Sashe 3
Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwankwad’an ruwan ya kumayi yana fuzar da fuci a hankali kana ya soma fad’in “This is not possible, bazan tab’a k’yalesa ya d’auki abinda na jima Ina gina rayuwata akai ba... How dare he rana tsaka zai dawo yace zai amshi sarauta, Uban mi ma ya dawo dashi Masarautar nan, mai ya sani gameda mulki da sarauta.... Wllhi idan za’a kashe rai a masarautar nan bazan k’yalesa ya karb’e what’s rightfully mine ba, what I worked hard for.... Babu wanda ya cancanci mulkin Masarautar nan face ni Yazeed..!!!” Ya k’arashe cikin tsananin huci yana buga k’afarsa daga zaune alamun k’unan zuciya had’ida matse gorar ruwan dake hannunsa lokaci guda yai jifa da gorar wanda har saida yasa Zuhrah d’an firgita...
Ta d’ago tana dubansa a hankali kaman mai tsoron kallon nasa, Sauk’e ajiyan zuciya Zuhrah tai dan tasan halin zuciyar mijin nata, hannunsa ta janyo cikin nata dikda rawar tsoro da hannun nata keyi, ganin bai gwaleta ba ya sanyata d’an d’aura kanta gefen kafad’arsa a d’arare, lokaci guda take furta “My Prince, Nifa wannan sarauta bai dameni ba as long as our family is happy, ban damu sai kayi sarauta ba... Kuma Ya Mahmood shine gaba da kai, a ganina shi ya kamata ya gaji Baba....”
Bata Kai aya ba ya dakatar da ita da fad’in “Ya isheki haka, ke wacece da zaki fad’a min ra’ayinki... Yaushe kika fara fad’in ra’ayin kanki a gidan nan, tashi Ki fita kafin raina ya b’aci, banson jin komai.... Tashi Ki fita.... I want to be alone...!”
Dubansa ta kumayi kaman zatai magana saidai irin kallon da yake mata tasan babu k’ofan kuma magana... A hankali Ta mik’e Ta nufi k’ofa tana mai kuma waigowa cikeda firgici da tsoron mijin nata....
***
BAUCHI
Cikeda tsananin tashin hankali Ansar ya taso daga mazauninsa ya komo gabanta, durk’usawa yayi nan gabanta yanda take shesshek’ar kuka bayan Ta gama karanto masa abinda ya faru da ita shekarun baya, shekaru goma sha biyar da ya shud’e....
Cikin tsananin k’unan rai yake furta “Dama abinda suka miki kenan.... Hibbah now more than ever bazan iya barinki Ki koma cikin Animals d’un nan ba.... Hibbah no..... No, bazan barki ba...!”
Cikin kuka itama Ta mik’e tana furta “Ansar ban sanar dakai ba saida ka amince mun da buk’ata ta... Ka fad’a ta yaya zan cika alwashin da na d’auka na fanasar rayukan iyayena har biyu.... Ta yaya zan sami justice d’in da nake nemawa kaina da iyayena...? Ansar those people are powerful, sunada dukiya da mulki, bazan iya shari’a dasu ba amma zan iya rama abinda suka min, Ansar ko a addini banyi kuskure ba dan na rama abinda suka min... The only way to get the justice that I deserve shine na shiga rayuwarsu and ruin them all... Kuma Wllhi alwashi na d’auka sai na tarwatsasu... Ansar you can’t stop me now....!!” Ta k’arashe cikin tsananin kuka mai tab’a zuciya....
A hankali ya fuzar da huci yana dubanta kana ya jinjina kai a hankali.... Shafa fuskarsa yai da duka hannayensa biyu kana ya zauna saman sofa gijif..... “You’re so stubborn..!” Ya furta a hankali
Muhibbah ta tako gabansa a hankali ta duk’a k’asa nan gabansa....
“please do this for me... And my parents...!” Tai maganar cikin tsananin rawar murya...
