saidai bazai iya fitowa ya fad’i ba dan shima mafita yake nema ma kansa...Ta yuwu ya fahimci ina gab da tono gaskiya shine bari ya rufe bakin Baba Wambai ta wannan hanya.... But koma menene I’d make sure to be one step ahead of them...!” Ya k’arashe yana mai duban Turakin....

Turaki ya murmusa kad’an cikeda jin dad’i yana mai jinjina kai lokaci guda yake ci gaba da yabawa zurfin tunanin abokin nasa... Tabbas ya yarda Mahmood zai zak’ulo duk wanda sukeda hannu cikin manak’isar wannan gida....

Yarima Mahmood ya d’auki glass cup dake aje gefensa na dama saman k’aramar table dake tsakankanin kujeru ya kurb’a, har lokacin k’uri yaima waje guda yana mai murza bandage d’in dake d’aure hannunsa... Soma murza bandage d’in Keda wuya tinaninta ya fad’o zuciyarsa... Take ya soma tina duk abubuwan da suka faru daki daki, sanda take goge masa ciwon da kuma sanda take rufe tafin hannun nasa da bandeji... For the first time da ya saki murmushi tun bayan abubuwan nan dake kan faruwa...

Turaki yai masa K’uri ganin ya k’urama waje guda idanu yana sakin sihirtaccen murmushi mai taushi wanda saika kula ka fahimci hakan...

Sallaman Ubandoma ya dawo dashi daga duniyar tinanin da yai nisa ciki... Ubandoma ya zube yana kwasan gaisuwa, nan yake sanarda Yarima Mahmood Giwa tayi Aiken Jakadiya cewa tana san ganin Yarima...

Jinjina masa kai yai alamun amsawa... Turaki ne ya soma ya soma mik’ewa sukai sallama kana suka jera a tare suka fito... Suka tsaya nan cikin haraban sashen Mahmood d’in...

Yarima Mahmoood yaci gaba da fad’in “Wani aiki nakeso kamin Turaki...!”

Turaki ya jinjina kai “Duk abinda mai Martaba yace...!”

Jinjina kai Mahmood d’inma yai had’ida yin gyaran murya kad’an “Ja’afar...!”

Turaki ya dubesa da mamaki yana jiran yaji mai Mahmood d’in zai d’aura...

“Turaki I want you to hire a private detective wanda zai mana bincike akan where about d’in Jafar, dik yanda Ja’afar ya shiga ya fita inaso a samoshi... Can you do that..?!”

Turaki ya jinjina kai “Of course your Highness, leave it to me... I can handle that Rankaidad’e..!”

Jinjina kai Mahmood ya kuma yi kana sukai masabaha had’ida sallama Turaki na fad’in sai yaji daga garesa...

Kallo guda zakai mata ka fahimci tana cikin tsananin tashin hankali.. Aiko Mahmood na shigowa Giwa ta k’araso garesa tana mai janyo hannunsa mai ciwo take fad’in “Sadauki lafia kake... Shin ta yaya wannan mahaukacin yaron zai shigo har cikin gidan nan yai mana wannan wulak’ancin... Toh wannan masarauta bazata lamunta ba, ya zama dole a hukuntasa...!” Ta k’arashe cikin tsananin huci cikeda tashin hankali...

Kafad’unta Mahmood ya kamo ya zauanrta saman cushion a hankali lokaci guda yake furta “Take it easy Maami, ki kwantar da hankalinki banaso kina saka irin wad’Annan abubuwan a zuciyarki...!”

Giwa ta d’an marairaice fuska tace “Shikenan sai in zuba idanu su sakaka gaba... Kaima kasan bazan iya hakanba Sadauki...!” Ta k’arashe cikeda kulawa...

Nusawa kad’an yai yace “Maami a gida irin namu dole mu saba da irin wad’ann abubuwan so ba wani abu bane In sha Allah...!”

Ta mik’e daga zaunen da take tana mai karantarsa, a hankali take zagaya d’akin har ta k’araso gabansa ta tsaya “Sadauki... Maiyasa kak’i amsar Sarauta...?”
Chapter 46 · 0% Book details