Da gefen idanu yake dubanta, saida ya d’an d’ibi lokaci a haka kana yace “Hibbah I’m sorry, how can I allow you to endanger your life just like that, Hibbah mai na zama...? I wouldn’t be there to protect you....And... what should I tell Mum.... Naci gaba da mata k’arya cewa makaranta kike a jos... What if tace zata Kai maki ziyara...? What if something went wrong...? What if your plan fails...? Hibbah what if... Na rasaki...? Do you think I can bear that...!!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya ga idanunsa da suka kad’a sukai jazir....
Mik’ewa tsaye tai tana goge ragowar hawayen idanunta kana tace “Shekara d’aya tak kawai zanyi cikin Fadar, da zaran an gama rikicin mulki, da zaran na gama tarwatsasu zan San yanda zanyi na fice daga wannan waje... And we would finally be together.... Please Dr... Kamin wannan alfarmar idan har da gaske kana k’aunata...”
K’uri yai mata kana ya kuma mik’ewa tsaye yana mai zagaya parlorn yake fitar da fuci a hankali, a hankali yake furta “This is a tough decision Hibbah...!!!”
“Ansar...!” Ta kirawo sunansa a hankali...
Sauk’e ajiyan zuciya yai kana yace “Shikenan, I don’t want you to think that I don’t love you... Zanyi komai as far as zaki kasance cikin Farin ciki.... Akwai Umaima d’iyar k’anwar Hajiya Turai Giwar Sarki AbdulJabbar mai rasuwa, a gaban Hajiya Turai take zama, zan kirata na sanar da ita akwai ‘yar uwata zatazo karatu na tsawon shekara guda a nan asibitin koyarwa na jos, kuma ta rasa accommodation gashi batasan kowa ba, zan rok’i alfarmar Ta baki masauk’i a nan Fadarsu, karki damu Umaima mutuniyar arziki ce, Sabon social media mukai, tana following page d’ina da nake bada shawarwari kan irin abincin da mutum zaikeci ya rage tumbi k’iba da sauransu, da yanayin motsa jiki da ya kamata ya dingayi... Daga nan muka saba dan idan naje Jos har gayyata Ta Fada tanayi tamin tarba mai kyau.... So na tabbata bazamu sami matsala daga wajenta ba in sha Allah....”
Tsananin Farin ciki yasa taji tamkar tai tsalle ta rungumesa.... Godiya taita jero masa cikeda Farin ciki... Ansar kaw dubanta kurum yake cikeda tausayawa musamman idan ya tuna labarin data gama bashi....
A ‘yan kwanakin Muhibbah ta soma shirin tafiya Fadar Jos, dan tuni Ansar sun gama magana da Umaima wacce tace dashi ya wuce neman alfarma wajenta, Fada gidansu ne shima, Masauk’i ko mutum nawa ne ya kawo zai samu balle k’anwarsa...
A b’angaren Mum d’in Ansar kuwa sanar da ita yayi Muhibbah makaranta zata tafi Jos kaman yanda suka tsara shida Muhibbar, Sam Mum batada labarin wannan al’amari nasu....
Koda tace zatai rakiyawa Muhibbah sai cewa Ansar Yai tai zamanta kawai tinda ba lafiya bane ya isheta shi zai kaita, hakan kuwa akai...
Muhibbah ta gama shirinta sukai sallama da Mum kana suka nufo Jos Babban gida.....
SameenaAleeyou📚
[5/20, 10:31 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*
*003*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Kishingid’e yake saman darduma shatin kwabo ta zallar fata, yana sanye da riga ‘yar shara irinta shan iskar masu sarauta... Gaba d’aya sai shekarunsa suka bayyana ba kaman lokacin da yake turai yake saka k’anan kaya dake b’oye yawan shekarunsa ba, sam bazaka bashi shekaru 46 ba a lokacinda yake k’asar Spain, yau kam sai Zahra taga girman Baban nata ya d’an bayyan dikda cewa Allah yayisa mai kyaun k’ira, da sallama saman bakinta Ta shigo farfajiyar harabar benen yanda Yarima Mahmood Ke kishingid’e.... Ya aje jaridar hannunsa yana mai amsa mata had’ida mik’ewa sosai ya zauna, kyakkyawan murmushi saman fuskarsa.... Lokaci guda yai alama da hannu ma dogarai guda biyu dake tsaye wajen tamkar an dasasu... Babu musu suka sa kai suka fice cikeda risinawa...
Kaman kullum yauma fuskarta a murtuk’e yake alamun har yanzu batai Na’am da hukuncin da mahaifinta ya yanke na dawowa k’asarsu ta gado da sukai ba....
Gyara zamansa yad’an kumayi murmushi saman fuskarsa yake dubanta, lokaci guda yake furta “Esa ropa te queda bien mi princesa..” (Kayan nan sun maki kyau my Princess)
K’ok’arin k’ak’aro murmushi tai kana tace “Buenos dias Paa..” (Barka da da hutawa Paa) Ta fad’i a tak’aice...
Hannunta guda ya kamo kana yace “Zahra d’ago ki kalleni....”
Ta d’anyi rau rau da idanu tana dubansa, shid’inma ita yake duba....
“Zahra Spain ba k’asarmu bane dole dik daren dad’ewa mu dawo nan wata rana... Ina fata ki fahimci haka...”
Share hawayen da suka gangaro mata tai kana ta soma fad’in “Paa ba Wai dawowa Nigeria bane bana so... Dejè mi vida allá en españa Paa... Mis amigas, mi escuela, and everything..” (Na baro rayuwata a Spain Paa, abokaina, makaranta na and everything)
Ta d’an ware idanunta kana taci gaba da fad’in “And you know what is worst...? Maami yanzu zata saka kayi aure, and Paa I hate Aunty Raheema... Bana so ka aureta Paa....!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya...
Bata Kai aya ba kuwa babban bawan Yarima Mahmood mai kula da al’amransa mai suna Uban Doma ya shigo had’ida zubewa k’asa cikeda ladabi irinta babban gida yake fad’in “Allah ya taimakeka Jakadiya ta sanar dani isowar bak’uwarka....” Yai maganar kansa a k’asa...
Duban Zahra Yarima Mahmood yanda annurin fuskarta ya kuma d’aukewa chak dan ta tabbata Aunty Rahima ce ta iso kaman yanda taji Kakarta d’azu na maganan tareda Jakadiya....
Ba don yayi niyyan maraba da bak’uwar tasa ba sai don baiso mahaifiyarsa ta kawo wani zargi ko kokonto gameda shirinsa, hakan ya sanyashi yin d’an gyaran murya kad’an kana ya jinjina kai a hankali, Uban Doma yasan mai hakan Ke nufi dan haka tuni ya kuma risinar da kansa yana mai furta “Godiya take Yariman Yarimomi Magajin Masarautar Jos.. Allah ya baka gidanku...Jaaa zamanin ka...!!!” Ya k’arashe yana mai baza jan babban gyaren dake jikinsa had’ida mik’ewa ya fice yana mai k’an k’an da kai alamun girmamawa.....
Zahra kaw tana jin haka mik’ewa tai tana mai furta “Paa zanje k’ofan Aunty Zuhrah.... Na Barka lafia Paa...”
Yarima Mahmood ya dakatar da ita da fad’in “Ki tsaya ku gaisa da Rahima....”
Kanta a k’asa kaman zatai kuka take fad’in “Pero Paa....” (Amma Paa) Kasa k’arashewa tai ganin yanda mahaifin nata ya kafeta da dara daran idanunsa masu firgita duk wani mai laifi....
A hankali ta shiga jinjina masa kai kana tace “Estaré abajo Paa...” (I’ll be downstairs Paa)
Ya jinjina mata kai a hankali kana ta mik’e cikeda risinawa ta sauk’o k’asa....
****